Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu matuka gaya wajen magance yaduwar cutar da ke karya garkuwar jiki wato Kanjamau don dakile ta ya zuwa shekara ta 2030.
Gwamnan ya jaddada aniyar ce ta cikin wani sakon da ya fitar ta hannun babban mai taimaka masa kan hulda da ‘yan jarida Ismaila Uba Misilli don alamta ranar yaki da cutar Sida ta duniya wannan shekarar da aka yi wa taken ‘Nuna goyon baya da daukar dawainiya’ yayin da taken ranar a Nijeriya ya kasance ‘Tare za mu ga bayan cutar Sida a tsaka da annobar Korona: je ka yi gwaji’.
Da ya ke bayyana farin ciki kan raguwar da aka samu a yaduwar cutar a jihar Gombe, Gwamna Inuwa ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa da tallafawa shirin yaki da cutar ta hanyar tabbatar da wadatuwar kayan gwajin cutar a dukkannin asibitocin jihar, da kara kokari kan kula da masu cutar da tallafawa marayu da yara marassa galihu tare da tabbatar da ingantacciyar kulawa ga masu dauke da cutar.
Gwamnan ya ce duk da cewa annobar Korona ta kara tabarbarar da matsalolin kiwon lafiya da dama, gwamnatinsa ta himmatu sosai kan yaki da cutar ta kanjamau wato SIDA don cimma burin kawar da ita a Jihar Gombe ya zuwa shekara ta 2030.
“Bincike na baya-bayan nan da aka gudanar kan cutar a jihohin kasar nan ya nuna cewa yaduwar cutar ya ragu sosai a Jihar Gombe, daga kaso 8.5 cikin dari a shekara ta 2006 ya zuwa kaso 1.3 kacal, wanda hakan wata babbar nasara ce ga jihar. Wannan na nuni da yadda hadin kai ke haifar da da mai ido kan yakin cutar da wannar gwamnati da masu ruwa da tsaki ke yi”.
To, sai dai fa ya ce ba lokaci ne na murna ba tukunna, domin har yanzu da sauran rina a kaba kafin cimma wannan buri na ganin bayan cutar.
Gwamnan sai ya umarci ma’aikatar lafiyan jihar ta tabbatar da samar da kariya ga likitoci da malaman jinyan dake gaba-gaba wajen yaki da cutar ta SIDA.
Ya kuma jinjina tare da godewa kungiyoyi da hukumomi da ma’aikatan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa tallafi da jajircewarsu kan yaki da cutar a tsawon shekaru.