Ranar Keke Ta Duniya: Da Naira 23 Na Sayi Kekena Shekaru 40 Da Suka Wuce -Wani Dattijo 3rd

keke

Wani dan Nijeriya dattijo mutumin Jihar Kano da aka bayyana da suna Ibrahim Dan Maliki ya ce ba shi da niyyan jefar da kekensa mai shekara 40. Mutumin mai shekaru 68 ya bayyana cewa lokacin da ya saya a kan kusan Naira 23, komai na da arha sosai saboda ana iya canza taya a kan farashin Naira 1.

A cewar mahaifin mai yara takwas din, zai ci gaba da hawa keken har sai ya mutu, yana mai nuni da cewa ita ce kawai hanyarsa ta saukaka zirga-zirga. Don bikin ranar kekuna ta duniya a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, BBC News Pidgin ta tattauna da wannan dan Nijeriya, Ibrahim Dan Maliki, wanda ya sayi nasa shekaru 40 da suka gabata.

A hirar da ya yi da jaridar, mutumin ya nuna matukar kaunarsa ga keken kuma ya ce zai hau shi har sai mutuwa ta raba su.

Abubuwa na da arha Mutumin ya lura cewa ya sayi keken a kusan Naira 23, yana mai bayyana cewa murnar da ya yi a ranar sayen ba ta da iyaka. Ibrahim ya bayyana cewa canza taya ya kasance kasa da Naira 1 amma lamarin ya sha bamban a yanzu saboda zai kashe Naira 2000 don yin hakan.

Dukanmu ke da hanyar Dangane da gwagwarmayarsa da masu ababen hawa, mutumin mai yara takwas ya ce hakuri ya kasance kayan aikinsa. Ya kara da cewa abin da masu motoci basu sani ba shi ne hanyar ta kowa ce. A wani hoto da jaridar ta yada a shafinta na Instagram, an ga mutumin dauke da buhu a daure akan keken.

Ga wasu daga cikin martanin jama’a kan labarinsa: sunnydyoung ya ce: “Keke ba ya mutuwa ina taya ka farin ciki saboda ka ji dadinka tsoho.” Julyanah-ta ce: “Ba na bukatar karanta cikakken labarin don sanin cewa shi dan Kano ne.” franky_burna ya ce: “Bikin shirme.” A wani labarin, wani saurayi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarshi cikin salon da ba zai yi saurin mantawa da shi ba.

Mai bikin, a cikin bidiyon da @kingtundeednut ya wallafa a shafin Instagram ya kayatar da wurin taron zagayowar ranar haihuwar nasa cikin shiga na kasaita.

 

Exit mobile version