Connect with us

TATTAUNAWA

Rashin Adalci Ne Zargin Malaman Tsangaya Da Rashin Bada Hadin Kai – Sheikh Hassan Musa

Published

on

SHEIKH HASSAN MUSA shi ne shugaban kwamitin malaman tsangaya da ke zama da gGwamnatin Jihar Neja kan yadda za a inganta makarantun allo. A hirarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ta ke wa tafiyar kafar ungulu, ya na mai cewa, bai dace a zargi malaman tsangaya da kin bayar da hadin kai ba. Ga dai hirar ta kasance:

 

Sheikh, a na zargin ku da rashin bai wa gwamnatin jiha hadin kai kan kudirinta na kwashe almajirai daga jihar da nufin inganta tsarin makarantun tsaya a jihar.

Maganar gaskiya duk wanda yai wannan furucin bai mana adalci ba, domin rahotanni da muka samu daga bangaren gwamna mun yi na’am da shi, saboda tashi tsayen da muka yi na wayar da kan malaman makarantun allo mahaddata Al-kur’ani mai tsalki. Domin mafi yawansu suna cikin kungiyar mahaddata, kuma a wannan kungiyar muna da shugabanni na kasa, mun zauna da su malaman kuma suka fahimci manufar gwamnati akan wannan kudurin. Sarakunan gargajiyar jihar nan da masu unguwanni, Allah ya saka masu da alheri; sun turo kusan dukkan makarantun tsangayun mu dan hada bayanan almajiran da ke karkashin kowani malami, mun zauna da su kuma sun amince akan za a mayar da almajiran nan garuruwansu na asali. Sannan akwai alheran da gwamnatin tace ta shirya za ta yi wannan bangaren, na gina makarantun tsangaya a dukkan masarautu takwas na jihar nan. Saboda idan mutum ya fito yanzu ya ce malaman ba su bada hadin kai ba, sai mu ce ba gaskiya ba ne, domin dukkan mu mun yi na’am da wannan tsarin na gwamnati ta yadda kowani yaron zai tsaya a gaban iyayensa yai karatun addini da na zamani.

 

Idan mu ka duba wasu jihohin, a na bin almajirai a na kamawa. Shin ya abin ya ke a jihar nan?

Gaskiya ne, abinda na fahimta kowace jihar tana da irin na ta matsalolin, na abinda ya shafi almajirai. Bisa shawarwarin da na bayar a wasu littattafan da na rubuta wanda yanzu haka wasu jahohin da shawarwarina ake anfani, abinda muka bayar da shawara ma tun farko ba maganar kama almajirai, ba maganar bin su da gudu, idan ka ce a bi su da gudu kar manta bai wuce a ce ayi anfani da jami’an tsaro wanda wasun su ba musulmai ba ne, kuma kai gwamna ba ka da iko da jami’an tsaron, sai ya zama na garin gyara an tsokane ido a tafiyar. Don haka mu ka ce ba kame za a yi ba, dan mu ba mu kira shi akan kame ba. Domin idan mun dawo akan dokar kasa, baka da ikon hana duk wani dan kasa watayawa a kasar nan muddin ba zai zama matsala ga tsaron kasar ba, haka Allah ma a cikin littafin sa mai tsalki, yace Allah ya shinfida kasa domin bayinsa, yana bada ita ga wanda ya ga dama, bako ya zo gari bai da komai, a kwana a tashi a wannan garin sai ka ga ya mallaki gidaje biyu, uku ba ma daya ba, karshen kwarai tana ga masu takawa. Amma tsarin da gwamnatin jiha ke bi kan maganar almajirai mun ya ba domin mu ne a ka bukaci mu tattara su ita kuma gwamnatin tai alkawalin kyautata rayuwarsu.

 

Amma akwai zargin wasu almajiran da ku ka fara bai wa gwamnatin sun tsere.

Wannan gaskiya ne, da farko bisa alkawali maigirma gwamna ya ce a sansanin da za a tara almajiran cin su da shan su, da samar masu walwala kafin daukar su zuwa wajen iyayen su duk ita za ta dauki nauyi. Amma abinda ya ba mu mamaki su jami’an gwamnati da ke ikirarin hana cinkoson jama’a sun kwashi yara wani dakin sun kai mutum 50 da wani abu, kuma haka bar su cikin tsunmukara ba wani tanadi mai inganci kuma ba tsaro a wajen, wanda mu ma mun yi korafi. Abinda ya ba mu mamaki a cikin dare sai jami’an kiwon lafiya suka zo wai dan gwajin Korona a sansanin, sun dauki sanfurin mutum tara, bayan sun dawo mu shugabannin ba a sanar da mu ba, wani jami’in kiwon lafiya yazo a wani daren ya tara almajiran yana fada masu cewar a cikin su akwai wanda ke da cutar Korona, hakan ya janyo almajiran fara bore a wannan daren dan an gaya masu cewar za a dauke wannan din. To, bayan wannan boren ne fa bayan dukkanmu mun bar wajen kwamitin bangaren gwamnati da na malaman tsangaya da muka halarci wajen cikin daren mafi rinjayen almajiran suka watse, wanda ita gwamnati mun ba ta wadannan almajiran ne bisa amana, kuma yanzu muna bukatar su ne bisa amana dan mayar da su gaban iyayen su. Wanda mu da ita muna kan neman almajiran ne. Almajiran da muke maganar fa akan su, ba wai mabarata ba. Muna magana ne akan wadanda suka zo neman ilimin Al-kur’ani wanda bakon safe da zai iya tafiya ko yaushe.

 

Malam, ganin yadda a ke ta kiki-kaka a kan almajiran kwargu, wato masu neman ilimin addini, wane hanya ya kamata a bi, don kawo karshensa?

Ko a satin da ya gabata mun ji wani fitaccen dan siyasa wanda ma ba dan arewa ba, amma yasan matsalolin arewar wato Sanata Rochas Okorocha yayi ta’aliki mai ma’ana wanda da shugabannin arewa zasu cire kyashi da hassada su bi wadannan shawarwarin ina da tabbaci ba wani uba a arewa da zai yarda ya sake barin dan shi zuwa wani garin da sunan neman ilimi. Maganganun Rochas abin a ya ba masa ne, kuma mu mun ya ba masa a kungiyance. Yana da kyau idan mutum yayi abin yabo koda ba musulmi ba ne ka ya ba masa, muna kira ga shugabannin arewa da su ji tsoron Allah kar su bari sai bayan ta kucce masu su dawo suna da na sani.

 

Sheikh Hassan, mu na godiya da lokacin da ka ba mu.

Ni ma, Ina godiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: