Rashin Kaya A Gida Ya Sa A Ke Zuwa Chana A Sayo – Shehu

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

 

An bayyana dalilin da ya sa yan kasuwa ke fita kasashen Duniya su sayo kayayyaki na sayarwa yanada alaka da rashin yin kayayyakin a kasar nan, sakamakon durkushewar Kamfanonin gida.

Manajan kantin”Atagi Inbestment” da ke kasuwar Kantin Kwari a Jahar Kano. Abdurrahman Shehu Dalhatu ya shaida hakan da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau.

Ya ce rashin kanfanoni dake yin kayan a kasar nan yasa dole a fita waje a kawo, da ace anayi a gida, yan kasuwa za sufiso su gina gidansu maimakon gina wasu a waje.

Ya ce akwai matsaoli da ake fuskanta a yanzu a harkar kasuwanci musamman ta wajen samun biza na zuwa a sayo kayan daga kasar Chana, saboda samun tsaiko sosai da ak e wajen bayarwa, an matse harkar ba a samun bizan kan lokaci.

Abdulrashid Shehu Dahatu ya ce in an shigar da neman biza sai a shafe watanni ba a samu ba, wannan tsaiko kuma daga “embassy” ake samu. Yakamata Gwamnatin tarayya da ta jahar Kano ta duba lamarin ta shigo domin ta samarda sauki ga yan kasuwa masu fita waje sayo kaya.

Abdulrashid Shehu Dalhatu ya ce sannan kuma akwai matsala ma da suke samu da hukumar Kwastam wajen kwace musu kaya da suke, wanda hakan ke jawo hasara ga yan kasuwa koda sun basu kayan daga baya saboda sai kaga ba a sayarba domin lokacinda ake bukatarsu ya riga ya wuce an daina yayinsu.

Shima a nasa bangaren Shugaban Atagi “Inbesment”Alhaji Sagir Yusuf Usman yayi kira ga Gwamnati ta farfado da kamfanonin saka na cikin gida zai taimaka wajen tsayawa a rika sayen kayayyakin da ake sakasu a gida, ba sai ana zuwa kasashen Sin ko Dubai, dan samo kayan da ake da bukata ba, in ana yin irinsu a kasar nan.

Exit mobile version