An bayyana rashin kudi masu gida rana da kuma filin gudanar da harkoki a matsayin manyan matsalolin dake ciwa kungiyar masu harkar Gwangawan tuwo a kwarya.
Daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a harkar na gwangwan dake Lokoja, babban birnin jihar Kogi, Mallam Jamilu Abdulkadir ne ya bayyana hakan, a yayin da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP Ayau a ranan lahadi a garin Lokoja.
Mallam Jamilu wanda dan asalin jihar Kano ne yace sana’ar gwangwan, sana’a ce mai albarka amma kuma rashin jari da yan kungiyar ke fuskanta na kokarin gurgunta sana’ar su ta gwangwan.
Kazalika ya kara da cewa rashin filayen gudanar da harkar, shima babban cikas ne ga sana’ar, wanda cewarsa yana samun habbaka ganin cewa matasa da dama sun rungumi harkar na gwangwan don dogaro da kawunanansu.
Ya ce, a yanzu haka yana da yara fiye da Ishirin dake aiki a karkashinsa wadanda, a cewarsa akasarinsu da sana’ar na gwangwan suke daukar dawainiyar kansu da iyalansa.
A kan haka nema mallam Jamilu ya roki gwamnatin jihar Kogi data karamar hukumar Lokoja dasu taimaka wa yayan kungiyar da kudade da kuma filaye domin inganta sana’ar su ta gwangwan.
Sai dai kuma yayi kira ga mambobin kungiyar ta gwangwan dasu zama tsintsiya madaurinki daya, yana mai cewa sai da hadin kai, za a samu ci gaba.
Har ila yau ya gargadi yan kungiyar dasu guji aikata laifufuka da ka iya bata sunan kungiyar, inda har ma yaja kunnensu da cewa duk dan kungiyar da aka kama da aikata laifi, za a mika shi ga hukuma don hukunta shi dai dai da laifin daya aikata.
Daga nan Mallam Jamilu ya yabawa shugabannin kungiyar na gwangwan a bisa kokarin su na hada yayan kungiyar dake jihar ta Kogi.