Umar A Hunkuyi" />

Rashin Kudi Yana Barazana Ga Aiwatar Da Kasafin Kudi

Har yanzun ba a fara aiwatar da manyan ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2018 ba, kasantuwan rashin kudade, kusan watanni biyu da sanya hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi a kan kasafin kudin, kamar yanda binciken mu ya nu na.

Ministan tsare-tsare da kasafin kudi, Udoma Udo Udoma, ya ce za a cike gibin da ke cikin kasafin kudin ta hanyar ranto Naira Bilyan 1.643 daga wasu wurare na ciki da wajen kasar nan.

Gwamnati za ta ranto Naira bilyan 793 daga nan cikin gida, sannan kuma ta ranto Naira bilyan 849 daga wasu hanyoyi na waje.

Sai dai har kawo yanzun, shirin karbo rancen da gwamnatin ta tarayya ke yi, bai samu amincewar majalisun kasa ba, wanda suka ta fi hutun watanni biyu.

Wani jami’in fadar ta shugaban kasa ya ce, an aika da bukatar ta neman rancen ga majalisar tarayyan tun kafin su ta fi hutu, sai dai wani daga cikin shugabannin majalisar wakilai ta kasa ya ce shi bai da masaniyan hakan.

Kwararru sun nu na tsoron su kan takun-sakan da ke tsakanin shugabannin majalisun da fadar shugaban kasa zai iya kawo tsaiko kan sanya hannu a rancen da ake nema.

Majiyoyin gwamnati ta tabbatar da cewa tilas ne a yi jinkirin aiwatar da manyan ayyukan, duk da cewa tuni lokacin da ya kamata ma a ce an kammala wasu ayyukan ma ya wuce, wanda ya sanya tilas a sauya lokutan kammala su din, kan rashin samun rancen da ake nema domin aiwatar da ayyukan.

Jinkirin aiwatar da wasu ayyukan

Wasu daga cikin manyan ayyukan da jinkirin aiwatar da kasafin kudin zai iya shafa sun hada da, aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri na Naira bilyan 10, gyaran hanyar Zariya-Funtuwa-Gusau-Sakkwato-Birnin Kebbi, wanda ake yi a kan Naira milyan 704, tagwayen hanyar Odukpani-Itu, Itu-Ikot Ekpene: kashi na 2. Itu-Ikot Ekpene da ake yi a kan Naira bilyan 11.1, gyaran hanyar Enugu zuwa Fatakwal da maishe su tagwayen hanyoyi na sashen Umuahiya zuwa Aba a Jihar Abiya da ake yi a kan kudi Naira bilyan 3.7.

Sauran sun hada da, gyara da fadada hanyar, Abuja-Kaduna-Zaria Kano da ake yi a kan kudi Naira bilyan 22.3,  tagwayen hanyan, Ibadan-Ilorin kashi na II a Jihar Oyo da ake yi a kan Naira bilyan 2.8, gina hanyar, Bodo-Bonny tare da gadan da ta tsallaka sashen, Opobo, a Jihar Ribas da ake yi a kan Naira bilyan 8.7 da kuma wasu ayyukan hanyoyin Jiragen kasa a karkashin ma’aikatar sufuri na tarayya.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a kwanan nan ne ya shaida wa manema labarai cewa, har yanzun ba a daddale kan wanda zai dauki nauyin aikin hanyar Jirgin kasa ta Ibadan zuwa Kaduna ba. Bankin China mai suna EDIM ne zai bayar da rancen kudin in an kammala daddalewa.

“A lokacin da muka zauna da bankin sun nemi da mu rage, amma mu ba mu ga ta yanda za mu iya ragewa ba, amma dai mun tura wa shugaban kasa domin ya duba lamarin bashin a lokacin da ya ziyarci kasar ta China a watan Satumba.

Ya kuma ce, gwamnati za ta biya kashi 15 na kudaden aikin, don haka in sun iya sanya hannu a kan bashin a wannan shekarar, tabbas  za su fara gudanar da aikin ne a shekarar 2019.

Majiyar mu ta nu na cewa, a yanzun haka bankin na EDIM ya bayar da basukan dala bilyan 1.89 kan wasu ayyukan a kasar nan.

 

Exit mobile version