Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A kwanakin baya ne kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Bauchi (NBA) ta rantsar da sabbin shuwagabaninta wadanda za su ja ragamar shugabancin kungiyar na tsawon shekaru biyu a bisa tsarin wa’adin da NBA take tafiya a kai.
Taron rantsuwar da kuma mika ragamar shugabancin ga sabbin wanda aka gudanar da shi a babban kotun jihar Bauchi a wannan ranar ya samu halartar dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar shari’a.
LEADERSHIP A Yau ta rawito cewar Barista M.M Mai Doki ne ya zama sabun shugaban NBA bayan da aka kada kuri’a a tsakaninsa da Barista Muh’d Umar. Mai-Doki ya kada Umar ne dai da kuri’u 64, a yayin da shi kuma Umar ya samu kuri’u 49, a bisa haka ne Mai-Doki ya lashe zaben, ya kuma amshi mulkin ne daga hanun Barista Naseer Jumba, inda ya mika masa mulki da kuma rantsar da shi a wannan ranar.
Sauran sabbin shugabanin da suka kama aiki a wannan ranar sun hada da Barista Sa’adatu I. Ebeneh a matsayin sakatariyar jin-dadi da walwala na NBA, sai kuma jami’in hulda da jama’a Barista A.S Idris.
Jim-ka-dan bayan kammala zaben manema labarai sun nemi jin ta bakin sabon shugaban kungiyar lauyoyi na kasa reshen jihar Bauchi Barista M.M MaiDoki, inda ya fara da nuna matukar godiyarsa ga Allah da ya ba shi wannan kujera, sai ya bayyana hakan a matsayin kalubalen rayuwa da ya samu kansa a ciki.
Ya ce, “Ina da burin yin amfani da wannan damar da na samu wajen ganin na hada kan mambobin wannan kungiyar da suke wannan jihar, ganin cewar a halin yanzu ana samun rarrabuwar kawuna, wasu a bisa dalilai muhimmai, wasu kuma babu ma dalilan amma a koma yaya al’amarin yake, ba fatanmu bane wannan rarrabuwar ya ci-gaba da faruwa a tsakani. Babu wani hadin kai da za a jimma ba tare da hadin kan mambobin wannan kungiyar ba.”
Babban Alkalin Jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ta gabatar da jawabi a wajen rantsuwar kama aiki na sabbin shugabanin, inda ta hore su da su aiki yadda doka ta tsara masu, ta kuma bukaci da su ci gaba da taimakawa wa sashen shari’a a kowane lokaci.