Connect with us

LABARAI

Rashawar Biliyan 17: Gbajabiamila Ya Mayar Wa Da Okonjo-Iweala Martani

Published

on

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya ce, shi ba shi da masaniyan cewa, ‘yan Majalisar sun karbi wani cin hanci, kamar yadda tsohuwar Ministan Kudi ta yi zargi a cikin littafin ta.

Okonja-Iweala, Cikin littafin na ta, mai suna, ‘Fighting Corruption is Dangerous: The Story Behind the Headlines,’ ta bayyana irin harkallan da aka rika yi kafin Majalisa ta sanya hannu a kan kasafin kudi a zamanin gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan.

Ta bayar da misalin shekarar 2015, inda Shugabannin Majalisar suka tilasta wa sashen gwamnati mika masu Naira bilyan 17 kafin su amince su sanya hannu a kan kasafin kudin.

A cewar Okonja-Iweala, wannan bilyan 17 din, baya ga kasafin kudin Majalisar ne na Naira bilyan 150 a duk shekara.

Gbajabiamila, wanda a wancan lokacin shi ne Shugaban marasa rinjaye na Majalisar, ya amince da cewa, ‘yan Majalisar sun sha fafatawa da Okonja-Iweala da mataimakan ta a kan kasafin kudin saboda sun cusa wasu ayyuka na su a cikin kasafin kudin ba tare da amincewar wasu ‘yan Majalisar ba.

Ya bayyana cewa, baya ga na ta ayyukan, mataimakan nata ma da ke hankoron tsayawa takarar wasu kujeru a Majalisar duk sun dankara wa kasafin kudin wasu ayyuka na su na kashin kansu.

Dan Majalisar ya ce, wannan shi ne ainihin dalilin takun sakan a tsakanin Ministar da ‘yan Majalisar.

A cewar shi, dalilin hakan ne, ya sanya ‘yan Majalisun suka bukaci sanya ayyukan na su mazabun a cikin kasafin kudin, a matsayin su na zababbun Wakilai.

Shugaban masu rinjayen ya ce, kuskure ne babba, Ministar ta kira hakan da cin hanci.

Shi ma Mai magana da yawun Majalisar Dattawan ta wancan zamanin, Sanata Eyinnaya Abaribe, cewa ya yi kudin da ake magana a kansu, Naira bilyan 17, za su iya zama kari ne da Majalisar ta yi kan kasafin kudinta, wanda bai yiwuwa a kira hakan da cin hanci.

Ya ce, “Ba na tsammanin tsohuwar Ministan kudin za ta kira hakan da cin hanci, ina ganin dai ‘yan Jaridu ne kawai suka dauki hakan a matsayin ta na nufin cin hanci ne.

A na shi martanin, wani wakili na Majalisar Wakilan, Abdulmumini Jibrin, ya ce ba shi da masaniya na zargin cin hancin Naira bilyan 17 din.

Ya ce, “A matsayi na na shugaban kwamitin Majalisar kan kudade na wancan lokacin da ake magana, ban taba halartar wani zama da aka tattauna hakan ba. ban kuma san komai kan wata Naira bilyan 17 ba, ban kuma amfanu da su ba, in ma har da gaske ne.

“Ba daidai ne tsohuwar Ministan ta yi irin wannan zargin ba, ba tare da ayyana komai ba. ai sai ta ambaci ko su waye suka tattauna da su a wajen zaman da ta ce anyi, inda aka karbi kudin.”

 
Advertisement

labarai