Ranar Dimokradiyya: Nijeriya Ta Samu Dimbin Nasarori, In Ji Gwamnan Gombe

Dimokradiyya

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya yaba wa ‘yan Nijeriya bisa kokarin su na kare demokuradiyya a matsayin tsarin shugabancin da suka zaba a kasar, yana mai cewa shekaru 22 a jere na mulkin demokuradiyya alama ce ta baiwa marar da kunya.

A wani sakon fatan alkhairi da ya mika wa al’ummar jihar kan bikin ranar demokuradiyya ta bana ta hannun Ismaila Uba Misilli, babban Daraktan yada Labarunsa, gwamnan ya bayyana farin ciki ganin yadda “Mulkin demokiradiyyan Nijeriya ya kankama har yake karyata al’adar nan ta nahiyar Afirka da a mafiya yawan lokaci mutum guda ko jam’iyya guda ke shafe shekaru aru-aru suna cin karen su ba babbaka a kan mulki”.

Ya ce a matsayin babbar kasa a duniya, Nijeriya za ta ci gaba da kokarin gina kasa da raya demokiradiyya mai armashi da kyakkyawan yanayin siyasance a Nihiyar Afirka da duniya baki daya.

Gwamnan ya ce, “Bayan shekaru 22 na demokiradiyya a jere, ina iya bugun kirjin cewa demokiradiyya Nijeriya ta kai mizani. Mun ga yadda aka mika mulki cikin lumana daga wata gwamnati zuwa wata, kuma daga wata jam’iyya zuwa wata.

“Kodayake mun dan fuskanci wasu matsaloli, amma in akwai wani abu da muka koya cikin shekarun nan 22, shi ne a matsayin mu na ‘yan Nijeriya, mun zabi tsarin demokiradiyya a matsayin tsarin da muke so a mulkin kasar mu.

“Mun fuskanci matsaloli, muna kuma tinakarar su cikin tsanaki da kwarwar da duniya ba ta yi tsammani ba. Duniya ta sha debe tsammani a kan mu, amma sai mu shawo kan matsalolinmu mu sake farfadowa da sabon karsashi da hadin kai”.

Da ya ke tsokaci kan ci gaban demokiradiyya a Jihar Gombe, gwamnan ya ce, “Mu shaidu ne kan yadda ake iya samar da gagarumin ci gaba mai ma’ana a tsari irin na demokiradiyya”.

Ya ce daga dan karamin gari, yanzu Gombe “ta yi girman da ta kasance jiha mafi saurin bunkasa a fadin kasar nan.”

Gwamna Inuwa sai ya alakanta nasarar jihar kan “jajircewa, zaman lafiya da ci gaban da aka samu bisa kyakkyawar fata da muradin al’ummar mu ga shugabanci na gari da kuma ci gaba.”

Gwamnan ya ce, “A yayin bikin cikar mu shekaru biyu da hawa kan karaga makonni biyu da suka gabata, mun nuna irin dimbin ci gaban da muka  samu a fannonin rayuwa daban-daban, kama daga giggina hanyoyin mota da noma da ilimi da lafiya da ruwan sha da muhalli, da kasuwanci da masana’antu, da bunkasa karkara da birane, da farfado da aikin gwamnati, da tallafawa mata da matasa da dai sauran su.”

Ya ce, “Burin mu shine mu nausa Jihar Gombe gaba ta fannoni daban-daban, tare da daura ta kan tsarin ci gaba mai daurewan da zai zama abun koyi ga sauran jihohin kasar nan, domin mun yi amannar cewa ta hanyar zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan raya kasa da ayyukan yi da damammakin habakar kasuwanci ne kawai zamu iya amfanar da jama’ar mu romon mulkin demokiradiyya”.

“A matakin shiyya, muna kan gaba-gaba wajen samar da hadin kai a yankin, saboda mun fahimci muhimmancin damar da muke da ita na kasancewa a tsakiyar yankin Arewa Maso Gabas.”

“Ta hanyar yin amfani da wannar dama, da damammakin da muke da su a fannin noma, da yin amfani da fasaha a shirye-shirye da tsare-tsaren mu tare da maida hankali kan muhimman ayyukan raya kasa, zamu maida Gombe wata cibiyar masana’antu da hada-hadar noma, da kasuwanci da cinikayya.”

Gwamnan ya kara da cewa duk da kalubalen tsaron da ake fama da shi a yankin na arewa maso gabas, Jihar Gombe tana da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya kuma bada tabbacin cewa “A yau Gombe ce jihar da ake tururuwan zuwa don zama da zuba jaridu a arewa. Mun kuma dorar da hakan ta hanyar damawa da kowa don karfafa alakar gwamnati da jama’a da masu ruwa da tsaki da kuma hukumomin tsaro. Za mu ci gaba da wannan kokari don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai daurewa.”

Ya kuma jaddada amannar Jihar Gombe na tabbatar da hadin kan Nijeriya, kamar yadda ta bada gudunmowar ta a kokarin kwaskwarimar kundin tsarin mulkin da ake yi, yana mai jaddada cewa jihar ta kuma yi amannar cewa demokiradiyya ce kadai hanyar damawa a siyasa bisa doka don dalewa kan madafun iko.

Gwamna Inuwa sai ya jinjinawa ‘yan Nijeriya mamata da wadmdanda ke raye, wadanda suka sadaukar da kansu ga hadin kai da demokiradiyya kasar cikin wadannan shekaru.

Ya ci gaba da cewa “Ina kuma yaba wa dakarun mu na soja, bisa jajircerwa da kwarewar su wajen kare hadin kai da demokiradiyya Nijeriya. Ina kuma yaba wa sauran sassan gwamnati, wato sashin majalisun dokoki da na shari’a bisa gagarumar rawar da suke takawa wajen nausa demokiradiyyar mu gaba”.

A karshe gwamnan ya yabawa kafafen watsa labarai bisa rawar da suke takawa a demokiradiyya da ci gaban kasa, yana mai jaddada bukatar kara hada karfi da karfe don magance matsalar yada labarun karya da kiyayya.

“A matsayin mu na gwamnati, mun himmatu wajen bunkasa walwala da tsaron rayukan al’ummar mu, da karfafa kwakkwarar demokiradiyya da zata hidimtawa al’ummar mu.

“Yayin da nake taya al’ummar mu murnar wannar ranar ta demokiradiyya, ina kira ga jama’a a ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu.”

Exit mobile version