Rashin Adalcin Da Muka Gano Ana Tafkawa A Bankin Raya Kasa –Sanata Ndume
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Adalcin Da Muka Gano Ana Tafkawa A Bankin Raya Kasa –Sanata Ndume

byBashir Bello, Abuja
3 years ago
Tafkawa

Shugaban Kwamitin Rundunar Sojoji a Majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Ndume ya bayyana cewa akwai bukatar a bindiki Bankin Raya Kasa watau ‘Development Bank of Nigeria (DBN)’ da Gwamnatin Tarayya ta kafa domin taimaka wa kananan masana’antu da `yan Kasuwa sakamakon zargin irin rashin adaldin da ake tafkawa da gudanar da al’amura ta hanyar da ba ta dade ba.

Ndume wanda ya kasande mamba a dikin wani kwamitin wudin gadi na mutum bakwai da Sanata Muhammad Sani Musa 313 ke jagoranta a Majalisar Dattawan Tarayyar, ya yi nuni da cewa a wani binciken da suka yi alamu na nuni da cewa kwalliya ba ta biya kudn sabulu ba a bankin.

An Bude Bikin Anime Na Kasa Da Kasa Karo Na 18 A Hangzhou

Kasashen Turai Sun Fusata Da Matakin Amurka

Ya kara da cewa an gabatar da wani kudirin doka a majalisar domin a bindiki Bankin na DBN wanda Gwamnatin Tarayya ta kafa saboda tabbatar da an taimaka wa kananan `yan kasuwa da masana’antu domin su samu tallafi mai sauki ta yadda za su farfado ko su kafa kananan masana’antu wanda yake da mahimmadi ga masu karamin karfi domin idan aka farfado da wannan za a iya farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya de “amma abun takaici shi ne mun lura a dikin wani bincike cewa Bankin CBN a cikin shekarar 2021, ta rabar da kudi kusan kimanin rabin Tiriliyan, amma abun takaidi shi ne inda talaudi ya fi katutu kuma inda ake bukatar a farfado da kananan masana’antu ba su samu ko rabin abin da suka rabar ba.

“Na gano cewa Jihar Legas kadai a dikin kudi Naira Biliyan 483 sun samu kashi 47% amma sauran shiyyar Kudu maso yamma sun samu kashi 10 wanda gaba daya kudin ya kama Naira Tiriliyan 274 a yayin da daga dikin Jihohi shida na Kudu maso yamma, ita Jihar Legas kadai ke da kudi kimanin Naira Biliyan 227 amma sauran jihohin biyar ke da kashi 10.

“Haka Kudu maso Kudu sun samu kashi 17 da ya kama Naira Biliyan 81, amma gaba dayan Arewa da ke da Jahohi 19 sun samu kashi 11 wanda ya kama kimanin Naira Biliyan 53, domin a shiyyar Arewa maso gabas ta samu kashi 5 wato Naira Biliyan 24, sai shiyyar Arewa maso yamma ta samu kashi daya wato Naira Biliyan 4,820.

“Makasudin kafa wannan Bankin shi ne don ta taimaka wa kananan `yan Kasuwa da masana’antu wanda sune ke fannin Noma, kasuwandi, sufuri amma sai muka ga sun dauki kashi 42 na kudin sun ba masu harkar mai.

“Kudin da aka bayar ga shiyyoyin 6 bashi ne ake bayarwa mai sassaudi don farfado da tattalin Arzikin Kasa ta hanyar Bankin don ita Bankin da za ta bayar, ba tana bayarwa ba ne don riba sai don a taimaka.

“Misali a Jihar Kano da Sokoto an rufe masana’antu da yawa don ba Kudin da za a farfado da su, shi ne ya sa ake so a basu wannan kudin da zai zamanto ba za a kuntata musu ba, toh amma kwalliya ba ta biya kudn sabulu ba.

Acewarsa, akwai bukatar a yi bincike don sanin shin nawa ne Kudin, mai yasa aka rabar da kudin haka, meye za ayi don tabbatar cewa dalilin da ya sa aka kafa wannan Banki da kuma tabbatar da cewa Kudaden da ake rabar sun je ga hannun wadanda ya kamata, kuma `yan Nijeriya su gani a kasa ta hanyar tabbatar da cewa kananan masana’antu na tasowa ta hanyar taimakon wannan Banki tunda a bisa wannan dalilin ya sa aka kafa Bankin na DBN.

“Kuma akwai Bankin Kasuwanci (BOI), NIRSAL ta DBN da Gwamnatin Tarayya da suka sha fitar da wadansu hanyoyin da tsari don taimaka wa `yan Nijeriya talakawa amma har yanzu ba a gani a Kasa ba saboda matsalar wadanda aka saka su su yi aikin ya sa muke son mu yi bincike a Majalisar domin idan da akwai wadanda suka hana ruwa gudu, sai a san yadda za a yi a kawar da su domin a samu tsari mai kyau a kan abin da ake bukata.

“An hada kwamitin wucin-gadi na mutum bakwai, an saka ni member kuma Insha Allah za mu tabbatar da cewa an yi abun da ya dade don tabbatar da cewa `yan Nijeriya sun ga abin da aka yi tare da tabbatar cewa an yi maganin matsalar.

“A yanzu talaudi ya addabi `yan Nijeriya musamman Arewa. A kiyasi, Jihar Kebbi na fama da talauci kimanin kashi 86, Jihar Gombe 77, Jihar Bauchi  87, Jihar Taraba 78, Jihar Zamfara kashi 80, sannan kusan rabin Jihar Filato na fama da talauci, haka sama da rabin `yan Jihar Ebonyi su ma suna fama da talaudi, shi ya sa ni a matsayin wakili na kai wannan lamarin gaban Majalisar don a yi wa tubkar hanci, a yi maganin lamarin kuma `yan uwana `yan majalisar sun karbi abun hannu biyu-biyu, don haka suka bani goyon baya.” In ji Ndume.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Cuba

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Cuba

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version