Sayyid Isma’il Umar" />

Ranar Da Wahayi Ya Cika Da Ita Ma Ba A Fara Kirgen Shekarar Musulunci Da Ita Ba

Masu karatu assalamu alaikum warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Kamar yadda a makon da ya gabata muka fara bayani a kan muhimmancin ranar cikar wahayi, sai dai ba mu yi nisa ba, a yau za mu shiga cikin bayanin sosai domin duba muhimmancin ranar wadda duk da haka Sahabbai ba su fara kirgen shekarar Musulunci da ita ba, sai da ta Hijira.

Kamar yadda bayani ya gabata, wata rana mai girma da kuma ba a fara kirgen farkon shekarar da ita ba ita ce ranar da Wahayi ya cika. Shekara 23 da aiko da Manzon Allah (SAW), a sannan kuma shekarar giwa tana da 63. Shekara  634 kuma da haihuwar Annabi Isah (AS). A wannan lokacin Allah ya cika mana addini a Dutsen Arfa, bayan Manzon Allah (SAW) ya isar da amana, ya yi wa al’umma nasiha, ya gama duk abin da aka aiko shi da shi na kira,  ya yi wa mutane bishara da wannan addini, sai Allah ya cika addinin da tun daga Annabi Adamu (AS) Ya faro har zuwa kan Annabi Muhammadu (SAW).

Allah ya cika Islam, Iman da Ihsan. Shekara wajen goma da aka yi a Makka ana ta fama ne da mutanen Makka a kan La’ila ha illallal da kuma kyawawan dabi’u. Har zuwa lokacin da Manzon Allah ya yi Isra’i da Mi’iraji aka kawo Sallah, daga nan sai Zakkah, sai kuma Azumin Ramadan. Sallah ce kawai aka saukar a Makkah, amma Zakkah da Azumin Ramadan da Hajji duk bayan Hijira ne aka saukar da su. A shekara ta goma Manzon Allah ya zo Hajji. A Hajjin bankwana da Manzon Allah ya yi, ya ce wa al’umma ku riki Hajji daga wuirna ba na zaton zan sake kaiwa wani Hajjin. Bayan ayar da ta yi magana a kan cika addini ta sauka a ranar Arfa, kashegari kuma sai surar Izha ja’a nasrullahi ta sauka. A cikinta ga batun Istigfari da Tasbihi a ciki.

Bayan an dawo gida da ko awa biyu ko kwana biyu (babu dai wata ruwaya da ta ce an yi sati guda) sai ayar Wattaku yauman ta cikin Suratul Bakara ta sauka, ita ce rufe Kur’ani. Ita kuma a cikinta ga batun Takawa nan (tsoron Allah) a cikinta. Duk dai komai na Shari’a ya sauka.

Lokacin da Mala’ika Jibrilu ya zo ya tambayi Annabi (SAW) mene ne Musulunci, mene ne Imani kuma mene ne Ihsani? Bayan Annabi ya ba shi amsa ya tafi, Manzon Allah ya ce wa Sahabbai Jibrilu ne ya zo don ya sanar da ku addininku. Ina kara jaddadawa cewa “Addini” Manzon Allah ya ce. Ka ga masu cewa ai addini ya cika don haka ina aka samo Darikun Sufaye ba su san mene ne addini ba.

To wannan addinin na Tauhidi shi ne tun daga Annabi Adamu har zuwa kan Manzon Allah (SAW) ya cika. Shari’a ce dai ta Annabawan ake saukarwa dai-dai da zamanin Annabin da aka aiko. Daga Annabi Adamu (AS) zuwa cikar Musulunci a wurin Annabi (SAW) an yi wajen shekara 7,000. Ka ga duk alherin da aka ce an fara shi wajen shekara dubu bakwai da suka wuce ranar kammala shi babbar rana ce ta murna. Wani Bayahayude ya ce wa Sayyidina Umar (RA) kuna da wata aya, da mu ne aka saukar mana da ita za mu riki ranar a matsayin ranar Idi. Sayyidina Umar ya tambaye shi wace ran ace, ya ce “Alyauma Akmaltu lakum dinakum”, sai Sayyidina Umar ya ce masa to ai a ranar Idin (murna) ta sauka, a ranar Arfa ce, to wane Idi za mu kara bayan na Arfa? Idan muka kawo wani idin daban a ranar sai ya zama kamar zai kwace wa Arfa Idinsa.

Ayar ita ta nuna wa Manzon Allah cewa zai huta bayan ya isar da sakon Allah Tabaraka wa Ta’ala. Kuma halitta ta yi wa Manzon Allah shaidar cewa ya isar. Manzon Allah ya yi wa al’ummarsa nasihohi. Ya ce na barku da abin da in kun yi riko da shi ba za ku bat aba bayana, shi ne Littafin Allah (Alkur’ani). Hadisin Ahmadu bin Hambal kuma ya ce “da ‘ya’yan gidana”. Littafin Allah shi ne farko, Shari’a ce gangariya, ‘Ya’yan gidana kuma ku yi riko da su don su nuna muku yadda ake aiki da Kur’anin. Wannan ne dalilin da ya sa dole sai ka riki wani Dan gidan Manzon Allah na jini ko na ruhi, duk dai ‘ya’yan gidansa ne (SAW). Shehu Ibrahim idan zai yi fassarar Alkur’ani sai ya jawo Dan gidan Manzon Allah Shehu Tijjani ya zo ya dafa shi, saboda kur’ani kamar High Tension ne na wutar lantarki, idan ka ce za ka yi masa hawan kawara sai ya kwada ka da kasa.

Shi ya sa mu ma idan za mu fassara sai mun kira Sahibul Faidhati, yadda Shehu Tijjani ya zamo masa roba na kama high tension mu ma ya zama mana haka don mu iya taba Kur’anin domin samun shiriya. Don haka duk mai cewa ba za a fassara Alkur’ani ba sai an bi wani mutum, a kyaleshi da kansa zai gudu, ya yi wuki-kuki duk ya birkice saboda ba shi da tsani. A Hadisin Imam Malik kuma, Manzon Allah ya ce ya bar mana Alkur’ani ne da Sunnarsa (SAW). Sai Sunnar Manzon Allah ta haska maka ka fahimci Kur’anin, to kuma ba ana nufin ka rabu da Kur’anin gabadaya ka ce ka kama Sunnah kadai ba, ba kuma hauka a ce an bar Sunnah an kama Kur’ani ba shi kadai.

Manzon Allah (SAW) ya ce in dai mun rike Kur’ani, mun yi sallah, mun yi azumin Ramadan, mun yi zakkah, mun yi Hajji (idan Allah ya ba mu iko), mun bi shugabanni; ba mu barbazu mun zama ‘yan yakin sunkuru ba, za mu shiga Aljannar Ubangijinmu. Wani ya tambayi Manzon Allah cewa idan mun bi shugabannin su kuma sun bata tsari ba a kan dai-dai suke ba fa?, Manzon Allah ya ce masa kai dai ka ba da abin da yake kanka ka roki Allah lafiya. Mutum in ya yi haka ya huta, idan kuma ya ki, to shi ma ya zama daya da shugaban da bai sauke nauyin kansa ba, saboda duk sun saba da bayar da hakkinsu duka su biyun. Akwai wa’azi da yawa a zamanin nan namu da muke gani. Dubi irin abin da ya faru a Iraki, dubi abin da ya faru da Libiya, duk wannan ya ishemu wa’azi mu hankalta. Mu dai da ake mulka mu yi kokari mu ba da hakkin da ke kanmu mu roki Allah lafiya. Kuma ba zancen wai ko malami mai fadar wannan ya zama malamin gwamnati ne ko kaza da kaza ba, a’a, duk ba ko daya, illa dai zance ne na Manzon Allah (SAW) da ya kamata mu bi.

Manzon Allah ya isar da sakon da Allah ya aiko shi, kuma ya kwanta damansa. Alhamdu lillah, ko wadanda suke ba Musulmi ba sun san sakon Manzon Allah har ma wasu suna cewa da a ce Annabin Musulmi (Annabi Muhammad) zai dawo duniya yanzu, kafin ya gama shan kofin shayi da ke hannunsa zai iya warware duk matsalar da duniya ke ciki.

To amma duk da muhimmancin ranar karshe da Wahayi ya sauka, Sahabbai ba su fara kirgen shekarar Musulunci da ita ba, sai da Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina.

Wannan Hijirar tun da aka bude Makka Manzon Allah ya ce ta kare. Amma har yau akwai Hijira ta tashi daga inda aka hanaka yin Musulunci (kamar a hanaka yin sallah, a rushe maka masallaci da sauransu) zuwa wani wuri da za ka samu sararin yin ibadarka, Allah ya ce kasarsa mai yalwa ce. Sannan akwai Hijira daga jahilci zuwa ilimi, akwai Hijira daga sabo zuwa biyayya ga Allah, akwai Hijira daga Hijabi zuwa Ma’arifa, don haka kullum a cikin Hijira ake saboda tana da ma’anoni da yawa.

