Connect with us

WASANNI

Rashin Ronaldo Ya Sa Magoya Bayan Real Madrid Sun Ki Zuwa Kallon Wasa

Published

on

Marcelo Ya Damu Da Koma Wa Jubentus
Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Marcelo yadamu da komawa Jubentus domin sake haduwa da abokin wasansa Ronaldo.
Ronaldo dai yakoma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ne a kwanakin baya wanda hakan yakawo karshen shekaru tara dayayi yana bugawa kungiyar wasanni inda ya taimaka mata ta lashe kofuna da dama.
Tuni dai aka bayyana cewa Marcelo ya takura akan Jubentus ta nemeshi domin komawa kungiyar koda a watan Janairun shekara mai kamawa ne sai dai abune mai wahala Real Madrid ta siyar da dan wasan nata.
Marcelo dai ya shafe shekaru goma da rabi a Real Madrid kuma ya buga wasanni 456 a kungiyar a gasanni daban daban har ila yau ya taimakawa kungiyar ta lashe kofuna 19 ciki hard a kofin zakarun turai guda hudu.
Marcelo dai yabuga wa Feal Madrid duka wasanninta guda uku data buga a gasar laliga inda kuma duk sun samu nasara sannan ya wakilci kasar Brazil a gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Rasha.
Advertisement

labarai