Muhammad Awwal Umar" />

Rashin Kiyaye Hakkin Matasa Ke Jefa Su A Halin Ta’addanci –Ishak

Exif_JPEG_420

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Sakacin gwamnati da rashin mayar da hankalin ta akan nauyin da rataya akanta na al’umma ne ya jefa matasan kasar nan a halin da suke ciki yau. Shareef Ishak Adam, wani Malamin addinin musulunci kuma matashi ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a minna.

Shareef Ishak ya ce an bar jaki ne ana bugun taiki. Ya ce a rayuwar matasa akwai ginshikai uku da ake bari a baya, na farko mahaifa, sai gwamnati da malaman addini, amma matsayin gwamnati yafi komai muhimmanci, wanda watsi da hakan ya jefa dubban matasa a gararanba wanda kuma da shi ne ‘yan siyasa ke fakewa a lokuttan siyasa dan samun nasarar siyasar su.

Ya zama gwamnati ta kula akan hakkokan matasa tare da infanta bangaren ilimi ta yadda tsarin ilimin  zai yi tasiri da saukin samuwa ga matasa karfi. Idan ba a saukaka a tsarin ilimin ba, ba yadda mai karamin karfi zai iya samun damar yin karatun koda yana da muradin hakan. Ni da ke wannan maganar na yi karatun har a matakin digiri duk da cewar akwai wadatar ni kadai na san zango da na ciwo.

Talauci da matsalolin arziki ya taimaka wajen rashin mayar da hankalin Iyaye akan tarbiyar yara, wanda kuma ba boyayyen abu ba ne duk irin yadda mai karamin karfi ke muradin ganin dan shi ya samu nagartaccen ilimi hakan ba zai yiwu ba saboda ita gwamnatin ma ta kasa gyaran na ta wanda nan hanya mafi sauki wajen baiwa ‘Yayan marasa  karfi ilimi. Idan ka duba a shekarun baya kadan kowa ya shaida cewar gwamnati da gaske ta ke musamman kan tsarin bada ilimi kyauta wanda kowa ya shaidi hakan, amma yanzu an dauka yara matasa ba su da alfanu sai lokacin zabe, wanda a lokacin ne ake karairayin kawo sauyi a rayuwar su.

Shareef ya ce ko malamai na da rawar takawa a inganta rayuwar matasa ta hanyar yin bayanai na gaskiya ga Iyaye da gwamnati ta yadda kowa zai iya sauke nauyin da ke kanshi, dora laifin tabarbarewar rayuwar matasa akan Kansu wannan babban kuskure ne, yanzu ba za ka iya bada kididdiga na adadin matasa da suka kammala karatun sakandare, gaba da sakandare har zuwa Jami’a ba kuma suna zaune ba aikin yi.

Mun taso mun ga yadda ake taririya da kara karin guiwa ga yara masu kwazo dan kara masu azamar karatun.

Idan ana bukatar rage rashin aiki tsakanin matasa da kara masu sha’awar karatun ya zama wajibi gwamnati ta samar da gurabun aiki ga ‘yan boko da ma wadanda ba su yi bokon ba. Komai ilimin ka indai ba aiki ilimin ba zai yi anfani ba, shi ilimi haske ne wanda ke taimakawa wajen nuna maka hanya.

Akwai da daman matasa da ke baiwa kuma da gwamnati za ta taimaka masu zasu taimaki kan su kuma su taimakawa rayuwar wasu, duniya ta cigaba ne da fasaha ta hanyar kirkira wanda kuma matasan kasar nan daga cikin matasan duniya da Allah ya yiwa irin wannan baiwa.

Exit mobile version