Ranar ‘Yan Jarida Ta Duniya 2021: Lokacin Tunawa Da Gwarzaye A Fagen Yada Labarai

'Yan Jarida

Daga Al-Amin Ciroma,

A yayin da a ke tunawa da ranar ‘yan jarida ta duniya a wannan shekara ta 2021, mai taken ‘Samar da ingantattun bayanai domin amfanin al’umma,’ yana da matukar amfani a kuma kallon gudunmawa gami da rawar da ‘yan jaridan ke takawa yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasashe daban-daban.

Kamar dai yadda aka sani, Majalisar Dinkin Duniya ce ta kebe wannan ranar, inda ta tabbatar da 3 ga Mayun duk shekara, ta zama rana ce ta musamman domin bibiyar muhimmancin ayyukan ‘yan jarida, wadanda a wasu lokutan su ke sayar da rayukansu a fagen aiki.

Manazarta dai sun ce taken ranar na bana, ‘Samar da ingantattun bayanai domin amfanin al’umma,’ ci gaba ne daga taken ranar ta bara, wato: “Aikin jarida ba tare da tsoro ko alfarma ba.”

Sanin kanmu ne cewar kasashen da dama a yau suna fama da matsaloli da suka shafi na tsaro da yunkurin tayar da komadar tattalin arziki, don haka a fagen tsaro dai, babu abin da yake saurin samar da nasara illa gano bayanan sirri da mika su ga jami’an tsaro, wadanda a kullum su yin amfani da shi, wajen dakile muggan manufofin mahara ko ‘yan tawaye, ko kuma ‘yan ta’adda.

Shakka babu, a yau dai duniya za ta yi na’am da taken ranar na bana, sabili da yekuwa da kuma wayar da kai da taken zai yi ga al’umma. A bara, yayin da duniyar da shiga cikin mawuyacin yanayi na annobar cutar Korona, hakan kuwa bai hana ‘yan jarida baje-koli gami da sayar da rayukansu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba.

Hakan ta sanya, wasu daga cikin fitattu kuma gwarzaye daga cikin ‘yan jaridar suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda kididdiga ta nuna akalla ‘yan jarida sama da 600 ne suka rasu a kasashe da dama sanadiyyar annobar ta Korona.  Kasar Indiya ce mafi yawan adadi daga cikin wannan, inda ta rasa fitattu kuma gwarzaye kusan 165, sanadiyya cutar.

Haka kuma da dama cikin ‘yan jarida sun rasa rayukansu a yayin da suke gwagwarmayar aikawa kafafensu labarai na rigingimu a yaki da ake tafkawa a kasashe da dama.

Daga shekarar bara zuwa yanzu dai, an sami akalla ‘yan jarida guda 236 suka ransu a fagen Daga, a yayin gudanar da ayyukansu. A nan ma, kasar Syria ce ke kan gaba wajen rasa rayukan ‘yan jarida, inda aka ruwaito cewar ‘yan jarida sama da 138 ne suka rasu a lokacin da suke kokarin harhada rahotanni.

Hatta ni kaina, na taba halartar wani shiri na musamman da Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta yi, inda ta gayyaci ‘yan jarida daga kasashe da dama a Afrika, domin su halarci kasar Somalia, a karkashin shiri na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, don su gane wa idanunsu irin gwagwarmayar da dakarun kwantar da tarzoma daga kasashen Afrika suke yi na wanzar da zaman lafiya a kasar ta Somalia da wasu makwabtansu.

Babban darasi da muka koyo a wannan tafiya dai shi ne, mahimmancin aikin dan jarida da taka-tsantsan da ya kamata kowane bangare ya yi. Abin da ya fi mahimmanci a nan shi ne yadda na ga ‘yan’uwana da suka halarci taron daga kasashe da dama, kowa ya bar kasarsa, ya bar ‘yan’uwa, iyali, da abokan arziki, ya kuma sayar da ransa domin ya gudanar da aikinsa.

Ko ba a ce komai ba, ya zama wajibi a duk lokacin da aka sami irin wannan yanayi, a rika ambaton mahimmancin aikin jarida, domin al’umma ta fuskanci irin hadari da sayar da rai da ake yi. A gefe guda kuma su tuna irin gudunmawar da ‘yan jarida ke yi domin ci gaban al’ummar duniyar.

Idan aka kalli irin wadannan alkalumman, za a fahimci mahimmancin aikin dan jarida a cikin al’umma da kuma gudunmawar yak e bayarwa domin wayar da kai, gami da aika sakonni yadda ya dace ga duniya.

