Abubakar Abba" />

Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya: Malaman Addinai Sun Gudanar Da Gamgami A Kaduna

An warae ranar 21 ga dukkan watan Satumbar ko wacce shekara don gudanar da gangamin zaman lafiya a fadin duniya.

Hakan ne ya sanya wata Gidauniya mai zaman kanta a jihar Kaduna da ake kira a turance,The Eye Opener ta gudanar da tattaki a wasu titunnan dake cikin jihar da nufin wayar da kan alummar jihar a kan mahimmancin daman lafiya.

Bugu da kari, wasu daga cikin malaman addinai dake a cikin jihar, suma sun shiga gangamin da Gidauniyar ta shirya.

Shugabar Gidauniyar  Margaret Gwada Julius ta sanar da cewa, dalilin day a sanya Gidauniyar ta gudanar da gangamin na yin tattakin a jihar shine, don a kara hada kawunan alummar jihar agu daya, musaman ganin cewar,  wasu yan siyasa ne a jihar suke haddasa rigingimu da kuma raba kan alummar jihar.

Ta ci gaba da cewa, Gidauniyar tana yin iya kokarinta wajen ganin ta dawo da martabar da aka san Kaduna da ita.

Madame Margaret ta kuma jaddada cewa, har yanzu ba’a fitar da rai ba wajen ganin an sake hada kawunan alummar jihar a guri guda, inda ta yi nuni da cewa, akwai bukatar a hada’a hannu waje daya don a cimma burin hakan.

Ta kara da cewa,“Mun hadu ne a nan mu sama da mata 200 da malaman addinai dake a cikin jihar da kuma sauran amsu ruwa da tsaki don wanzar da mahimmacin zaman lafiya, musamman a jihar Kaduna.

Ta yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da kuma gwamnatin tarayya dasu hada karfi da karfe don tabbatar da zaman lafiya musamman a yankin Arewacin Nijeriya.

Shima da yake nashi jawabin sannen Fasto a jihar Kaduna Yohana D Buru ya jinjinawa shugabar Gidauniyar a kan gangamin data shirya.

A cewar sa, “ Mun kuma gayyato wasu daga cikin Fastoci da Malaman addinin Musulunchi don suma su halarci taron na gangamin, inda mukayi tattakin tatre dasu da numin wanzar da zaman lafiya, musamman a jihar Kaduna.”

Ya yi nuni da cewa, “Idan babu zaman lafiya babu wani ci gaba da za’a iya samu a cikin kowacce alumma, inda ya kara da cewa, zamuci gaba da yin addu’oin zaman lafiya, musamman don Allah ya kawo mana dauki a kan kalubalen da ake fusaknta a daukacin fadin duniya.”

Itama a nata jawabin, wata kwarariya a cikin kungiyar mabiya addinai mabanbanta ta kasa da kasa Hajiya ramatu Tijjani  ta yi nuni da cewa, ranar ta zaman lafiya ta duniya wani kokarin ne hada zumunta da kuma kare tashe-tashen hankula a tsakanin alumma dake a fadin duniya.

Ramatu wadda kuma ita ce Jakadar wanzar da zaman lafiya ta kara da cewa,sakamakon rikice-rikicen addini dana kabilanci da suka auku a baya a jihar, hakan ya janyo shar rayukan darurun allama a jihar da kuma yin asarar dukiyoyi.

Ramatu ta kuma yi nuni da cewa, akwai bukatar Musulmai da Kiristoci, musamman dake a cikin kasar nan su san da cewa, dukkan su sun fito ne daga tsatson Annabi Adam da kuma Hauwa’u.

Shima a nasa jawabin Shugaban kungiyar yan jarida na reshen jihar Kaduna Kwamarade Adamu Yusuf ya nuna jin dadinsa a kan gudanar da gangamin da Gidauniyar ta shirya, inda ya yi nuni da cewa, idan babu zaman lafiya baza’a iya samun wani ci gaba ba a cikin kowacce alumma.

Shima wakilin kwamishinan yan sanda na jihar CSP Uzairu Abdullahi ya bai wa daukacin alummar jihar tabbatacin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Exit mobile version