Daga Lawal Umar Tilde Jos.
Shugaban gwamnonin Jihohin Arewa goma sha tara wanda kuma shi ne gwamnan jihar Filato Honarabul Simon Bako Lalong, ya yi kira ga Iyaye da suke a jihohin Arewacin tarayyar kasar nan da cewar su kara zage damtse wajen ba ‘ya ‘yansu ilimin addini da kuma na Boko don kawo karshen matsalar rashin tsaro da rikice-rikicen addini, da na kabilanci da suke kawo tarnaki wajen ci gaba shi yankin.
Gwamna Lalong, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke kaddamar da shi asusun bukatar taimako na naira miliyan ashirin da biyar, da kungiyar Izalatil Bid’ah ‘Wa’Ikamatis Sunnah [JIBWIS], ta kasa reshen jihar Filato, ta gudanar a Masallacin Jumma’a na ‘yan-taya Jos, a ranar Lahadi ta makon da ya gabata.
Gwana Lalong, wanda Kwamishina a ma’aikatar sufuri na Jihar Ustazu Muhammad Muhammad Abubakar ya wakilta, ya bayyana cewar karfafa wa yara guiwa su sami ilmi mai inganci zai taimaka matuka wajen rage yawan fitintinu da suke danuwar yankin Arewacin Nijeriya.
Ya kuma yima jagororan kungiyar addu’a da fatan Allah ya kara basulafiyar da basirar tafiyar da harkokin kungiyar a cikin nasara, kuma yahori al’ummar musulmi dasu cire nuna girmankai wajen neman ilmin addinin musulunci, don su sami sukunin bautawa Allah kamar yadda ya umurce su.
Shi ma da yake jawabi a wurin bikin Shugaban majalisar dokoki ta jiharFilato, Rt. Honarabul Abok Nuhu Ayuba, ya yabawa kungiyar akan gudunmuwar da take bayarwa wajen kyauta’ta zaman lafiya a jihar Filato, ya ce samun ilmi shi yake sa dan Adam ya zama mutum ne na kwarai a cikin al’umma, kuma kungiyar na taka kyakkyawar rawa wajen ilmantar da al’ummar kasar nan.
Shi ma a Jawabin na sa shugaban kaddamar da asusun, Alhaji Abubakar Shu’aibu Aljumma, wanda aka fi sani da suna Saadeek Plaza Jos,.ya nuna farin cikin sa akan sa shi da kungiyar tayi na ya zama shugaban kaddamar da asusun ya ce, da yana kan hanyan tafiya amma saboda muhimmancin taron ya bar yin tafiyar, don ya sami gabatar da gudunma warsa, sai kuma ya yaba akan irin namijin kokari da kungiyar take yi wajen ilmantar da al’umma kuma ya bukaci wadanda Allah ya hore masu da su rika sa jarinsu wajen ayyukan alkhairi don kyautata rayuwarsu ta duniya da kuma lahira.
Shi ma a jawabinsa shugaban kungiyar Izalatil Bid’ah ‘Wa’Ikamatis
Sunnah [JIBWIS], Shiekh Muhammad Sani Yahaya Jingir, wanda mataimakinsa na biyu, Sheikh Sa’eed Hassan Jingir ya wakilta, ya yaba wa shugabannin kungiyar daga matakin kasa har ya zuwa na rassa akan irin kyakkyawan hadin kan da suke bayarwa, wajen gudanar da ayyukan kungiyar, yace imba don hadin kai da kwazo wajen tafiyar da aiki, da ya ‘yan kungiyar ke yi ba, da kungiyar bata kai inda take ba a yanzu ba.
A jawabin sa na godiya shugaban majalisar Malamai na reshen jihar Filato, Sheikh Dokta Hassan Abubakar Dikko, ya nuna farin cikin sa bisa goyon baya, da shugabannin majalisun kananan Hukumomi takwas, na yankin Arewacin jihar suka bayar wajen cimma nasarar kaddamar da asusun.
Daga karshe kuma ya godewa wadanda suka baro dimbin ayyukansu suka zo suka bada gumuwarsu da fatan Allah ya saka wa kowa da alkhairinsa,taimako mafi tsoka na naira miliyan hudu, ya fito ne daga shugaban kaddamar da shi asusun Alhaji Abubkar Shuaibu [Sadeek Plaza Jos], sai kuma naira dubu dari biyar daga wajen gwamnan Jihar Filato, Rt. Honarabul Simon Bako Lalong.