Rarara Bai Kawo Kudin Aurena Ba - Aisha Humaira
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rarara Bai Kawo Kudin Aurena Ba – Aisha Humaira

byRabilu Sanusi Bena and Sulaiman
11 months ago
aisha humaira

Jaruma a masana’antar Kannywood kuma makusanciya ga mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara Aisha Humaira ta karyata maganar da ake yi cewar mawakin ya kai kudin aurenta(Sadaki) a wata tafiya da su ka yi zuwa birnin Maiduguri domin kai kayan tallafi ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a watan Satumba.

Da ta ke amsa tambaya akan sahihancin maganar da ake yi cewar akwai alaka mai karfi a tsakaninta da mawaki Dauda Kahutu Rarara wanda har ta kai ga batun aure,wanda shi Rarara yanzu haka aka ce ya dauki kudin auren Aisha ya kai wa magabatan jarumar,Aisha ta ce ko kusa wannan magana babu kamshin gaskiya a ciki.

  • Gwamnatin Kano Za Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Hausa – Mataimakin Gwamnan Kano
  • MOFA: Kasar Sin Na Son Sanya Sabon Kuzari A Ci Gaban Tattalin Arzikin Yankin Asiya Da Tekun Fasifik Da Ma Duniya

Kamar yadda na fadi a baya da ni da Dauda akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninmu hasali ma idan ka ganmu tare zaka iya cewa mu tagwaye ne saboda yadda jininmu ya hadu da shi,amma maganar aure a yanzu dai babu ita, domin kuwa maganar da ake cewar ya kai kudin aurena gidanmu ba gaskiya bane,kawai dai mutane na fadin hakan ne saboda jin dadin bakinsu inji Humaira.

A kwanakin baya dai mutane sun yi ta maganganu dangane da yiwuwar auren Aisha Humaira da Dauda Kahutu Rarara inda har aka samu wasu mutane su na hada hotunan mawakan biyu, wata waka da Dauda ya rera mai taken AISHA ya kara ruruta wutar zato a zukatan mutane kafin ya fito ya bayyana cewar wannan wakar da ya yi ba don komai ya yi ta ba illa shirin fim kuma ita Aisha Humaira ta bukaci ya rera mata wakar wadda aka yi amfani da ita a cikin wani shirin fim da ta dauki nauyi mai suna A Cikin Biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

October 4, 2025
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

September 28, 2025
Next Post
PDP

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: PDP Ta Lashe Dukkanin Kujerun Shugabanni A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version