Ranar Talata Za’a Bude layukan Sadarwa A Zamfara –Gwamna

Daga Hussaini Yero,

Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Bello Muhammad Matawalle ya bada Umarnin Bude layukan Sadarwa da ke fadin Kananan hukumomin sha uku da suka kwashe tsawon kwanaki tamanin da daukewar layukan Sadarwa Sabo da matsalar ‘Yan Bindiga .

Matawalle Maradun ya bayyana haka ne a Taron zabar sabbin Shugabani na jam’iyyar APC na Jihar a Yau Asabar.

‘kuma ya bayyana cewa, sakamakon sauki da aka samu na matsalar ‘Yan Bindiga ya sanya bada Umarnin Bude layukan Sadarwa daga nan zuwa ranar talata mai zuwa.kuma wannan zaiba wanda bai yanki katin zabe ba,damar mallakar katin zaben, inji gwamna Matawalle.

Idan ba a mantana aranar Asabar 4/9/2021 , Gwamna Matawalle ya bada Umarnin rufe layukan Sadarwa dan samun damar yima Yan Bindiga kofarago dan gamawa dasu.

Exit mobile version