Connect with us

WASANNI

Rashford Na Hararar Matsayin Lukaku A United

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Marcus Rashford ya bayyana cewa zai nemi wajensa a kungiyar ta karfi da yaji a wajen dan wasan gaban kungiyar Lukaku, bayan dan wasan ya haskaka a a wasanni biyun da yabugawa kasar Ingila.

Tun bayan fara kakar firimiya ta bana dai sau daya aka fara buga wasa da dan wasan a kungiyar yayin da ragowar wasanni sai dai ya shigo daga baya kuma nan gaba bazai buga wasanni uku ba na kungiyar bayan jan katin da aka bashi a wasan da kungiyar tabuga da Burnley a satin daya gabata.

Sai a wannan satin dan wasan ya nuna kansa bayan da ya zurawa kasarsa ta Ingila kwallayenta guda biyu data zura a wasannin kasashen da suka fafata da kasashen Sipaniya da kuma kasar Switzerland inda kowanne wasa ya zura kwallo  daya.

Wasannin da dan wasan yabuga ya nuna cewa dan wasan yana bukatar ya dinga buga wasa a matsayin dan wasan gaba sai dai kociyan kungiyar yafi amincewa daya dinga amfani da Lukaku wanda kungiyar ta siya da tsada.

Hakan yasa Rashford baya jin dadi sosai kuma baya samun buga wasanni akai akai kuma ana bashi shawarar cewa idan har yana son ya zama babban dan kwallo dole sai yaz ama dan wasan gaba kuma yana zura kwallaye.

Mourinho ya mayar da dan wasan gefe wanda hakan ya sa kuma suke fafatawa da dan wasa Aledis Sanches wanda shima yake bin gefen daman a kungiyar sannan kuma ga Anhtony Martial wanda shima gefen yake bugawa.

A ranar Asabar dai Manchester United zata kai ziyara gidan Watford domin buga wasa na biyar na gasar firimiya sai dai Watford din duk tasamu nasara a wasanninta data buga na baya tun farkon fara firimiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: