Ma’aikatar tattalin arziki ta Kasar Rasha ta gargadi gwamnatin Amurka kan barazanar da shugaban kasar yayi na ficewa daga kungiyar kasuwanci ta duniya.
Kamfanin dillancin labaran Sportnic ya nakalto ma’aikatar tattalin arzikin kasar ta Rasha tana fadar haka a ranar Jumma’a, ta kuma kara da cewa idan gwamnatin Amurka da kuskura ta fice daga kungiyar kasuwanci ta Duniya WTO to kamfanonin Amurka kansu za su yi asara, sannan za ta rikita harkokin kasuwanci a duniya don kamfanonin Amurka kansu suna bukatar kwanciyar hankali a duniya don samun masu sayan kayakin da take da siu.
A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kungiyar kasuwanci ta duniya da canza wasu dokokinta, idan ba haka ba ya yi barazanar ficewar Amurka daga kungiyar.