Yana daga cikin abin da ya tabbatar da ‘yanci a duniya Hijirar Manzon Allah (SAW). Amma ba irin ‘yancinmu na Afirka da yanzu wasu ke ganin har gara ‘yancin da ake da shi a karkashin mulkin turawa da shi ba, ‘yanci na adalci da ake bai wa kowa hakkinsa.

Yanzu misali, ‘Yan Misra su da kansu suka taimaki Musulmi suka kori Rumawa daga kasar suka kafa mulki. Amru Binil’as shi ne yake Gwamnan Misira a zamanin kalifancin Sayyidina Umar (RA), dansa ya taba dukan wani Bakifde dan kasa wayayye. Wanda aka doka ya ce “ni ban yarda ba, haka kawai muna murna kun taimakemu mun kori azzalumai (Rumawa) sai kuma ku ku zo daga baya kuna zaluntarmu, zan je in fada wa Kalifa Sayyidina Umar”. Amru Binil’as ya ce idan mutumin nan ya je Madina ya kai kara sun shiga uku, don haka a kama shi a sashi a kurkuku. Ya aka yi; ya aka yi mutumin nan ya balle daga kurkuku ya tafi Madina ya gaya wa Sayyidina Umar. Nan take Sayyidina Umar ya tashi dan aike zuwa Misira yana kiran Gwamna da dansa bakidaya. Suka zo, ko ruwan sha Sayyidina Umar bai basu ba, ya ba wannan Bakifde goransa ya ce ya daki Dan Gwamnan, mutumin ya dakeshi Amru Binil’as yana gani, mutumin da rama iya dukar da aka yi masa sai ya tsaya, Sayyidina Umar ya ce masa yaya? Ya ce ya rama dai-dai iya abin da aka yi masa ne. Sayyidina Umar ya ce da ka ci gaba ma ba mai tsayar da kai har sai ka gaji. To, yanzu kuma daki Baban (Gwamna), Amru ya ce “ni kuma mene ne laifina a ciki”, Sayyidina Umar ya ce “saboda takama da ka yi danka ya bige shi”. Mutumin ya ce “a’a, ni dai na daki wanda ya dakeni”, Sayyidina Umar ya ce “da ka dake shi ma ba abin da ya isa ya yi ma”. Sayyidina Umar ya ce “ya Amru yaushe za ku rika bautar da mutane alhali iyayensu sun haife su a matsayin ‘ya’ya (ba bayi ba)”. Sayyidina Umar ke nan (RA). Wannan yana daga cikin alheran Musulunci da gyaran da ya kawo a zamantakewar al’umma.

Zama ba a karkashin shugabanci ba; ba shi da amfani. Kamar misali, yanzu me ya sa maharbi yana kallon saniya a gida amma zai barta ya je daji ya harbi bauna kuma duk da cewa ana ganin bauna ta fi ‘yanci? Ita saniya tana da shugaban da take karkashinsa kuma idan maharbin ya sake ya tabata zai ga abin da zai faru, ita kuma bauna da ake ganin tana da ‘yancin a sake take ba ta karkashin kowa. Don haka, ba wai ma’anar ‘yanci ka zamo ba ka da shugaba ba, ba wai ma’anar ‘yanci ka zamo ba ka da addini ba. To a Hijira an samu cikakken ‘yanci. Sahabbai sun zamo ba su da wani abu da zai dame su, sai dai sha’anin Allah da Manzonsa.

Don haka in an samu ‘yanci ba zama kawai ake ba, dole ne a samar da tsare-tsare na kula da ci gaban kasa a sassan gudanar da rayuwa daban-daban. Gine-gine ne, abinci ne, siyasa ce (tsarin nada shugabanni), samar da hukumomi da za su tabbatar da zaman lafiya da kare kai, da bude hanyoyin samar da arziki da sauransu. Wannan duka Hijirar Manzon Allah (SAW) ta koyar da mu. Tun da ya isa Madina, an yi tsari na zaman kasa inda aka ba kowa ‘yanci ya yi addininsa, sannan abin da ya shafi kasa kowa an ba shi hakkinsa. Sannan su ma ‘yan kasa an tsara musu hakkokin da za su kare wa kasa. Idan aka yi la’akari da tsarin da turawa ke yi za a ga duk daga na Manzon Allah ne suka sata.

Mun gode Allah, Shehu Ibrahim ya dora mu a kan wannan tafarki na Manzon Allah (SAW). To, duk wadannan alherai su ne Sahabbai suka kalla suka sanya kirgen shekarar Musulunci da Hijira. Saboda Hijirar ta hade alherin haihuwar, da na yakin Badar din da sauransu.

Exit mobile version