Rashin Dacewar Goyon Bayan Masu Tayar Da Zaune Tsaye A Nijeriya

Zaune Tsaye

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Allah Sarki kamar dai yadda masu iya magana suke cewa kowar samu rana sai yayi shanya, wannan haka ne domin kuwa wasu ma ba shanyar ce kadai suke yi ba, har ma barin abubuwan da suka shanyar suka yi, har sai da suka kai ga kwana. Sai dai kuma idan aka yi la’akari da  yadda wasu da wasu ke yi ma shi al’amarin na  Shugabannin siyasar Kudanciun Nijeriya, bayan shekarun da suke dasu wadanda basu kadai bane harma da hankali da hangen nesa ne cikin su , Uwa Uba kuma ga ilmi wanda shi ne gishirin zaman duniya. Wannan al’amarin  na irin wadannan Shugabannin wadanda idan sun tashi yin wasu maganganun su da kuma wasu take- taken su basu kallon komai illa vangaranci da kuma nuna cewa ai nasu ne komai ayyukan ashshan da yake aikatawa ba a fa isa a hukunta shi ba. Lokacin ne za su ce kodai an tsane shi ko kuma ba ayi masu adalci, amma kuma ga wani abin dariya da yaro ya tsinci hakori, sun manta da cewar shi fa wanda suke nuna wa matukar so da kuma goyon baya, ba karamin mai aikata laifukan da suke da alaka da cin zarafiin al’umma bane.

Masu bibiyar yadda al’amuran yau da kullun suke tafiya musamman ma idan aka yi la’akari da siyasar Nijeriya, da yadda wasu suka zama ‘ya’yan Mowa wasu aka bar su  a dakin Bora. Nace bibiyar yadda al’amuran yau da kullun suke tafiya ta sanin halin da ake ciki ta kafafen yada labarai da suka kunshi Rediyo, Talabijin, Jarida, da kuma sauran kafofin sadarwa na zamani irin su Facebook, Whatsup, Twitter, da kuma Instagram, da dai sauran wasu kafafen. Idan an manta sai a tuna da Sunday Igboho da kuma Nnmadi Kanu jagororin tsarin samar wa yankunan nasu kasashe masu cin gashin kansu. An dai san irin dauki ba dadin da aka yi   tayi dasu inda suka yi ta cin zarafin dan Adam ta hanyoyi daban- daban amma shugabannin su babu wanda ya samu rana daya ya kira taron manema labarai inda ya dace ya ce su abubuwan da   gwanin nasu yake yi bai kamata. An samu salwantar rayuka,  dukiyoyi da kuma kaddarori na al’ummar musamman  ma na Arewacin Nijeriya amma ba wani wanda yau yace kai abubuwan da suka yi ko kadan basu dace ba.

Duk tavargazar da shi Nnamdi Kanu ya yi ta aikatawa bai aikata wani laifi ba, wanda har belin sa aka ma bayar amma ya tsere, ya kasance tsakanin kasashen Ingila da Isra’ilainda yake kai gwauro ya kai mari,, daga can ma bai tsaya wajen ruruta wuta ba, umarni ya rika badawa na ranar da za a aikata ayyukan ashsha, lokaci da kuma wuraren da za a kai ma hari amma, shi ba  a kalle shi da sunan wanda ya aikata laifi ba, in banda zuga shi ma da ake kara yi, babu wanda yace ma shi uffan. Shi dama al’amarin duniya ai haka ne yake Kwana 99 na Varawo yayin da kwana  daya tak shi ne  na mai kaya, inda Allah ya sa aka kamo shi a kasar Kamaru. amma koda aka kawo shi Nijeriya sai  wadanda suke  ganin kamar an yi masa abinda bai dace ba suka fara maganar ai ba’a kyauta masa ba, kai akwai su gwamnonin sashen Kudu maso gabashin Nijeriya wadanda suka ce za su rika bibiyar yadda ake aiwatar da shari’ar  sa lokacin da za a fara sauraren shari’ar ta shi. Akwai wata motar da ta dauki shanu zuwa can Jihohin na gabas maso Kudu, sai ga shi shanun suna cikin Tirela hakanan kawai akan banka masu wuta, da haka suna ji suna gani wuta ta gama da su kurmus, amma ba wani daga cikin ko dai su shugabanni na Ohaneze Ndiigbo da suka kallon cewa abin bai dace ba, bare kuma su gwamnonin na kudu maso gabashin Nijeriya. Yanzu kuma lokaci ya yi da zai girbe abinda mutum ya shuka ai bace ma shi aka yi, ba, a gonar bace ya yi shukar, bayan ya san shi ya yi shukar, ya kuma yi huri, maimai, da kuma sarsarya, tunda yanzu lokacin girbi ya yi kamata yayi ace su bar shi zai iya yin komai da kansa.

