Rashin Abin Yi A Tsakanin Matasa Da Illolinsa

Matasa

Daga Rabiat Sidi,

Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira, Tsokacin yau zai yi duba ne game da yadda wasu matasan ke zaune kara zube ba tare da sana’a ba, ya yin da wasu kuma ke samun sana’ar amma sai su raina su ki yi saboda wasu dalilai nasu marasa kan gado, wanda rashin yin sana’ar ita ke haifar da tabarbarewar tarbiyya, da samun yawaitar bata garin mutane walau matasan, walau kuma kananan yara.

Rashin abin yi ga matasa na jawo matsaloli da dama, wannan shafi na Taskira ya ji ta bakin wasu matasa inda suka fayyace dalilin da ke janyo rashin aikin yi ga Matasa, tare da hanyar da za a magance matsalar, matasan sun ba wa sauran matasa shawarwari har ma da gwamnati ta yadda za a shaho kan wannan matsalar ga dai yadda bayanan na su yake kamar haka:

Sunana Aisha Idris Abdullahi (ALEESHA):
Abu na farko da yake kawo rashin abin yi ga matasa mu girman kai da sanya buri a cikin ransu, girman kai na taka muhimmiyar rawa wajen hana matasa aiki, kana ganin kayi karatu ba za kai kowane aiki ba sai aikin ofis ka fi karfin aiki ka za ni sai ka za, sun sanyi burin duniya aciki ransu. Hanyar da za abi wajen magance matsalar rashin aikin yi shi ne; su kansu matasan su tsabtace idan ka yi karatu ka nemi aiki baka samu ba to ka je ka fara wata sana’ar idan kana da rabon samun aikin gwamnati sai kaga ka dace a gaba, ba wai ka zauna kawai kana jiran dole sai kai sai ka samu aikin gwamnati ba, sanan za kai neman kudi. Shawara gareku matasa da suke samun aikin yi suke rainawa duk wanda kaga ya zama wani baka san gwagwarmayar rayuwar da ya sha ba, ku tashi ku nemi na kanku ba maraya sai rago, wanda ya raina kadan kuma barawo ne, dan haka matasa A motsa, kirana da gwamnati anan shi ne duk wanda ya yi karatu kuma har karatun ya kai matakin da za a dauke shi aiki to a dauke shi, wanda ba su yi karatu ba ma a basu jari su yi sana’a.

Sunana Zahra’u Abubakar (Dr.Zara) Jihar Kano:
Rashin adalci ga ‘yan kasa, tabbatar da wutar lantarki wannan shi ne, matasa ina ba su shawara da su kama sana’ar su hannu biyu-biyu su jajirci babu abinda ya fi dadi irin mutum ya tashi ya nemi na kansa, kuma a daina raina kadan hausawa na cewa abokin barawo shi ma baraho ne, gaskiya ya kamata a koda yaushe mu rinka kallon na kasa damu ba wai na sama da mu ba, mu daina raina abinda muke samu wataran sai labari da ‘rarrafe yaro ya ke tashi’, Allah ya sawa sana’oin mu albarka, ya kamata gwamnati ta ji tsoran Allah ta rinka sauke nauyin al’umma da ya rataya a wuyanta, matasa na zaune birjik babu abin yi wasu na da kwalayansu a hannu babu aikin yi sannan in an zo da a kama sana’a nan ma matsaloli kala-kala masu keke napep an takura masu, masu rumfuna a kasuwa ma haka Allah ya kawo mana dauki Alfarmar nabiyyu rahamati.

Sunana Bilkisu Musa Galadanchi (Billy Galadanchi):
Lalaci ne wannan ya ke kawo shi, ga sana’o’in hannu nan burjik, amma matasan mu na yanzu sun dage akan lallai sai aikin gwamnati. Ta hanyar dogaro da kai, da ace matasan mu za su yi wa kansu fada, su tashi tsaye kikan su nemi na kansu, Sana’a in dai ta alkhairi su runguma da ko tabbas an samu waraka akan wanan abin. Shawarar da zan baiwa masu samun abin yi suna rainawa shi ne su godewa Allah, su tashi tsaye duk sana’ar data fado musu in dai ba muguwar sana’a ba ce ba, su rungumeta hannu bibbiyu. Dayawa matasa irin su suna neman wannan damar ba su samu ba. Kiran da zan yi ga gwamnati shi ne ta duba lamarin nan ta tallafawa matasa, ba lallai da aikin gwamnati ba amma da sana’a ma zai wadatar, idan kuma aikin ya samu sai a ba su.

