Rashin Ilimi Ne Ya Sa Aka Bar Mata A Baya -Amina Gwamna

A makon da ya gabata ne wakilinmu IDRIS UMAR ZARIYA ya ziyarci shahararriyar marubuciyar litattafan nan da ke Kanon Dabo, mai suna HAJIYA AMINA GWAMNA don jin ta bakinta dangane da yadda wasu mata suka bari aka barsu a baya wajen ci gaban zamani da  ɓ angaren zamantakewar rayuwar zaman aure da kuma ilimin boko mai zurfi, Ga yadda zantawar tasu ta kasance.

Malama masu karatu za su so su ji sunan ki da tarihinki?

Suna na Amina Yusuf, Gwamna kuma ni Bafulatana ce kuma yar asalain jihar Kano. Na yi karatu a Magwan firamare kuma na tafi Jahun na yi Kwalejin Kimiyya na yi digiri a  ɓ angaren Biology a F. C. E. Kano kuma na yi karatun kwamfuta a jami’ar Bayaro a yanzu haka ni ce shugabar makarantar nan da a ke kira Abu Nusaiba kuma ni marubuciya ce na littattafan Turanci da Hausa don ci gaban al’ummar mu baki ɗaya, kuma ina da sha’awar amfani da baiwar da Allah ya bani wajen gyara auratayya don ciɗgaban mata, wanda hakan ya sani wasu lokutan nakan shirya taron mata don wayar masu dakai domin samun lada a wajen Allah, taron mukan masa lakabi da (NAGARTACCIYAR  MACE) wanda mata ɗaruruwa kan halarta don samun ilimin zama da maigida kuma ina da sana’o’i daban daban, kamar su hada turare da gyaran amare, dadai sauransu.

Me ke kawo barin wasu mata a  ɓ angaren ci gaban zamani?

To a gaskiya babban abin da kan sa akan bar wasu mata wajen ci gaban zamani shi ne rashin ilimin addini da na zamani sai lalaci da girman kai, wani lokacin kuma talauci na taimakawa, don kaga in har mata na samun ci gaban zamani to tabbas za kaga al’umma na canzawa canji mai kyau inko kaga ana samun matsala to ka duba za kaga anbar matane a baya don ko tarbiyar gidanka ce kaga ta lalace to ka bincika za ka ga matsalar daga matar gidan ne ko kuma mai gidan baya adalci a wannan gida ko kuma ya auro mara ilimin zaman duniya da addini illa iyaka.

Me za ki ce a kan matsalar da ake samu a auren masu ilimi, kuma ga shi an nuna cewa auren mai ilimi ya fi ka auro jahila?

A gaskiya duk wanda zai yi aure to kar ya kula da wani abu face abin da Allah ya ce, ya kula dashi wato mai tsaron Allah duk saura mai sauki ne, in ka ga ji namiji ya yi aure ana samun matsala ko mace ta yi aure ka ji tana samun matsala to in ka bincika ya bi ko tabi son zuciya ne ba son Allah da Annabi su ka bi ba, ga misali namijin da bai ta ɓ a zuwa makaranta ba sai yaje ya auro wacce take jami’a to me ka ke gani zai faru a wannan aure sai dai gyaran Allah don haka duk wanda zai yi aure to ya duba daidai da shi don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wasu mata kance Aure na hana karatu ko suce karatu na hana Aure, me za ki ce a kan haka?

To a gaskiya a halin yanzu ba za mu lissafu ba, wanda muke da aure ga shi muna karatu, domin aure shi ibada ne na Allah baya hana karatu don in har da fahimta to wallahi za ka ga mai gida na biya maki kuɗin makaranta har ki gama ba tare da samun wata matsalaba karatu  shima auren ibada ne don haka ba wanda zai hana wani. idan kika ƙ i Aure wai sai kin gama karatu na farko sai kin jajirce wajen kare kanki daga faɗawa cikin halaka, kuma kar ki manta in kin gama karatun ba lallai bane ki samu miji a wannan lokacin kuma ko ba komai ga mutuwa naci kamar rana ko kuma ma ki koma auren da a ainihin ƙ oƙ on zuciyar ki ba son shi kike yiba amma saboda gudun surutun mutane ne yasa ki ka yi auren, Allah Ya tausaya mana da yaranmu baki ɗaya.

Bincike ya nuna mutuwar aure ya fi yawa a Arewacin Nijeriya, me ke kawo haka?

To gaskiya jahilci ne ya yi yawa don auren da ake yi yanzu da yawa a kanyi shi ne ba tare da an san muhimmancin soyayya ba da kuma rashin sanin ilmin zaman auren a zamanance misali, mace bata san hakin mijin taba miji baisan hakin matarsaba ga rashin kulawa na abin da ya shafi al’amuran yau da kullum, ga sakaci wajen kulawa da shimfida (Romantic Aspect) ga kuma talauci shima yana taimakawa kuma wasu lokutan da sanya hannun iyaye a ciki don za kaga yaro baya sana’ar komai amma an dauko aure an bashi kuma an zura masa ido, to kaga hakan ai ya saba wa tsarin zaman lafiyar aure.

Za a iya magance matsalar yawan mutuwar aure da a ke fama da shi a jihohin Arewa kuwa?

Sosai kuwa.

Ta wacce hanyar?

Hanyar ita ce tun yara na ƙ anana a nuna nasu  muhimmacin ƙ aunar juna tun kafin suyi aure su ganewa idonsu soyayyar da mahaifinsu ke yi wa mahaifiyarsu kuma a nuna mu su cewa aure ibada ne, ba filin danbe bane da zaka jira a dukeka kaima ka rama, a’ a, Allah ya ce a yi don haka kuma yana da ka’idoji. Daga bangarori biyun duk su iya ado wato tsafta wannan shine hanyar magance yawaitar kashe aure.

Wasu mata kance duk wanda ya rike miji a matsayin Uba to zai mutu maraya shin haka ne?

Gaskiya ba haka ba ne don idan mace ta yi dace da miji na gari wanda yake nuna mata soyayya da tsoron Allah da ƙ okarin kamanta adalci to dole ta ce masa baba, amma fa inda mace ke mutuwa a marainiya shine ta yi rashin sa’a ta sami mugu mai baƙ ar aniya to anan ne za ta muta marainiya to amma duk da haka ba zai yi wu a yi wa duk maza kuɗin goro ba akwai masu adalci.

Akwai hanyar da mace za ta mallaki mijnta ba tare da ta kaucewa hanya ba kuwa?

Kwarai kuwa na farko mace ta yi ƙ oƙ ari ta gyara duk wata dangantakar ta da mijin ta kuma nemo itacen rura wutar soyayyar da baza ta bari wutar ta mutu ba har abadan, kuma ta kula da abin ka iya bata masa rasansa ta iya gyara masa shimfidarsa ta kuma daure ta girmama iyayen sa, ƙ oƙ arin iya abinci mai dadi, kwaliya akai akai, lallashinsa da bashi haƙ uri lokacin da aka sami sa ɓ bani kuma ta bayar da jikin ta wajen hutawar mijin ta. Annabi (S. A.W) ya ce, “Lallai a cikin magana akwai sihiri.” Duk sukan sa mace ta mallaki mijin ta ba tare da ta kauce hanya ba. Ta yi ƙ oƙ ari ta iya amfani da kayan zamani na halas wajen mallakar mijin ta Allah ya taimakemu.

To wacece namiji ya kmata ya Aura?

Matar da namiji ya kamata ya Aura itace ma’abuciyar addini wacce ta ke da wayewar zamani kuma ta iya soyayya.  Annabi (S.A.W) Ya ce a kan auri mace ne akan abubuwa guda uku na farko addinin ta, sai dukiyarta kuma idan baku auri ma’abuciyar addini ba to damar ku za ta yi kuka.

Ƙ arshe wani kira za ki yi wa mata akan neman ilmi?

To a gaskiya ya kamata kowace mace ta sani cewa a halin yanzu rashin ilmi ne ya sa aka bar wasu mata ‘yan uwanmu a baya don haka ina kiran mata birni da ƙ auye da su koma karatun addini da na zamani wanda  hakan zai sa a sami sauƙ in magance wasu wahalhalun da mata ke fuskanta a rayuwar da muke ciki a yanzu, kuma za a sami zuriyya masu tarbiya, domin a duk lokacin da aka gina aure akan turbar ilmi to za ka ga auren ya yi albarka, kuma zan yi amfani da wannan damar in sanar da da duniya cewa, nan ba da jimawa ba zan kamala wani lattafi mai dauke da sinadarai da hanyoyi masu sauki ga ‘yanuwana mata don samun ilmin zaman aure a sauƙ aƙ e, kuma ina godiya ga dukkan masu karanta littatafaina da fatan za a ci gaba da bamu shawarwari a duk inda ku ka ga mun yi kuskure na gode Allah ya taimaka mana baki ɗaya.

Exit mobile version