Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu

bySulaiman
9 months ago
Mazan jiya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin iyalan hafsoshi da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Gwamnan ya halarci bikin tunawa da sojojin da suka rasu a ranar Laraba a harabar baje kolin kasuwanci da ke Gusau, babban birnin jihar.

  • Da Ɗumi-ɗumi: Sojoji Sun Haramta Amfani Da Jirage Marasa Matuƙa A Arewa Maso Gabas
  • Karramawa: Ma’aikatan Kano Sun Yaba Wa Jagorancin Gwamna Abba Na Tausayi

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Daudaa Lawal ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga Rundunar Sojojin Nijeriya, reshen Jihar Zamfara a yayin ƙaddamar da tambarin tunawa da sojojin da suka rasu na shekarar 2025.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya duba wani tambari da rundunar sojin Nijeriya suka ɗora. “Gwamna Lawal shi ma ya jagoranci shimfiɗa furannin sannan ya ba da umarnin a yi shiru na minti ɗaya domin karrama jaruman da suka rasu.”

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya jaddada cewa yau ranar tunawa da jaruman da suka mutu ne, kuma kira ne ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki ɗaya.

“Ana yi bikin tunawa da sojojin Nijeriya ne a duk faɗin ƙasar a ranar 15 ga watan Junairu na kowace shekara domin tunawa da kuma jinjina wa waɗanda suka sadaukar da ransu da tsofaffin sojojinmu da suka yi fafutuka wajen kare martabar yankin Nijeriya, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu domin mu samu damar zama lafiya.

“Muna godiya kuma muna daraja sadaukarwar da suka yi, wanda ya kawo sauyi a rayuwarmu a yau. Tare da godiya da mutuntawa, mun yi alƙawarin ci gaba da tunawa da su tare da tallafa wa iyalan ​​da suka bari.

“Wannan rana ta zama karramawa ga jaruman mu da suka mutu da kuma kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki ɗaya. Wata dama ce ta yin tunani a kan sadaukarwar da waɗancan jajirtattun mutane suka yi. Ya kamata sadaukarwar sojojinmu ya zaburar da mu wajen habaka zaman lafiyar da muka samu a yau da kuma fafutukar samar da gobe mai kyau.

“Kada mu manta da muhimmancin tallafa wa iyalan waɗannan jarumai da suka mutu da kuma tsofaffin da suka yi yaƙi domin mu yi barci cikin lumana da kuma waɗanda har yanzu suke da rauni na hidimar da suke yi wa ƙasa. Juriya da sadaukarwarsu dole ne ya tunatar da mu alhakin da ya rataya a wuyanmu na tabbatar da jin daɗinsu. Ta yin haka, muna girmama sadaukarwar da suka yi, kuma muna nuna godiyarmu ga jajircewar da suke yi ga al’ummarmu.”

Gwamnan ya bayyana cewa, duk da ƙarancin kayan aiki, ana samun gagarumin ci gaba wajen magance matsalolin tsaron cikin gida ta jihar ta hanyoyi daban-daban.

“Wannan gwamnatin ba wai kawai ta ba da tallafin kayan aiki masu muhimmanci ba ne. Har ila yau, ta kuma tabbatar da jin daɗin iyalan jami’an da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Mun himmatu wajen biyan kuɗaɗen jinya ga waɗanda suka jikkata a ayyukan tsaro da tallafa wa jaruman mu da iyalansu.

“A wani bangare na ƙoƙarin da gwamnatina ke yi na daƙile matsalolin tsaro, mun samar da motocin tsaro sanye da na’urori na zamani, tare da babura ga jami’an tsaro. Wannan yunƙurin na ƙara haɓaka damarsu ta hanyar shiga wurare masu rintsi don tabbatar da cewa babu wani yanki na jiharmu da ke a baya.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa dabarun haɗin gwiwa tare da jihohi makwabta, hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki don tunkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar jiharmu, domin haɗin gwiwa shi ne babban jigon samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Next Post
Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 7 Cikin Jerin Sassan Da Ba Za A Iya Dogaro Da Su Ba

Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 7 Cikin Jerin Sassan Da Ba Za A Iya Dogaro Da Su Ba

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version