Daga Abubakar Abba
Babbar Kotu ta Ƙasa da ke Ibadan cikin Jihar Ondo, ta yanke wa Tsohon Darakatan Cibiyar Binciken Aikin Noma da Horaras wa, Farfesa Benjamen Ogunmodede, hukuncin shekaru 40 a gidan Yari. Kotun ta yanke wa Farfesan Benjamen hukuncin ba tare da bashi zaɓin biyan tara ba.
An gurfanar Farfesan ne, a bisa zargin almubazarancin kuɗaɗen da aka ware don biyan albashin ma’aikata da kuma aiwatar da ayyuka a makarantar.
Su kuma Akawu biyu dake aiki a sashen kuɗi na cibiyar, Zacheus Tejumolada Adenekan Clement, su ma an yanke musu hukuncin shekaru 40 a gidan yari.
Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun, Mai Shari’a Ayo Emmanuel, ya yanke musu shekaru hur-huɗu akan kowanne laifi ɗaya, sakamakon amsa laifinsu.
Alƙalin ya ce, Ogunmodede da sauran ana tuhumarsu ne akan karkatar da Naira Miliyan ɗari 177 daga cikin Naira Miliyan 600 da gwamnatin tarayya ta tura wa cibiyar. Naira Miliyan 177 ɗin an ce an kashe su ne ba bisa ƙa’ida ba.
A bayanansu na kariya, waɗanda aka yanke wa hukuncin sun ce, sun kasha kuɗaɗen ne wajen bai wa ‘yan majalisar wakilai na Goro da kuma wasu ma’aikata a Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, waɗanda suka taimaka wajen ganin an fitar da kuɗin.
Sai dai, Mai Shari’a Emmanuel ya yanke hukuncin cewar, tsohon Darakatan da sauran sun amsa laifukan da ake tuhumarsu.
Lauya mai kare waɗanda ake ƙara, Tunde Olupona, ya ce, za su sake yin nazari akan hukuncin don sanin matakin da za su ɗauka nan gaba.
Shi kuwa Lauyan hukumar EFCC, Nkereuwem Anana, ya yi nuni da cewa, hukuncin wani abu ne da ke nuna ana cin nasara a yaƙin da gwamnatin tarayya take yi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan.