Connect with us

KASASHEN WAJE

Rasha Da China Sun Gargadi Amurka Dangane Da Takunkuin Da Ta Dora Wa Sojojin China

Published

on

Gwamnatocin Rasha da China sun gargadi gwamnatin Trump dangane da takunkumin da ta dora wa rundunar sojin China, saboda sayen makamai daga Rasha.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da gwamnatin Rasha ta fitar a shekaran jiya, ta bayyana takunkumin na Amurka a kan China da cewa mataki ne mai matukar hadari, kuma tana kiran Amurka da ta sake yin nazari kan batun.

A nata bangaren gwamnatin China ta yi Allah wadai da kakkausar murya da wannan mataki na Amurka, inda ta ce tana kiran Amurka da ta gaggauta janye wannan magana, idan kuma ba haka ita ce ke da alhakin duk abin da ya biyo baya.

Amurka ta dauki matakin kakaba takunkumi kan kasar China ne biyo bayan sayen wasu makamai masu linzami da kuma jiragen yaki da China ta yi daga kasar Rasha ne, lamarin da Rasha da China suke kallonsa a matsayin wani yunkuri da Amurka take yi na karya karfinsu ko ta wane hali.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: