kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta soma tuntubar dan wasanta Kylian Mbappe a kan bukatar sabunta yarjejeniyarsu dake shirin karewa a shekara ta 2022 duk da cewa har yanzu babu wata Magana mai kwari da aka tattauna.
A baya bayan nan ne dai Mbappe ya bayyana cewa har yanzu bai yanke shawarar ci gaba da zama a PSG ba, ko kuma ya sauya sheka zuwa wata kungiyar, wadda ake kyautata zaton ba za ta wuce Real Madrid ba.
Sai dai a bangaren Real Madrid da ta jima tana bibiyar bajintar dan wasan, zai yi wahala ta iya kulla yarjejeniya da shi a nan kusa, la’akari da kalubale har kashi biyu dake gabanta wanda tana bukatar maganace su.
kalubale na farko dai shi ne raguwar kudaden shigar da take samu saboda annobar Korona, sai kuma bashin yuro miliyan 570 da ta karba domin sake fasalin filin wasanta na Santiago Bernabeu, wanda za ta fara biya a farkon shekarar 2022, kuma kawo yanzu yuro miliyan 100 ya zo hannun kungiyar, yayin da ragowar kuma sai watan Yunin shekarar ta 2022.
Kawo yanzu dai Mbappe na karbar albashin yuro miliyan 21 ne duk shekara a PSG wanda ake ganin a halin da ake ciki babu wani dan wasa da yake karbar albashin da dan wasan yake karba tun bayan da kungiyar ta bayar da aron dan wasa Gareth Bale