Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rashin abinci mai gina jiki babbar barazana ce ga lafiyar ɗan Adam, wacce ke da nasaba da matsin tattalin arziƙi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ƙaddamar da Shirin Abinci Mai Gina Jiki na Ƙananan Hukumomin Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, a Gusau.
- Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya
- Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa shirin na nufin bunƙasa abinci mai gina jiki a dukkanin ƙananan hukumomi na jihar, tare da haɗa ɓangarori da dama irin su lafiya, noma, ilimi, tsaftar muhalli da kuma kula da jama’a (WASH).
Yayin jawabinsa, Gwamna Lawal ya ce kafa majalisar kula da abinci mai gina jiki a Zamfara domin kawo sauyi wajen tabbatar da lafiyar al’umma da ci gaban yara.
“Ba za mu iya gina jihar da za ta kasance mai kwanciyar hankali da wadata ba idan jama’arta ba sa samun abinci mai gina jiki. Zuba jari a farkon kwanaki 1,000 na rayuwar yara shi ne mafi kyawun jarin da za mu iya bayarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki.
Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar da shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar.
“Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa wannan shiri ya ɗore tare da haɗin kan gwamnati da abokan hulɗa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Hon. Abdulmalik Gajam, ya ce gwamnatin Gwamna Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkar lafiya da abinci mai gina jiki ga yara ƙanana.
Haka kuma, Misis Uju Rochas Anwukah, babbar mataimakiyar shugaban ƙasa kan harkokin kiwon lafiya, ta yaba da yadda gwamnatin Zamfara ke gudanar da ayyukan lafiya, inda ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen gina Nijeriya mai wadataccen abinci mai gina jiki.














