Daga Rabiu Ali Indabawa,
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Hajiya Aisha Buhari, ta koka kan yadda ake cigaba da sace dalibai, mata da ’yan mata ta hanyar ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya, musamman a Arewacin Nijeriya.
Aisha a cikin wata sanarwa a yayin Bikin Ranar Mata Ta Duniya da aka wallafa a shafinta na Tiwita, ta ce, “a matsayina na uwa, Ina nuna bakin ciki da radadin wadanda abin ya shafa da iyalai.
“Ni kuma ban san tasirin da wadannan sace-sacen za su iya yi ba wajen juya akalar nasarorin da muka samu har yanzu, musamman ta fuskar ilimin ’ya’ya mata da kuma auren wuri.”
Ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi amfani da matakan da suke da shi wajen kawo karshen sace-sacen mutane.
Yayin da take yaba wa kokarin mata da ‘yan mata a yakin da ake yi da annobar cutar Korona, ta lura cewa, wannan annoba ta yi matukar tasiri ga mata, ta hargitsa ilimi, sana’o’i da kuma yawaitar rikice-rikicen cikin gida.
Sai ta bukaci kowa da cewa, bayan yada sakon yarjejeniyar Korona, ya kamata su tuna tare da tallafa wa wadanda cutar ta shafa.