Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Rashin Adalci Ne Muraran A Ce Ina Kira A Yi Juyin Mulki – Bishop Kukah

by Khalid Idris Doya
December 31, 2020
in LABARAI
3 min read
Bishop Kukah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Babban Shehin Majami’ar Roman ta Katolika ta jihar Sokoto, Bishop Matthew Hassan Kukah, ya fito balo-balo ya karyata tare da musanta rahotonnin da aka ce ya furta a cikin jawabinsa na ranar Kirsimeti wanda aka ambato shi na cewa a yi juyin mulki a kasar nan.

Ya na mai cewa rashin adalci ne gareshi a ce shi din ya na kira da a yi juyin mulki. Illa dai ya ce har yanzu ya na nan daram kam batun da ya yi kan tabarbarewar tsaron kasa, yana mai cewa ba zai cigaba da zura ido yana kallon rayukan mutane na zuba a ce ba zai yi magana ba.

samndaads

A lokacin da ke ganawa da wasu kebantattun ‘yan jarida a sakatariyar St Bakhita da ke Sokoto a daren ranar Litinin, Bishop Kukah ya kuma bayyana cewar dukkanin wani dan jarida ko gidan jarida da suka bada labarin cewa ya yi kira da a yi juyin mulki, to ba su masa adalci ba sam-sam.

LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewa bayan fitar bayanan na Mista Kukah, hukumomi ciki har da Ministan yada labarai Lai Mohammed sun soki shehin malamin tare da cewa yana yunkurin yi wa gwamnati mai ci zagon kasa, sannan, kungiyar Buhari Media Organisation ita ma ta caccaki Kukah tare da kungiyoyi daban-daban ciki har da masu kiran a kama babban shehin malamin bisa abun da suka ce yunkurin zubda wa gwamnati kima da mutunci tare da kokarin jawo rigima a kasa.

Sai dai a taron manema labaran, Bishop Kukah ya nuna matukar damuwarsa a bisa yadda wasu ‘yan Nijeriya suka gaza gane hakikanin sakon da yake son fitarwa, wanda hakan ya kuma a cewarsa ya yi bayaninsa ne domin tsananin kishinsa ga kasar nan.

Bishop Hassan Kukah na cewa: “Na yi matukar mamaki da bakin cikin masu gaggawar sukana da hantara ta, su na kallo a kan idonsu a kowace rana ake samun asarar rayukan jama’a a kasar nan. Yawaitar asarar rayuka cikin shekara goma da suka gabata, tun kafin zuwan gwamnati mai ci, ta yi ta ikirarin cewa za ta shawo kan matsalar tsaro.

“Dukkanin wani mai son cigaban kasa dole ya tashi ya yi sukarsa kan matakin tabarbarewar tsaro. Abun kaito da takaici ne a ce a kullum Nijeriya baya take komawa, kima da mutuncin kasar na kara zubewa. Don me ba za mu yi magaba ba. Ni irin mutanen nan ne da ban cika damuwa ko jin haushi da abun da wasu ke cewa a kaina ba.

“Abun da fa na ce shi ne, na bayyana ra’ayina bisa dogaro da tulin hujjoji da shaidun abun da suke faruwa a Nijeriya, idan ka duba tarihi ka waiwaiyi baya, akwai tulin hujjoji da za su tabbatar da jawabin da na yi, sanna, duk wani da yake tunanin ban yi daidai ba, zai iya fitowa da na shi ra’ayin na daban bisa hujjoji da za su shafe nawa.

“Amma, rashin adalci ne wani dan jarida ko gidan jarida su bada rahoton cewa ni ina kira da a yi juyin mulki yayin da nake bayyana ra’ayina na kashin kai kan lamarin da Nijeriya ke ciki,” Inji shi.

Dangane da martaninsa ga masu cewa ya jingine rawanin shehunta ya tsunduma harkar siyasa, Bishop din ya ce zai iya shiga siyasa ne kawai a lokacin marigayi Aminu Kano.

“Ba na da shiri ban kuma taba ko mafarkin shiga siyasa bisa kowani irin dalili ba. Wadanda suka bage da kokarin jingina sakona da siyasa kawai wasa suke yi da almara.

“To, don meye wani ko wasu za su yi tunanin jingina sakon Bishop Kukah da siyasa? Wadanda ma suke wannan batun ba su ma san tarihin siyasar farko da kuma irin rawar da ‘yan siyasan baya suka taka ba.

“A zahirin gaskiya dukkaninmu muna cikin siyasa, ni ba mambar wata jam’iyyar siyasa ba ne ba kuma zan taba kasancewa hakan ba. Idan na je rumfunar zabe na kada kuri’ata, ‘yanci na ne.

“Koma dai yaya ne, abun da na fada ko ya faranta ma wani ko wasu rai, ko ya bakanta ma wani ko wasu rai, ni dai na fadi ra’ayina ne, ba kuma zan hana wani ma ko wasu fitowa su bayyana nasu ra’ayin ba. Idan ka ko kuna tunanin ra’ayina ba daidai bane, fito ka kadi naka mana.

“Ba na da wata matsala da Musulmai, ko Kiristoci ko wata addini, amma ko kadan bana son wani ya yi amfani da addini wajen takara rawar siyasarsa, wannan ba daidai bane ko kadan,” a cewar Babban shugaban Kiristocin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa Zai Bunkata Harajin Gwamnati – Hadiza Usman

Next Post

Tarbe: An Shammaci Gwamnan Nasarawa A Titin Akwanga

RelatedPosts

Jami’an NIS Na Samun Horo A Kan Amfani Da Dokokin Shige Da Ficen ƙasa

Jami’an NIS Na Samun Horo A Kan Amfani Da Dokokin Shige Da Ficen ƙasa

by Khalid Idris Doya
9 hours ago
0

Shirin yaƙi da safarar bil’adama da fasa-ƙwaurin ‘yan gudun hijira...

‘Yan Nijeriya Mutum Miliyan 15 Na Shan Kwayoyi, Inji Buba Marwa

‘Yan Nijeriya Mutum Miliyan 15 Na Shan Kwayoyi, Inji Buba Marwa

by Khalid Idris Doya
12 hours ago
0

Shugaban Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun...

Katin Zama Dan Kasa

Nijeriya Ta Wajabta Wa Jami’an Diflomasiyya Mallakar NIN

by Khalid Idris Doya
18 hours ago
0

A jiya Lahadi Gwamnatin Tarayya ta shaida cewar, ya zama...

Next Post
Gwamnan Nasarawa

Tarbe: An Shammaci Gwamnan Nasarawa A Titin Akwanga

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version