Connect with us

LABARAI

Ranar Dimokradiyya: Dan Majalisar Wakilai La’ori Ya Gana Da Jama’ar Mazabarsa

Published

on

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabun kananan hukumomin Numan, Demsa da Lamurde a majalisar wakilai ta kasa Kwamoti Bitrus La’ori, ya gana da jama’ar mazabarsa da sauraren korafe-korafen jama’ar yankin.

Irin wannan ganawar itace irinta na farko a tarihin siyasar yankin da jihar Adamawa, inda dan majalisa kan dawo gida ya bayyana abubuwan da yayi ya kuma nemi jama’a su fito da korafe-korafin abubuwan da yafi damunsu.

Da ya ke jawabi a wirare da dama lokacin ganawar Mista Kwamoti La’ori, ya ce duk da kasancewar yanayin da kasar ke ciki, bai hana ya cimma abubuwa da dama tun farko ya yi alkawari ga jama’ar yankin ba.

Ya ce cikin muhimman abubuwan da ya yi alkawari lokacin yakin neman zabe sun hada da batun tsaro, taimakawa jama’a su samu abin dogaro da kai da kuma samar da ayyukan ci gaba, inda ya bayyana cewa ya cimma nasarori kan alkawarin da ya yi, cikin shekara guda.

La’ori, ya ce “dama na shaida mu ku wannan shugabancin zai zama daban, domin babu wani da kuka turashi Abuja, ya dawo ya taraku ya ce ga abunda ya yi, ya kuma bukaci ku mishi tambayoyi ba.

“Lokacin yakin neman zabe, na ce mu ku za mu tabbatar mun tsaya akan batun tsaro, kashe-kashen da’akeyinnan an daina za’akare lafiyar mutane, munyi muka alkawari za’a tallafawa mu ku, mun yi alkawarin za’a yiwa mutane ayyukan ci gaba.

“Wadannnan abubuwa uku, ina son shaida mu ku muna tsaye akansu kuma mun yi nisa, mun cimma nasarori da dama akan alkawuran da mu ka yi mu ku.

“Ta bangaren tsaro, babu wani abu da ya fara abab da ban kawo tallafi ba, ba ku ganni ba ban kuma je wajen da abin ya faru ba, na rubuta a turo sojoji a yankin Bacham da Dong, bayan harin da’aka kai mu su na ziyarci yankin, na kuma tabbatar sojoji su na wajan.

“Wannan na nuna yadda mu ka dauki batun tsaro da muhimmanci, rayukan mutane ba’abin da za’ayi wasa da shi ba ne, ina kuma tabbatar da cewa kowani lokaci a shirye mu ke mu dauki mataki, haka abinda ya fara a Tingno gwamna ance kada ya je, amma ya je, wannan ya nuna a wannan lokaci ba’irin lokacin da sai anyi ta kashe-kashe gwamnati ta zo tana kawo tallafi ba” inji La’ori.

Da ya ke magana game da aikin tallafawa mutane kuwa Kwamoti La’ori, ya ce ya kashe samada naira miliyan uku da rabi (3.5m), domin bada horo ga matasa yadda za su samu bashi daga babban bankin Nijeriya (CBN) ta hanyar bankin alumma NIRSAL.

Ya ce, “mutum 103 su ka samu horo, an rubuta mu su takardar bukatar bashin, mutum 62 daga ciki an amince za su samu, mutum 20 daga cikin 62 za su samu bashi a wannan wata na Yuli, mutum guda kawai daga ciki zai samu dubu dari 3, shima bansan me ya faru ba, amma sauran duka za su samu daga miliyan daya da rabi zuwa miliyan 3 da rabi.

“Kuma sauran mutane 41, idan 20 sun samu za’a sake a diban wasu 20 daga cikinsu, sannan wani watan a sake, sauran mutanen kuma mu na ci gaba da bi ta yadda su ma za su samu, kuma bayan haka za mu sake bada sunan wasu mutanen 150” ya jaddada.

Jama’a da dama da su ka yi jawabi a taron kamar su Mista P.P Power shugaban hukumar kananan hukumomi ta jiha da shugabannin kananan hukumomin Numan, Demsa da Lamurde da shugabannin alumma sun yaba matakin da dan majalisar ya dauka da cewa zai kawo cigaba mai amfani a harkar siyasa.

An kuma bada kyautar na’ura (Computers) kirar HP coma sha biyar ga daliban jami’o’i da su ka fi kokarin dama cin jarawar College of Graduate and Professional Studies (CGPS), a taron.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: