Connect with us

LABARAI

Rashin Imani: Mahara Sun Kashe Sama Da Mutum 100 A Filato

Published

on

•Gwamnatin Jiha Ta Sa Dokar Ta Baci
Daga Sulaiman Bala Idris Da Lawal Umar Tilde, Jos
Wani Babban Malamin Iklisiyya ya bayar da rahoton cewa an kashe mutum 120 a yayin da suke dawowa daga wurin jana’iza a Jihar Filato. Sai dai na su bangaren, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da afkuwar farmakin amma alkaluman da suka bayyana ya sha bamban, inda suka ce mutum 11 ne aka kashe.
Faston wanda shi ne shugaban Iklisiyyar COCIN a karamar hukumar Barikin Ladi ya bayyana cewa, ana zargin makiyaya ne da aikata wannan mummunan ta’adi.
Fasto Pam Chollom ya bayyana wadannan bayanai ne a wata hira da yayi da Kafar Yada Labarai ta yanar gizo ‘PREMIUM TIMES’, inda ya ce, an dauki awowi masu yawa ana aikata wannan ta’addanci a daren Asabar.
“Maharan sun kaddamar da hari ne membobinmu wadanda suka halarci jana’izar mahaifin daya daga cikin limamanmu, Baba Jakawa, wanda aka gudanar a Gidin Akwati dake gundumar Gashis. Marigayi Jakawa ya rasu ne yana da shekaru 80, kuma cikakken dan Iklisiyyar COCIN, wanda hakan ya sa jana’izarsa ta samu halartar mutane da yawan gaske.
“Maharan sun yi mana kwanton bauna ne a lokacin da muke kokarin dawowa, inda suka kawo mana hari suka kashe mutum 34 daga kauyen Nekan, 39 daga kauyen Kufang, 47 daga kauyen Ruku. A yanzun ma da nake wannan maganar, akwai mutane da dama wadanda ba a san inda suke ba, sun bace.” inji shi
Limamin Iklisiyyar ya ci gaba da cewa; “Lamarin ya fara ne tun da misalin karfe 1:00 na rana har zuwa karfe 8:00 na daren jiya (Asabar). Mun yi kokarin sanar da rundunar ‘Special Task Force’ dangane da wannan lamari, inda suka garzaya zuwa daya daga cikin kauyukan, sai dai ko kafin su karasa, maharan sun tafka ta’asa sun kama gabansu.”
Kakakin rundunar ‘STF’ wacce aka fi sani da ‘Operation Safe Haben’, Umar Adams ya tabbatar da afkuwar hare-haren a jiya. Sai dai bai bayyana irin barnar da lamarin ya haifar ba.
su ma a bangarensu, rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Filato ta bakin Kakakin rundunar, Terna Tyopeb, ta sanar da ‘yan jarida cewa, mutum 11 ne suka rasu a farmakin.
Inda Kakakin ya ce, tuni an kai gawarwakin matattun zuwa Babban Asibitin Barikin Ladi. Sannan kuma ya ce, rundunarsu ta baza jami’an tsaro a kauyukan da abin ya shafa.
A nata bangaren, Gwamnatin Filato ta kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe.
Gwamnatin ta sa wannan dokar ne bisa kokarin da ta ke yi don dakile ruruwar wutar sabon rikicin da ya barke yankin kananan hukumomin Barikin Ladi, Riyom da Jos ta Kudu.
Wannan bayanin na kumshe ne a wata takardar sanarwa da Kwamishinan yada labaranm Jihar, Mista Yakubu Datti ya rabawa manema labarai jiya a Jos, Babban Birnin Jihar Filato.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: