Connect with us

MANYAN LABARAI

Ranar Dimokradiyya: Muhimman Abubuwan Da Jawabin Shugaba Buhari Ya Kunsa

Published

on

A ranar tunawa da mulkin dimokradiyya ne, shugaba muhamnadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Nijeriya akan abinda gwamnatinsa take yiwa ‘yan kasa don inganta rayuwarau.
In ba’a manta ba dai a shekarar 2018 ne shugaban ya maida 12 Ga watan Yuni a matsayin ranar tunawa da dimokradiyya a maimakon wacce ake kai ada wato 29 Ga watan Mayu. Wadda wannan ranace da aka keve don murnar kawo karshen mulkin soja kuma akafara mulkin farar hula kashi na Hudu wanda ya fara daga shekarar 2000.

Acikin jawabin nasa, shugaban za no wasu bangarori da yace gwamantinsa tasamu nasarori sosai akai, duk da matsalolin dasuka da bai-baye kasa kamar(Korona). Cikin Nasarorin sun hada da:

Rashin aikin yi
Shugaban kasa yace acikin hanyoyin dasuka bi na kirkiran ayyuka don rage raxaxin talauci acikin matasa da korona ta haifar, ya bada umarnin daukar ma’aikata 774,000. Ya Kara da cewa: “Ko wane daya daga cikin karamar hukuma 774 da suke kasa, za a basu damar daukar mutum 1000, kuma wannan tsarin tuni ya fara aiki,”

Tattalin Arziki
Shugaban kasa yace tun da muka futa daga cikin durkushewar tattalin arziki, tattalin arzikinmu ya samu karuwa da daukaka sosai, daga 1.91% a shekarar 2018 zuwa 2.27% a shekarar 2019.
Ya kara da cewa akashi daya cikin hudu na farkon shekarar 2020 ansamu saukar tattalin arziki zuwa 1.87% sanadiyyar cutar korona da ta tsayar da harkokin yau-da-kullum na duniya. Kuma duk wani tattalin arziki na kasashen duniya saida ya samu rauni. Amma namu Bai samu rauni sosai na.
Ya kara da cewa tarin ajiyarmu ta kasashen waje ta karu daga dala biliyan 33.42 a ranar 29 Ga Afrilu,2020. Zuwa dala biliyan 36.00 a watan Mayu, 2020. Wannan ya ishemu mu gudanarwa zuwa wata Bakwai nan gaba.

Korona Da Dimokradiyya
Shugaban kasa yace “Karfin gwiwar mu, mutuncinmu da dimokradiyyarmu tana karkashin barazanar Cutar Korona”
Ya kara da cewa ” Nijeriya tashiga cikin halaye mawuyata da dama a baya kuma ta fita lafiya da karfinta, ina da karfin gwiwa cewa wannan ma da karfin mulkin Allah zamu futa lafiya da karfinmu”

Noma
Noma, a wurin shugaban kasa shine babban abunda gwamnatina tarike don karo sauyi wajen kirkiran tattalin arziki.

Tsarin Takin shugaban kasa zai cigaba da bunkasa da kuma kawo sauki ga manoma wajen siya da amfani dashi

Ya kara da cewa “Wannan kirkira ta shugaban kasa ta gyara tsirrai 31 kuma sannan ta samarwa matasa da aikin yi Kala-kala.”

Ya sake cewa dai “gwamnati tana kara inganta Auduga, Masaka da kuma wuraren kayan saka ta hanyar shirin Babban Bankin Kasa – CBN da ya kawo don rage yawan kudin da ake kashewa wajen shigo da kayan Masaka da Auduga.

A bangaren abinci kuwa, ” muna inganta shiri Mai taken” munoma abinda muke ci kuma muci abinda muka noma ” Grow what we eat”, and “eat what we grow” shugaban Kasa ya kara da cewa ” gwamnati za taci gaba da tallafawa Bangaren Noma ta hanyar shirin Babban Bankin Kasa CBN mai taken ” Anchor Borrowers da ire-irensu”
“Don kula da hannun jarinmu akan Noma, mun sanya Agro-rangers 5000 sannan mun dau ma’aikata 30,289 daga cikin hukumomin mu.
Kuma ashirin mu nafitar da kayan da ba mai ba (non-oil) zuwa kasashen waje ya fara bada kyakkyawan sakamako.
Misali ashekarar data gabata, revenue daga cocoa da irin sesame ya karu daga dala miliyan 79.4 zuwa 153.”

Saukakawa wajen yin Kasuwanci
Shugaban kasa ya bayyana cewa Nijeriya itace ta 25 a tsarin Bankin Duniya wajen saukaka yin kasuwanci daga na 146th zuwa 131st amma gashi yanzun muna cikin goman farko na kasashe masu farfadowa

Kuma ya kara da cewa wannan cigaban yasamu ne sanadiyyar tsarin Visa on arrival policy na mulkinsa da kuma jajircewa akan kirkire-kire dasuka fadada kananan kasuwanni da masana’antu, harka da fasahar zamani da tsarin biyan kudi na zamani, tsarin registar kasuwanci da rage kudin registar zuwa kashi hamsin 50%

Bangaren Wutar Lantarki
“Lallai muna fuskantar kalu bale kan wannan bangaren amma muna kokari kan shawo kan matsalar ta dabaru daban-daban.” Shugaban kasa ya kara da hakan. Ya bayyana wasu jerin ayyuka da gwamnatinsa keyi kan shawo matsalar. Wadanda suka hada da

Alaoji zuwa Onitsha, Gidan Wuta na Delta zuwa Benin da Kaduna zuwa Kano;
Daga Kebbi zuwa Kamba Layi mai Nisan tsawon 62km karfin wuta 330kv DC;
Aikin Gidan wuta na Lagos/Ogun;
Abuja Transmission Ring scheme DA
Northern corridor Transmission Project.
Kuma ya kara da cewa Alkawarin da akayi da kamfanin Siemens zai kawo kuma ya raba wuta 11,000 megawatts a 2023.

Sufuri
A bangaren sufuri, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ta hanyar tsarin SUKUK-Funded, an samu 412km a cikin 643km na hanyoyi da akeso a cimma, ma’ana ansamu kaso 64% acikin aikin.

” a bangaren aikin gadar Niger ta biyu, aikin fila an kammala kuma anfara ayyukan hanya. Shima an samu kashi 48% na aikin.
“Mun gina 102km daga cikin 376km akan aikin titin Abuja-Kaduna-Kano, ansamu kashi 38% cikin aikin. Sannan akwai aikin titin Obajana-Kabba wanda ansamu kashi 87.03%.
Ya sake bayyana cewa hukuma mai kula da titinan gwamnatin tarayya ta kammala gyaran tituna masu tsawon 4000km cikin 5000km da akeson gyarawa.
A bangaren titin dogo kuwa, shugaban kasa yace tarago da yawa an kaddamar dasu akan titin Abuja-Kaduna.
“Hanyar Ajaokuta-itakpe-warri itama angama kuma an hada ta da itakpe zuwa Abuja sannan kuma daga Warri town zuwa warri port.
” Titin Dogo da yataso daga Lagos-Ibadan itama kashi 90% angama kuma za a kara shi zuwa Lagos port wanda zai taimaka wajen rage cunkoso akan hanyar da aka dade an rasa yadda za ayi dashi a Apapa Port.”
“Kano – Maradi titin dogo mai hannu daya, aikin titin dogo na bakin teku da kuma aikin port Harcourt – Maiduguri wadanda suke hade da layinka da suka hada yamma maso gabas da Kamfanonin garin Gombe da Bonny Deep Sea port dukkansu sunanan angama maganarsu.”

Ilimi
Ya ce gwamnatin shi tana kokarin tabbatarwa da tilastawa akan karatun yara na shekara taran farko ya zama kyauta.
“Don samun hakan, mun kaddamar da tsarin samun ingantaccen ilimi na bai duka a Jihohi 17, sannan aka kara kaddamar da kwalejin kimiyya da fasaha na tarayya guda 6, kuma yanzu haka ana gudanar da matakan koyan aiki ga malamai na jihohi gaba daya DA Abuja.

Kasuwancin kimiyya da fasaha
Shugaba Buhari yace kimiyya da fasaha tana taka rawar gani akan ayyukan cigaban kasa ta yarda muka samu kanmu akan duniyar na’u’ra mai fasaha.
“Tin fara aikin ma’aikatar sadarwa ta zamani, aka kaddamar da tsarin sadarwa.”

Gine-gine
Yace gidaje 1,200 akaba na kasa da matsakaita samu, dakuma filaye 520 da sauran kayayyakin rayuwa ta hanyar hadin kai da kungiyoyi masu zaman kansu dakuma bada jingina da tatasar ma Naira 7.7Billion
“Bugu da kari, An bawa mutane 19,210 hayar gidaje na kimanin kudi Naira Biliyan 16.2.”

Halin Dar-dar, Ta’addanci da Rashin Tsaro
Duk da yawan tashin hankulan dake faruwa a kasa, shugaban kasa yace ” yayi bakin cikin abubuwa da kashe-kashen dake faruwa a Katsina da Borno sanadiyyar batagari da suka samu damar Kulle ta Korona”
“Jamian Tsaro zasu kamu masu laifi kuma sukaisu ga kuliya,” ya fada hakan.
Shugaba Buhari ya Kara da cewa” duk kananan hukumomin dasuke karkashin Boko Haram A Borno, Yobe da Adamawa yanzu duk an kwatosu an mayar wa mutanen dasuke da asalin unguwar.”

“Lalacewar tattalin arzikin wannan bangarorin, wanda ya janyo mana rauni a kan tattalin abincinmu, shima ya fara da wowa a hankali ta hanyar cigaba da noma a bangarorin.
“Yana daga cikin matakan tsaurara tsaronmu na cikin gida, aka samar da ma’aikatar kula da walwala na Jami’an ‘yan sanda.”

Shugabanci na tsarin bin doka, fada da cin hanci da kuma dawo da kadarorin kasa
Shugaban kasa yace ” gwamnatinsa zata tabbatar da shugabantar Al’umma ta hanyar bin doka da oda” ya kara tabbatar da cewa “zai kiyaye kundun tsarin mulkin kasa kuma zai kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma”
Akan yaki da cin hanci da da wo da kadarorin kasa, hukumomi masu yaki da cin hanci sun samu nasarori a kotu sama da 1,400 da kuma kwato kudi sama da Naira biliyan 800. Wadannan kudaden ansasu ne a harkokin cigaban kasa.

Matasa, Mata da Nakasassu
Ya bayyana cewa yawan matasa na kasa ” sune gin shikin samun nasarori na kasa”
Akan hakan, zamu kara maida hankali sosai akan ci gaban fasahar su. Da basu dama su baje ilimin su akan kirkiren kasuwanci, bincike da fasahar kamfani da kuma basu dama akan shugabanci don cigaban kasa.

Yace ya bada umarni” duk wani bangare na gwamnati dasu dunga sa nakasassu cikin al’amuransu.
“Mata sun zama wani babban abun lura da darajawa a wannan kasa saboda haka wannan gwamnati zata ci gaba da basu dama da adama dasu acikin gwamnati,”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: