Connect with us

LABARAI

Rashin Biyan Giratuti Ya Jefa Wadanda Suka Ajiye Aiki A Zamfara Tsaka Mai Wuya

Published

on

 

Ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwar su wajan cigaban alummar jihar Zamafara , harta kawo yanzu ,rashin biyan su hakokin su

ga tsafin Ma’aikatan na giratuti da sukai ritaya a jihar , ya sasu  cikin tsaka mai wuya ,sakamakon rashin biyan su akan lokacin da ya dace .

Shugaban kungiyar fensho na jihar Zamfara , Kwamaret Hassan Muhammad Gusau ne ya bayyana haka a lokacin da ke zantawa da ‘Yan Jaridu a ofishinsa da ke Gusau ,babban birnin jihar Zamfara .

Kwamaret Hasssan Gusau ya bayyana cewa , ‘ shekaru tara ke nan tsafin ma’aikata na fama da matsalar rashin biyan su fensho ,dan yanzu haka wasu tsafin ma’aikatan sunrigamu gidan gaskiya ,sai dai aba magadan su .

” Shugaban yayi kira ga gwamnatin jihar Zamfafa ,karkashin jagorancin gwamna Bello Matawallen Maradun ,gwamna mai tausan alumma kuma gashi shima tsohon Ma’aikacine , da ya taimaka ya shawo karshen wannan matsalar kamar yadda Allah ya bashin na sarar dakile “‘Yan ta’addan da suka addabi wannan jihar tamu .

” Kwamaret Hassan Gusau kuma ya jinjinawa shugaban hukumar Fenshio , Alhaji Abdulkadir Mai Kiyo Maradun da Manbobinsa wajan biyan tsafin Ma’aikata Fensho su akowane wata batare da matsalaba . kuma muna fatan zasuci gaba da yinkokarin wajan ganin giratutin mu ya samu a wannan lokaci nasu mai albarka .
Advertisement

labarai