Wato kullum dabi’ar madigo ci min tuwo a kwarya take yi, na kyamaci dabi’ar matukar kyamata, kuma ina yi wa yaran mu, kannen mu, yayyen mu da matan mu fatan Allah Ya kiyaye su da jefa kai cikinta. Saboda haka ne ma nake ta nazartar shi kan shi madigon da kuma masu aikata shi, don haka na tsunduma cikin kogin bincike ta fuskoki mabanbanta, ciki kuwa har da zama da abokiya mai wannan dabi’ar, amma da nufin nusar da ita ta ji tsoron Allah ta daina, tare da nuna mata illolin shi a addinance da kuma kiyaye lafiyarta. Amma kafin nan ina mai tabbatar muku madigo tsakanin mata ya zama ruwan dare.
Kwanakin baya a cikin wannan jaridar ta ranar Alhamis 31 ga watan Disemba 2020, na yi wani rubutu mai taken ‘Alamomi 50 Da Ake Gane Mata ‘Yan Madigo” wanda har na dan kawo takaitaccen tarihin wata hatsabibiyar mawakiya da ta shahara ta kuma yi fice a harkar madigon, wadda ita ce kusan ummul-aba’isin samuwar shi.
Matar ‘yar kasar Girka wadda ta yi rayuwa tsakanin 1464 – 1526 mai suna Sappho. Saboda jajircewarta akan kare ‘yancin mata, sai ya kasance duk inda Sappho ta je ko za ta je, za ka samu mata ne zalla zagaye da ita, dalili kuwa shi ne yadda take wake-wakenta gabadaya suna takalo wa mata da wani maganadisun sha’awar junansu ne, ma’ana wakokin da take rerawa kamar ishara ne ga matan da ke sauraron wakar ga neman ‘ya’ya mata ‘yan uwansu ya fi neman jinsin maza. Sannan tana rera wakar cikin sigar sha’awa da yanayin takalo wa matan da ke zagaye da ita sha’awarsu.
To babban abin da yake ba ni tsoro yanzu shi ne tun ana kawar da kai ana Allah-wadai da wannan dabi’a, anan kasashen mu idan ba mu yi hankali ba zai zame mana jiki kamar yadda kasashen yammacin duniya suke ta kokarin zamar da shi. Wani abin mamaki da takaici shi ne a kasashen Turai, a kasar Iceland misali, a shekarar 2009 har zaben Firaminista suka yi wacce ta kasance cikakkiyar ‘yar madigo kuma mai da’awar shi, wato Johanna Sigurdardottir, da ta kasance mace ta farko mai matsayin Firaminista wacce ta fito fili ta yi ikirarin cewa ita ‘yar madigo ce.
Haka zalika, a shekarar 2017, Firaministar kasar Serbia, Ana Brnabic ta kafa tarihi wajen shiga taron gangami na ‘yan madigo da luwadi. Ta yi hakan ne da zummar nuna goyon bayanta gare su, wacce ita ma kanta ‘yar madigon ce. Ana Brnabic ita ce mace ta farko kuma wacce ta fito ta bayyana wa ‘yan kasarta ita ‘yar madigo ce.
Yanzu ko in ce tuntuni a kasashen turawa aure suke yi wanda kuma cikin wadannan kasashe da dama cikinsu sun ma halasta abin, misali a kasar Amurka a da su kan yi auren amma ba don kasarsu ta halasta ba. Kuma su ma al’ummar su da dama suna nuna musu kyama da Allah-wadai. Amma a yau sun samu rinjaye sosai inda idan mutum ya fito ya nuna rashin goyon bayan shi a gare su, sai a dauke shi kamar wani bagidaje. Kuma yanzu haka sabon Shugaban Kasar Amurka Mista Joe Biden ya aike wa majalisa da daftarin kudirin dokar halasta auren jinsi domin zama da shi doka.
To, ni abin da ke daure min kai, wai shin me ke sa mata suke shiga wannan lamari ne? Shin wai wannan lamari sabon abu ne kamar yadda muke ganinsa ko kuwa yanar gizo ke kara rura wutar abin kasancewa duniya ta zama dunkulalliya wuri guda?
A binciken da na yi su wadannan masu wannan dabi’a ta madigo sun yi imani da cewa dabi’ar ba wani abu ba ne na daban kamar yadda mutane da dama suke zato. Su imanin su shi ne wai suna da bambanci da sauran jama’a ta fuskoki mabanbanta kuma sune ganin cewa ai haka Allah Ya halicce su.
To, amma idan ka dubi abin ta fuskoki da dama wannan lamari ya saba wa hankali ta ko’ina. Misali idan ka dauki bangaren haihuwa, ko shakka babu idan aka yarda da madigo to haihuwa kuma karewa za ta yi, tunda Allah da ya hallice mu, ya yi mu ne dauke da kwayar halittar maza da kuma mata, wanda idan babu wannan to ba mutum, ko dabba ba zai samu ba. Wasu sai su ce ai akwai mafita tunda mutum na iya bada kyautar maniyyin sa, wato ‘sperm donation’, ko kuma a je gidan marayu a dauki yaro a goya, wato ‘child adoption’.
A ce mun yarda da (sperm donation) sayar da maniyyi, mata biyu sun yi aure suna bukatar haihuwa, sun samu wani ya ba su maniyyi sun yi nasara an yi haihuwa lafiya. To yaro ko yarinyar da aka haifa mene ne matsayin shi, ya na da uba ko bai da shi? Hakika mun san yana da uba to amma ina uban yake? Babu. To kun ga an saka wannan ya cikin matsala a rayuwar sa har abada, musamman irin matsaloli da zai fuskanta a wajen jama’a. Bincike ya nuna yara da suka tashi a irin wadannan gidaje sukan fuskanci matsaloli bila adadin, fiye da takwarorin su wadanda suka taso a gidajen sunnah ma su uwa da uba.
