A daidai lokacin da zabukan shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a jihar Kogi ke kara karatowa, wani matashin dan siyasa kuma dan takarar kansila mai neman wakiltar mazabar gundumar ‘Ward C’ da ke karamar hukumar Lokoja, karkashin tutar jam’iyyar PDP, Honorabul Umar Abbas Adamu, ya ce rashin jagoranci da kuma shugabanci na gari ne manyan kalubalen da mazabarsa ke fuskanta a ‘yan shekarun nan.
Honorabul Adamu, ya furta hakan ne a yayin da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU JUMA’A a ranar larabar da ta gabata a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
dan takarar wanda ya yi alkawarin gudanar da wakilci na gari idan al’ummar mazabarsa suka zabe shi a matsayin kansila, ya kuma ce akwai ayyukan more rayuwa da daman gaske da jama’ar mazabarsa suke bukata, amma sun rasa saboda rashin wakilci na gari.
Kazalika, matashin dan siyasar ya ce, ya yanke shawarar tsayawa takarar kansilan ne biyo bayan kiraye-kirayen da matasan gundumar na ‘Ward C’ suka rika yi masa na ya fito don cire masu kitse a wuta, ya na mai jaddada cewa, yana da dukkan sharuddodin da ake bukata na tsayawa takarar.
Honorabul Adamu har ila yau, ya yi bayanin cewa akwai kudurori da kuma shirye-shiryen da ya tsara na inganta rayuwar al’ummar mazabarsa ta gundumar ‘Ward C,’ idan har Allah ya ba shi nasarar lashe zaben.
Ya kuma ce yana da yakinin lashe zaben fitar da gwani da jam’iyyarsa ta PDP za ta gudanar don tsayar da dan takararta na kansila a gundumar ta ‘Ward C.’
dan takarar ya kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha (SIEC) da ta gudanar da zabukka masu tsafta da inganci ba tare da nuna son kai ko bambancin jam’iyya ba.
Daga bisani, Honorabul Adamu ya yi kira ga dimbin magoya bayansa da su fito kwansu da kwarkwata don zabarsa a matsayin kansila.
A watan Satumbar wannan shekara ta 2020 ne dai ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kogi (SIEC) za ta gudanar da zabukkan shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a dukkan yankunan kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar ta Kogi.
Za A Kulle Duk Layin Da Ba A Yi Rijistarsa Da Katin Dan Kasa Ba Ranar 9 Ga Fabrairu
Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin da aka diba wa ’yan...