Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta zauna da Ukraine domin tsara yarjejeniyar zaman lafiya, idan an cimma wasu sharuɗa masu muhimmanci.
Putin ya faɗi haka ne bayan wata doguwar tattaunawa ta waya da ya yi da Shugaban Amurka, Donald Trump, wacce ta ɗauki kusan sa’o’i biyu.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara
- Akwai Kure A Maganar Gwamna Kan Kulawa Da Masu Rauni – Ƙungiyar Dattawan Zamfara
Gidan talabijin na Rasha ya ruwaito cewa Rasha na duba yiwuwar tsagaita wuta na ɗan lokaci, matuƙar an samu ci gaba a yarjejeniyar.
Tattaunawar na zuwa ne bayan Rasha ta ƙara kai munanan hare-hare kan Ukraine ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a ƙarshen mako, duk da cewa ƙasashen biyu sun haɗu a wani zama na sulhu a birnin Istanbul a ranar Juma’ar da ta gabata.
Yanzu haka, harin da ake kai wa Ukraine na ƙara haifar da asarar rayuka da ɓarnar ga fararen hula, yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da kira da a kawo ƙarshen rikicin.
Masu sharhi na ganin cewa ko da Rasha na nuna amincewar sulhu, dole ne a fuskanci ƙalubale da dama kafin a kai ga cikakkiyar yarjejeniya, musamman dangane da yankunan da Rasha ta mamaye.