Idan kuma muka dawo kan shi al’amarin na Sundaya Igboho shi ma ya aikata lafuka dai dai na shi, shi ma ba wata Kanwar lasa bace, a tserewar da  yayi shi ma bayan da aka kai samame gidan sa, aka kuma samu wasu muggan kayayyaki wadanda suka zama sheda ne kan zarge- zargen da ake yi masa. Bai sha da dadi ba domin kuwa ranar Litinin ce ta wannan makon da muke ciki ya shiga komar masu  neman sa, rana ta vaci ma sa, inda ruwa kuma ya karewa dan Kada amma bai gama wanka ba. Abin dai kamar da kasa inji mai ciwon Ido sai ga shi  an sake tafka shegiyar wato inda shi ma ‘yan kabilar sa ta Yarabawa suke ta gunagunin ba za su bari a kawo shi  Nijeriya ba ya fuskanci hukuma ba, duk kuwa da sun kwana da sanin cewa shi tsohon mai laifi ne. Lokaci ya yi  har aka kama shi Allah bai bashi damar zuwa kasar da yayi niyya ba ta Jamus, domin kuwa shi babu wanda ya san idan da yayi sa’ar arcewa har ya kai ga kaiwa wurin da yayi kuduri, ai Allah ne kadai ya san shi ma abubuwan da zai rika aikowa ana yi a kasar  sa ta haihuwa Nijeriya.

Lokaci yayi wanda yakamata su masu kiran kansu shugabanni kabila can da wannan, su tuna ba mai aikata ta’addanci domin kawai addiniku da harshen daya ne zaka goya wa baya ba, wannan ba karamin rashin wayo bane da kuma  rashin sanin abinda ka iya zuwa ya kuma dawo, saboda ai komai nisan jifa kasa zata. Koda kuwa zata kai shekaru nawa kafin ta kai ga fadowa kasa.

Dokokin kasa kamata ya yi su yi aiki kan ko wanene mutum da kuma wadanda suke rufa masa baya, a tuna fa duk wata shegantaka ta mutum sai gwmnati taga dama ta kyale shi, sai dai kuma duk lokacin da hankalinta ya dawo kan shi to ya kuka da kan shi , kar ya kuka da kowa. Abin ba zai yiyu ba kuma har ila yau bai dace ba don kawai mutum kun fito da ga wuri daya kuna magana da harshe guda da addininku daya, bayan ya aikata laifi kace ba za a isa a hukunta shi ba, a kyale shi kawai, wannan ba wata magana bace wadda za a saurara kamata ya yi ita gwamnati tayi duk abubuwan da doka ta shimfida. Idan kuma mutum bai son Jaki ya kada shi to kada fa ya hau, muddin kuma  har ya kai ga hawa sunan shi fa kasasshe kuma kadadde. Lokaci kuma har ila yau ya yi da su wadanda suke nuna goyon bayan na su, duk wadansu ayyukan ashsha da suka aikata ma wasu wannan ba wani abu bane su dai kada a tava masu nasu duk kuwa  sharvotan da suka yi domin su shafaffu ne da mai. Gwamnati musamman ma ta tarayya kada ta bari a watsa mata kasa, a ido da akwai kotuna da kuma Alkali suma ai aikin su ne su fidda daci daga cikin zaki, su kuma fidda mara kyau daga cikin maikyau, kada mutum bayan ya san aikin sa har ya bari wasu ‘yan bani na iya su fara nuna masa ai ga yadda ya dace ya yi.

Tambaya nan ga su wadanda suke nuna goyon bayan su kan wadanda suke aikata shi, shin suna ganin ayyukan ashsha ad suke aikatawa, hakanan ka wai za  a bar su babu wata kwavawa? Su kuma wadanda ake lalatawa kaddarori da kashe su shin su ba ‘yan kasa bane, ko an lura basu da wayo ne shi yasaake yi masu cin kashi da  kallon hadarin kaji, a fa tuna duk fa wanda ake kokarin kai shi bango to sai fa jiwo ne za a gane ashe shi ma yana da wayo, hakurin da yake yi  ne har ake ganin ko yi ma shi kallon kamar ma bai san ciwon kansa ba ne.

 

Exit mobile version