Kuma ai kusan duk mun sani kamar yadda uwa ta ke da muhimmanci haka uba ya ke wajen tarbiyya da kula da yara.
A wani bangaren kuma shi wannan (sperm donation) bada maniyyi, din ma yana da na shi irin matsalolin barkatai.
A takaice zan iya cewa wannan dabi’a ta madigo kawai halayya ce ta banza da dan adam ya kirkiro wa kansa da sunan wai “haka suke sha’awa saboda haka kowa ma yana da damar bayyana yadda irin sha’awarsa” Kuma a hakan suke neman su saka wasu ta hanyar jan ra’ayinsu, da cewa ai Allah ne, ya halicce su a haka.
Wannan kenan. To amma wai shin mene ne dalilan da kan sa mutane fadawa cikin wannan dabi’a rana tsaka?
A wani bincike da na gudanar, duk da cewa sakamakon bai isa ya zamanto an yanke hukunci a kan wannan lamari ba, amma zai iya ba da wani haske. Ga wasu daga cikin abin da na ke ganin ke iya jefa mata da dama cikin harkar madigo.
Zamani: A yau muna cikin wani zamani ne mai rikitarwa, wanda ya zo mana da abubuwa kala-kala. Wasu dabi’un da a baya ake kyama da hantara yanzu sai ka ga sun zama abin ado. Madigo na daya daga cikin ire-iren wadannan abubuwa. Duk da cewa har yanzu mutane da dama suna kyamar sa, to amma idan aka sake zai fara zama ba komai ba kamar yadda matsayin sa yake a kasashen turawa da dama. Su ma kansu turawan a ‘yan shekaru kadan da suka wuce ba haka abin ya ke ba.
Rashin samun auren mata: Da alama yawaitar rashin yin aure a tsakanin ‘yan mata na jefa wasu mata cikin wannan harkar, duk da cewa ba a taru aka zama daya ba tunda wasu matan da auren su suke aikata wannan masha’a. Amma lallai rashin samun aure na iya jefa mace cikin wannan lamari domin bincike ya tabbatar da hakan. Kuma idan ta saba ko ta yi aure zai yi wuya ta daina.
Rashin ilimin addini: Sanin kowa ne addini ya nuna haramci, da babbar murya, na madigo da danginsa irin su luwadi. Saboda haka idan mace ta samu ilimin addini daidai gwargwado zai yi wuya ta fada cikin wannan dabi’a. Duk da cewa wasu kan take sani su yi abin da ransu ke so, to amma samun ilimin zai taimaka wajen rage mata masu fadawa cikin wannan bala’i.
Abota da masu dabi’ar: Wai an ce ‘nuna min abokinka sai in gaya maka ko kai wanene’. Wannan gaskiya ne. Abokai na taka rawa sosai a cikin rayuwar mutum. Ko dai kai ka rinjaye su, ko kuma su rinjaye ka. Saboda haka abota da mace ‘yar madigo na iya jefa yarinya cikin hatsarin madigo. Wannan kuma ya shafi ‘yan mata hadda wasu matan auren.
Yanar gizo: A wannan zamani ba wata magana da za mu yi mu manta da zancen yanar gizo da yadda take da tasiri a cikin rayuwarmu. Wannan tasiri na ‘Internet’ ya mai da samun duk wani labari da sakonni cikin sauki. Hakan ya sanya wannan dabi’a ta madigo ta kara bazuwa da kuma tasiri sosai. To wasu matan ta amfani da yanar gizo sukan koyi madigo, ko ma su hadu da wasu abokai da za su rinjaye su. Bincike ya tabbatar akwai dubban zauruka wato ‘groups’ a Facebook da WhatsApp daban-daban na ‘yan madigo.
Kallace-kallacen fina-finai da karance-karancen littatafan ‘yan madigo: Kasuwar fina-finai da na littattafai cike take makil da labaran ‘yan madigo da su Luwadi a yanzu. Don haka idan mace ta kasance ba ta da wata dabi’a sai wadannan kallace-kallacen ko karance-karancen, idan ba a yi hankali ba za ta iya fadawa cikin hatsarin shiga harkar madigon.
Shaye-shaye: Idan mace na shaye-shaye akwai yiwuwar ta fada cikin wannan dabi’a ta madigo, musamman idan tana tare da masu yi. A yayin da take hali na maye ba abin da ba za ta iya aikatawa ba.
Makarantar kwana (boarding school): Tabbas ‘yan mata da yawa masu yin madigo sun koyo shi ne a makarantun kwana, domin a wurin za ka taras ba irin macen da babu ita. Idan ba a yi sa’a ba yarinya ta fada hannun abokiya mai yi, kuma hukumar makaranta ba sa kula sosai, sai ki ga ita ma ta fada ciki tsundum. Kuma idan an saba a makaranta sai ki ga an dawo gida an ci gaba da yin hakan.
Rashin wayar wa yara kai da wuri: Dabi’ar mu ne musamman mu a Arewacin Nijeriya na rashin iya yi wa ‘ya’yanmu magana akan wani al’amari mai muhimmanci. Wani lokacin saboda rashin sani sai ka ga yara sun fada cikin irin abubuwa masu hatsari. Idan yarinya ba ta san zancen madigo ba ko kuma iyaye da ya kamata su hankaltar da ita ba su yi, hakan ba sai ki ga ta je ta samo gurguwar bayani akan abin. Kafin a farga sai ki ga yarinya ta fada a ciki. Allah ya kyauta.
Bari mu tsaya nan, in ya so nan gaba idan Allah ya bayar da iko sai mu nemo mafita.