Abdul-Azeez Shehu (Yareema) 08030704570 daga Kano:
Abin da ke jawo matsalar rashin abun yi ga matasa su ne; Girman kai tare da raina sana’a domin duk matashin da bai da wata sana’a shi ya so gaskiya, kuma babban matsalar tunkaho da matasa ke yi da iyayensa, tare da sa rai a dukiyar da iyayensu suke da su, to hakan na sanya matasa kasala a cikin zuciyoyinsu. Hanyar da za a magance matsalar sune; matasa su tashi ka’in da na’in su nemi halaliyarsu su cire girman kai. Ina kira ga masu raina sana’a da su daina, in sun samu komai kankantarsa su yi hakuri, su yi da sannu wata rana sana’ar na su zai habaka har su dauki wasu a karkashinsu. Ina kira ga gwamnati da su ji tsoron Allah, su kula da matasa wajen samo musu aiyukan yi, domin rashin hakan ne ke haifar da tarin matsalolin a duniyarmu a Yau.

Sunana Aisha Hussaini (Princess Ayshatou):
Babban abin da yake jawo matsalar rashin abin yi ga matasa bai wuce mutuwar zuciya ba da lalaci ba, sun taka muhimmiyar rawa gurin tallafawa matasan wannan zamani a gurbacewa. Sun fi son komai su samu daga sama, ba tare da wahala ba. Ta ya ka kashe zuciyarka za ka tsumayi zuwan alheri ga rayuwarka? Sannan abin takaici idan ka ga abin da zamani ke ya yi sannan kace dole sai ka mallake shi, alhalin kowa ya san tsaki dai-dai da ruwa ake saka shi, sannan ko a yatsun hannunka ka duba wani ya fi wani tsayi me ya sa ba za ka shiga wata hanya domin samun ba. Yanzu mu dauki misalin Bandits din da suke addabarmu lalaci da rashin watadar zuci shi ne ya assasa musu bin muguwar hanya. Ni tambayar ma da zan yi wa masu wannan dabi’ar sun manta cewa ‘Babu maraya sai rago?’ Kuma Allah (S.W.A) ya ce “Tashi na taimake ka?”. Hanya daya ce dole sai an cire raggwanci da lalaci sannan ake ganin dai-dai. Kar mutum ya tsaya jiran aikin gwamnati ‘if he’s graduate there’re so many business’ da za ka iya ‘inbesting with the little you habe’. Idan na ce kasuwanci ya hada komai amma fa wanda bai kaucewa hanya ba, Masu iya magana na cewa “Raina kadan ka ga gayya” Wani lokaci ribar da kake rainawa ‘by the time’ idan kana adanarta za ka ga ta zame maka taskar arzikinka. Sana’ar da ka raina wani yana can yana neman irinta ido rufe. Idan dambu ya yi yawa bai jin mai. Nauyin da ya ke rataye akan gwamnati ya yi mata yawan da ba za ta iya biyawa kowa bukatarsa ba, amma duk da haka ina kira da ta waiwayo domin tana tafiya a makance ne, idan ba ta tanadar wa ‘yan kasarta abin yi ba ‘by the time’ su ‘yan kasar za su nema ta hanya mai kyau ko akasin haka. Don haka dabara ta ragewa mai shiga rijiya da baya. ‘Yan ta’addar da suke addabar arewacin Nageriya ya zama izina a gare ta.

Sunana Shua’ibu Abdullahi:
Rashin maida hankali ga iyaye wajan kula da tarbiyyar ‘ya’ya da jajircewa don sanin me suke su sama musu aikin yi, Ina kira ga iyaye don Allah su rinka kulawa da tarbiyyar ‘ya’yan su wajan sanin me suke yi da kuma sama musu aikin yi ba wai gwamnati kadai ba. Shawarata ga matasa masu abin yi komai kake yi ka yi hakuri koyaya kake kafi wani in dai ka jajir ce Allah zai taimake ka watarana sai ka kai inda baka za ta ba, Shawarata ga matasa indan ka sami abin yi karka raina, kar kace sai ka gina gida ko mota komai kankantar abu ka rike shi da kyau in dai baka raina ba, da sannu za ka cimma burikanka kai dai kawai ka rike gaskiya a kowane hali.

Yusif Abdullahi Musa R/Lemo:
Gwamnati ce ta jaho saboda bata ta su take ba, gewamnatice ya kamata ta fito da wata hanyar tallafawa matasa ba dole sai ta daukesu aiki ba, akwai hanyoyi da za ta kula da su, ta addancu zai ragu, matasa su daina rainasa a duk kankantarta, Shawarata ita ce gwamnati ta tsaya ta kula da al’umarta musanman ma matasa saboda sune ginshikin Al’umma. Sannan gwamnati idan ta kula da matasa ta addanci zai ragu, saboda gwamnatin sai ta bashi kunawa babu wane wanda zai ce masa gama kamai dan ya kashiwa ne abasa kudiya karma saboda gwamnatin ta bashi kula, su kuma samari da ‘yan mata sune kashi bayan al’umma ga kamar zuciya suke Allah ya sa a dace.

Exit mobile version