Yusuf Shuaibu">

Ranar Rage Harajin Shigo Da Motoci Za Ta Fara Aiki – Kwastom

Hukumar Kwastom ta bayyana ranar da za a kaddamar da rage harajin shigowa da motoci kafin wannan watan da muke cikin. Shugaban hukumar kwastom, Hameed Ali shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dallancin labarai ta kasa (NAN) a ranar Asabar a garin Abuja. Ya bayyana cewa, an yi wannan kokarin ne bisa umurnin da ma’aikatan kudade da kasafi da tsare-tsaren kasa ta bai wa hukumar kwastam din.

NAN ya ruwaito cewa, a ranar 26 ga watan Junairu ce, shugaban hukumar kwastom ya bayyana cewa, hukumarsa tana jiran umurni daga ma’aikatan kudade da kasafi da tsare-tsaren kasa kafin ta fara aiki da wannan dokan rage shigo da motoci cikin kasar nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar kudade ta shekarar 2020, a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2020, wanda zai rage yawan harajin shigo da kayayyaki na motoci cikin kasar nan.
“An gabatar mana da wannan doka. Mun sami umurnin minista a wannan mako domin fara aiki a kai, ko da yake akwai bukatar kulawa da wasuu matakai a kan yadda za a kayyamar da dokar.
“Dole ne mu canja dokokinmu domin su dace da wannan sabuwar doka. Kamar yadda aka sani ne harajin shigowa da motoci ne kadai za a iya ragewa tun daga kashi 35 zuwa kafi biyar.
“Domin haka ne, dole mu canza yanayin dokokinmu domin su dace da wannan sauran doka, ina matan za su samu nasarar kammalawa cikin kwana biyu, inda minista za ta duba sannan ta amince da abubuwan da zamu yi.
“Ina fatan daga yanzu ba za a dauki tsawan lokaci ba, ina fatan daga nan zuwa makonni biyu kafin a fara amfani da wannan doka. Za mu yi kokari sosai wajen ganin an fara amfani da wannan doka,” in ji shi.
Shugaban hukumar kwastom ya ci gaba da bayyana cewa, wannan sabon doka zai taimaka wa kasar nan wajen inganta sufuri domin saukaka wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da suke sha wajen harkokin sufuri. Ya jaddada cewa, yawan biyan haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar nan suke kara haifar da fasahaurin motoci a cikin kasar nan. Mista Ali ya kara da cewa, kididdigar da suke da shi ya nuna cewa, ana yin safarar motoci tsakanin motoci 300,000 zuwa motoci 400,000 daga kasar Jamhuriyar Benin zuwa Nijeriya. Ya ce, wannan rage haraji musamman ma a bangaren sufuri zai karfafa wa Nijeriya ta fannin motocin dauko kayayyaki da ayyuka da kuma na dauko fasinjoji. Ya ce, wannan doka cikin karamin lokaci da za ta samar wa Nijeriya kudade masu yawa tare da amfanar da ‘yan Nijeriya wajeb saukaka harkokin sufuri a cikin kasar nan.

Exit mobile version