Connect with us

NAZARI

Rashin Gaskiya Da Son Rai Daga Masu Sukar Janar Monguno

Published

on

Babu wani tantama cewa, an cimma nasarori sosai a yaki da ta’addanci, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da barayin shanu. Wannan kuwa saboda irin tarin bayanan sirrin da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya tattara kuma aka yi amfani da su ne. Yanzu wadannan mabarnata sun watse suna gudun neman mafaka. Shi ya sa ma a kwanakin baya aka cafke wasunsu a Kudancin Nijeriya.

Kamar yadda aka sani, dole wannan nasarar ta harzuka masu goya musu baya da kuma makiyan Nijeriya, wadannan da ke so a ci gaba da zama cikin halin rashin zaman lafiya da fargaba. Domin sauke haushinsu, sun yi kutse a kafafen watsa labaran Nijeriya, inda suka dauki marubutan da ke rubuta karairayi, su yi bayanai na bogi don kawai a bakanta gwamnati.

A ‘yan kwanakin nan, wasu daga cikin marubutan nasu da suke daukan nauyi suka yi wani rubutun banza akan mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno. Dalilin yin rubutun shi ne a ci mutunci tare da dauke hankalin Mai ba shugaban shawara kan harkokin tsaro daga wannan babban aiki da yake tsaka da yi.

A daya daga cikin irin wadannan mugayen rubutu nasu, sun yi ikirarin cewa tunda NSA Monguno ya yi gaggawan daura matsalar tsaro kan shugabannin bangarorin tsaro, kenan yana so ne ya wanke kanshi daga zargi. Lallai mutanen a rude suke, walau su ko masu biyansu kudin wannan aiki sun manta cewa aikin NSA shi ne tattara bayanan sirri, su kuma shugabannin bangarorin tsaro aikinsu shi ne aiwatar tare da fuskantar barazanar tsaro. Sai ka rasa ma me suke kokarin cewa.

Sanin kowa ne cewa NSA cikakken masanin harkar tattara bayanan sirri ne, jajirtaccen soja wanda ba a tantamar kwarewarsa. Idan ya yi aikinsa yadda ya kamata wurin tattara bayanan sirri, amma su masu aiwatarwa suka ki yin abin da ya dace, wane ne za a tuhuma da sakaci?

Su kansu masu sukar NSA din sun yarda cewa sai da bayanan sirri sannan za a iya yin galaba kan ‘yan ta’adda. Wanda kuma abin da NSA ke fadi kenan. “Mun yi kokari matuka wurin tattara bayanan sirri. Sai dai nasara tana ga yadda aka tafiyar da wadannan bayanai a aikace.” Misali, ai aikin malami shi ne ya koyar, inda su kuma dalibai nauyi ne da ya hau kansu da su yi aiki da abin da suka koya.

A dai wannan rubutun cin mutunci, wanda makiyan Nijeriya suka dauki nauyi, sun yi yekuwar a sauke Mai ba shugaban shawara daga mukaminsa. Kowa fa ya sani cewa ba yau aka fara wadannan ayyukan ta’addanci ba, gadonsu wannan gwamnatin ta yi daga gwamnatocin baya, don haka dole sai an yi aiki tukuru mai yawan gaske kafin a kawo karshin lamarin gabadaya.

Kai ka ce muna zamanin yada karairayi ne, daya daga cikin irin wadannan mutane da ake daukan nauyi ya yi zargin wai NSA Monguno ba ya ba shugabannin bangarorin tsaro hadin aiki, ba ya tafiya tare da su.

Kowa ya san irin yekuwar da Monguno yake ta yi na cewa dole ne sai an hada karfi da karfe sannan za a iya magance matsalar tsaro a Nijeriya. Amma wannan ba yana nufin kowa zai yi abin da ya ga dama ba, dole ne sai gwamnatin tarayya ta sa hannu domin komi ya tafi daidai da bayanan sirrin da take da su a kasa. Wannan shi ne abin da NSA Monguno ya sanar da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal. Amma duk da wannan kyakkyawar niyya ta NSA, wasu na zarginsa da kin tafiya da abokan aiki.

Ai rashin hankali ne ma su rika kwatanta NSA Monguno da rashin sanin aiki. Mutumin da tsohon Janar din Soja ne, tsohon dalibin ‘Kings College’ dake Legas, wanda kuma duk kwarewarsa a sashen tattara bayanan sirri ya yi, duk da kasancewarsa Injiniya. Yana da kwarewa kan harkar yaki da ta’addanci. Su burin masu sukarsa shi ne su dauke hankalinshi daga gagarumin aikin da ya fuskanta, domin Nijeriya ta fada cikin hayaniya.

Haka kuma NSA Monguno ya sanar da kafafen watsa labarai yayin da ya yi bayani da hausa cewa dukkanin shugabannin bangarorin tsaro hakki ne a wuyansu su rika gabatar da jawabi ga na gaba da su, ba a kodayaushe su rika rige-rigen zuwa wurin shugaban kasa ba. Don Allah mene ne abin aibu wurin kira a yi abin da ya dace?

Sojoji wadanda suka hada da sojin kasa, sojin sama, sojin ruwa suna da alaka da ‘yan sanda, DSS, NSCDC da sauran bangarori domin yaki da ta’addanci, garkuwa, ‘yan bindiga da sauran barna da ke addabar Nijeriya. Amma zancen da NSA ke yi shi ne dole ne a fadada wannan alaka ta yadda za a cimma manufa.

Dole ne a inganta ayyuka irin nasu ‘Operations Crocodile Smiles, Sharan Daji, Harbin Kunama, Ayen Akpatuma, Whirl Stroke, Safe Haven’ da sauransu  domin a kai ga nasarar wannan aiki da aka sanyo a gaba.

Tunda har NSA Monguno shi ne shugaban tattara bayanan sirri na gabadaya Nijeriya, kenan dole ne a barshi ya tsara yadda harkar tsaro za ta kasance a fadin kasar. Idan ya fahimci wata matsala a yanayin tafiyar da aikin daya daga cikin shugabannin bangarorin tsaro, hakki ne a wuyansa nay a tsawatar don a gyara.

 

  • Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC).Advertisement

labarai

%d bloggers like this: