… Za Su Tsayar Da Jihohi Cak!
Daga Sulaiman Bala Idris
Ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta tarayyar Nijeriya ‘NLC’ tare da haɗ in gwiwar ta ƙungiyar ‘yan ƙasuwa ta Nijeriya ‘TUC’ sun yi shelar cewa za su fara wata gagarumar zanga-zanga a jihohin da suka ƙi yin amfani da tallafin gwamnatin tarayya wurin biyan albashin ma’aikatansu.
’Yan ƙ wadagon sun buƙ aci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya dakata bayar da duk wani tallafi da yake ba gwamnonin har sai sun yi mishi gamsasshen bayanin yadda suka tafiyar da tallafin da aka basu a baya.
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Ƙwadago ta Ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba, wanda ya tattauna da Jaridar LEADERSHIP A Yau ta wayar tarho, ya bayyana cewa furucin da shugaban ƙ asa Muhammadu Buhari yayi, ya nuna ƙ arara cewa shugaban ya san darajar ma’aikata, kuma yana jin zafin abin da ake yi musu.
Ya ce: “Mun gano cewa waɗannan gwamnonin sun je ne wurin Shugaban Ƙasan domin su nemi ƙ arin kuɗ aɗ en tallafi. Wannan kuma ya isa zama ishara a fahimci cewa ba wai kawai batun sakar musu kuɗ aɗ e bane. Dole ana buƙ atar su yi bayanin yadda suke tafiyar da su.
“Kamar misali, gwamnatin jihar Jigawa ba ta samu wannan tallafi ba, amma kuma babu wani ma’aikaci da ke bin gwamnatin jihar bashi. Amma kalli jihar Bayelsa, duk da irin kuɗ aɗ en tallafin da ta amsa, basussukan ma’aikata ne jibge akan gwamnatin jihar.” Inji shi.
Ya ce, ma’aikata za ta shirya tsaf domin tabbatar da cewa sun tsayar da dukkan jihohin da ke binsu bashi cak!
Shi ma a nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Bala Kaigama ya ce ƙ ungiyoyin biyu; na NLC da TLC sun rubutawa shugaban Ƙ asa Buhari wata wasiƙ a inda suka buƙ aci da kada ya sake sakarwa gwamnonin da ke riƙ e da albashin ma’aikata kuɗ in tallafi. Sannan kuma ƙ ungiyoyin za su yi iya yinsu wurin ganin sun tursasa wa waɗ annan gwamnonin biyan albashin ma’aikata a jihohinsu.