Muhammad Awwal Umar" />

Rashin Hadin Kai Ne Ya Hanawa Kabilar Gwari Zama Gwamna A Jihar Neja –Wanna

Dattijan kungiyar Gbognu Boku Yako na kabilar gwari a jihar Neja, sun nisanta kan su ga tsaida Barista Bello Bawa Bwari na jam’iyyar ACD a matsayin dan takarar gwamnan jihar wanda zai wakilci kabilar gwari a zaben gwamna mai zuwa.
Hakan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na kungiyar bisa jagorancin shugaban kungiyar Gbognu Boku Yako na farko, Alhaji Muhammad Awaisu Giwa Wana a Minna.
Dattijan sun ce ba su ki Barista Bello Bwari ba, dan dan su ne kuma harshen su daya, amma ita wannan kungiyar ba kayan mutum daya ba ce, domin akwai ‘yayan Gbognu Baku Yako a sauran jam’iyyun siyasar jihar nan, ba mu kafa kungiyar nan dan wata jam’iyyar ba, mun kafa ta ne dan lalubo hanyoyin da za a walwale matsalolin da ke tasowa gwarawa
Maganar takarar kujerar gwamna, mun yi sake tun farko domin mun ki hada kai shi yasa lokacin mu ya wuce, ya zama wajibi mu mutunta tsarin karba-karba tunda tabbataccen abu ne a jihar nan, mun yi yunkuri haka a baya amma rashin hadin kai ya kai mu ga rashin nasara, ya zama wajibi mu hakura mu bari har ya sa ke zagayowa kan mu kafin gwagwarmayar karban mulkin ya taso.
Babu dokar da tace ka dauki kungiyar jama’a ka je ka mika ta ga wani dan biyan bukatar kan ka, wannan tsarin na karba-karba tsari ne da dukkan bangarorin jihar nan suka amince da shi, in ma kana bukatar yin hakan ne dan ware kan ka, sai ka kafa kungiyar ka ta siyasa dan yin anfani da ita wajen cimma burin kan ka, saboda mu dattijan wannan kungiyar ba mu amince da a dauki wannan kungiyar da manufar ta ba na mutum daya ba ne ka mika ta ga wani ba.
Ka fin mu ai akwai wasu kungiyoyin kare wasu kabilu a jihar nan, ka taba jin wata kungiyar Nupawa ko Kambari sun dauke ta sun mika ta ga wata gwamnati ko dan siyasa a jihar nan, sai dai ka ji sun tsaya a kungiyance dan kare muradun harshen su, ko anfani da ita wajen walwale wasu matsalolin da ke damun al’ummarsu amma ba ka ji kungiya mai karfi a ce an dauke ta an mika ma wasu ‘yan siyasar ba, to yanzu idan wancan bangaren bai ci zabe ba ke nan ba mu da bakin magana ke nan, wannan ba dai dai ba ne, ba mu amince da wannan kudurin na su ba sam.
Ya kamata hukumar da tai mana rajistan wannan kungiyar ta dubi manufofin mu da muka ba ta kafin mu samu rajista ta jawo hankalinsu, ni na fara shugabantar wannan kungiyar a jihar nan, dan haka na san manufofinta fiye da yadda ake tunani domin ni na fara jagorancin tafiyar da kuma ganin kungiyar ta zama kungiya ta hanyar doka da kuma manufar da muka kafa kungiyar domin ta.
Wannan tada jijiyar wuyar na kungiyar Gbognu Boku Yako ya biyo bayan yadda wasu shugabannin kungiyar suka bayyana amincewa da takarar kujerar gwamnan jiha ga Barista Bello Bawa Bwari a inuwar ACD a wannan babban zaben zuwa wanda dattijan kungiyar suka nuna rashin amincewarsu da hakan, tare da barranta kungiyar ga wannan nufin na wani sashen shugabannin kungiyar.
Lokacin da ya kamata mu hada kai dan ganin mu ma mun mulki jihar nan ba mu yi hakan, ganin hakan yasa mu kai tafiyar Abubakar Bawa Bwari ministan ma’adanai na yanzu, ni kuma a lokacin ma ina rike da mukamin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin masarautu, da kai na aje mukamin, amma rashin hadin kai yasa ba mu yi nasara ba ko zaben ma a wannan lokacin ba taka wani rawar gani ba, kuma da sunan kungiyar mu ka je ba, amma yanzu bisa wannan tsarin da mu kaiwa kan mu dole mu kara hakuri har wa’adin mu ya sa ke zagayowa kila in mun hada kai, mun fahimci kura-kuran mu a gaba an iya samun gwari a kujerar gwamnan Neja amma dai ba yanzu ba kam.

Exit mobile version