A yayin da ake bukin tunawa da ranar da nakasassu ta duniya a ranar Talata, wata kungiya da ba na gwamnati ba, wato CCD a takaice, wacce take kare muradun nakasassu a Nijeriya, ta bayyana cewa rashawa ke ta’azzara talauci a Nijeriya.
David Anyaele, Babban Daraktan CCD din shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin da yake gabatar da jawabi domin tunawa da ranar nakasassu na 2019 da ya gudanar a garin Legas.
Anyaele ya yi kira ga mutanen da suke da nakasa da su goyi bayan shirin gwamnatin tarayya na yakar rashawa a Nijeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa a duk ranar 3 ga watan Disamba, an ware ta ne domin mutane masu nakasa a duniya.
Anyaele ya ce yaki da rashawa a Nijeriya zai taimaka wajen rage talaucin da ‘yan kasar ke fama da shi. Kuma a cewarsa talauci yana daya daga cikin ginshikin da ke kawo nakasa.