Irin wadannan batutuwan da ma sauran nazari da fitattun ‘yan jarida na duniya suka yi ne, ya haifar da taken ranar na bana, wato mahimmancin bayanai domin amfanin al’umma. Babban abin da ya fi mahimmanci na tunawa da wannan babbar rana ta ‘yan jarida shi ne, hada kawunan mutane tare da yin la’akari da halin da duniya ke ciki a yau.

Tabbas, bayanai za su amfani al’ummar duniya a yau ta fuskoki da dama, kamar yadda na ambata a baya. Haka ma babu dan jarida da zai samu nasarar harhada rahotanni masu inganci, ba tare da samun gamsassun bayanai ba. Ta nan kadai hanyar da rahotonsa zai cika rahoto, mai cike da adalci ga kowane bangare.

A gefe guda kuma, idan har duniya ta fahimci mahimmancin bayar da wasu bayanan sirri ga jami’an tsaro, to, an yi maganin manyan matsalolin tsaro kusan na kasha 70 a cikin 100. Domin kuwa jami’ai za su yi amfani da bayanan wajen dakile muggan manufofin ‘yan ta’adda, wadanda a yanzu suke yaduwa kamar ruwan dare.

A daidai lokacin da bikin ranar tunawa da gwagwarmayar ‘yan jarida ya cika shekaru 30 daga shekarar 1991 zuwa 2021, yana da matukar mahimmanci kowane dan jarida ya fahimci Mustahabbai gami da Farillan aiki da kuma nauyin da ya rataya a kansa.

Tun da fari dai, a ranar 29 ga Afilun 2991 ne wasu fitattun ‘yan jaridan Nahiyar Afrika suka taru a Birnin Windhoek da ke kasar Namibia, domin tunawa da ‘yancin fadin albarkacin baki, musamman ma a lokacin da Nahiyar ke fuskantar manyan tarzoma ta kowace fuska.

Taron na farko da aka yi a kasar Namibia, ya sami tagomashi Kungiyar Ilmin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO), tare da hadin gwiwar wasu manyan kungiyoyin duniya guda 12 da kuma babban zauren ‘yan jarida na kasashen duniya. Mahalarta taron na farko dai sun fito ne daga kusan kasashe 38 na duniya.

Abin da aka fi tunawa da shi a ranar taron na farko shi ne irin kwarin gwiwa da gudunmawar da Firai Ministan Kasar ta Namibia, Hage Geingob (na lokacin ya bayar), kafin zamansa shugaban kasar na uku. Ya bayyana mahimmancin ‘yancin fadin ra’ayi da kuma turakun adalci na aikin jarida, a yayin da yake bude taron.

A bana dai, an samar da taken ne, domin a kara wayar da kan al’umma dangane da mahimmancin bayanai ta kowace fuska, ita kuma gwamnati ta jajirce ta bai wa ‘yan jarida damar fadin albarkacin bakinsu da ra’ayoyinsu na aiki daidai gwargwado.

‘Yan jarida da dama a Nijeriya sun jinjina taken ranar na bana, inda suke yin kira ga dukkanin ‘yan’uwansu ‘yan jarida a fadin kasar da ma duniya baki daya, su yi riko da ayyukansu, kana su rika yin amfani da bayanai matuka wajen gudanar da ayyukansu.

Ta wannan hanyar ne kadai za a kara inganta aikin jarida gami da tsaftace harkar wayar da kai domin tabbatar da kafa ayyukan kwarai a fagen yada labarai.

 

Shin me ya kamata al’umma ta yi a lokacin da ake tunawa da irin wadannan gwarzayen a cikin al’umma? Wannan amsa ce da kowannenmu yake da ita a cikin ransa. Ranar tunawa da ‘yan jarida ta duniya, rana ce da ya kamata duniya ta rika jinjina da kuma yabawa masu wayar da kan al’umma a fagen jarida, musamman ma wadanda har gobe suke ci gaba da sayar da rayukansu da kuma wadanda ma suka amsa kira, suka rasu.

 

Ba zai zama almubazzaranci ba idan ana shirya manyan taruka ko gangami domin tunawa da irin wadannan gwargwayen, tare kuma da bayar da manyan kyaututtuka ga wadanda suka ciri tuta, ko da sun riga mu gidan gaskiya ne.

 

Exit mobile version