Rashin Shigowar Gwamnati Harkar Fitar Da Amfanin Gona Waje Na Kassara Mu —Yahaya Karo

Alh. Yahaya Abdulrahaman Musa shi ne shigaban kamfanin ‘KKU Global Investment Nigeria Limited’ matashin dan kasuwa, ya shara a matsayin dillalin kayan amfanin gona zuwa kasashen waje. Ya nuna irin alfanun amfanin gona a, tattaunawar da ya yi da wakilinmu, Sani Tahir Kano.

Za mu so jin takaitatcen tarihin rayuwarka?

Alhamdu lillah ni dai sunana Yahaya Abdulrahaman Musa, an haifi ne a unguwar, Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa. Na yi makarantar firamare a Dawakin Kudu a shekarar 1989, na yi sakandiren ‘Yar gaya, sannan na karasa a ‘commercial’ da ke nan ‘airport road’ a 1995, na samu shiga jam’ar Bayero a shekarar 2000 inda na yi karatun babbar Difloma a ciniki da mulki zuwa 2003 daga nan na tsunduma harkar kasuwanci.

 

Ya akai aka tsinci kai a harkar kasuwanci?

Tun ina karami mahaifina yake koyamin kasuwanci ni kasuwanci gadar shi na yi da ma mu gidanmu, muna harkar amfanin gona, tun muna siyarwa a nan gida har zuwa kasashen waje, abin da muke yi har yanzu ke nan.

 

Mutane nawa ne suke aiki a karkashin kamfaninka?

A yanzu muna da ma’aikata sama da ddri biyu tsakanin maza da mata da suke aiki ana kawo shi babu gyara mu ne muke sa ma’aikata su gyara shi, kamar sobo, citta, karo, da sauransu sannan a zuba a buhu a tura zuwa kasashen waje.

 

Ku, keke nomawa ke nan ko kuwa?

Ba mu, muke nomawa ba, manoman ne in sun noma suke kawo mana, muna da kwastomomi a Jigawa, Bauchi, Katsina kamar karo daga Maiduguri ake kawo mana Yobe da Sakkwato, nan Kano. Da sauran garuruwa.

 

Wane kira kake da shi ga gwamnati duba da irin alfanun da kuke da shi a cikin al’umma, saboda samar musu aiki da kuke?

Muna so gwamnati ta shigo cikin harkar nan tamu yawancinmu, masu karamin karfi ne kudaden da  muke wannan harkar sun mana kadan. Shi ya sa ma wasunmu ba su iya tura kayan kasashen duniya sai dai a siyar a gida in kuma aka siyar a gida babu riba sosai, muna da kungiyoyi wadanda gwamnati ta san da su.

 

Ba ku zuwa bankuna domin neman rance tunda gwamnati  ta ware kudade don ba wa manoma rance?

Bankuna da yawa sun kira mu mun yi tarurruka kalakala da su sun mana alkawarin za su ba mu rance, to amma har yanzu babu wani hobbasa da aka yi kuma sharudden sa suke kafawa sai kana da wasu abubuwa sannan ka samu rance, yawancinmu masu karamin karfi ne ba su da wata babbar kadara da za a kawo a karbi rancen sai dai a hakura. Muna kira ga manyan masu kudi da su shiga wannan harkar don su dinga bude kamfanonin kaya kamar sobo za mu iya sarrafa shi a nan gida ba sai an fitar da shi ba. In sun sarrafa shi a dawo mana da shi. Misali ganyen shayin sobo ana siyar da kwalinsa Nera (500), kuma kilo dinshi ana siyan shi N300 da sauransu.

 

Daga karshe wane sako kake da shi?

Ni sakona shi ne ina kara kira ga, attajirai da su shigo cikin wannan harkar ta amfanin gona duba da albarkar da Allah ya zuba a gona in har suka shigo ina mai tabbatar wa al’ummah za su karu sosai, ba wai sai mun jira munfitar da kayan amfanin zuwa kasar waje ba muma. Sobo ka ga zu mu iya yin ganyen shayin shi, haka shima karo za mu iya mai da shi abubuwa da dama.

 

Mun Gode

Na g,ode kwarai, Allah ya taimaki wannan kamfanin jaridar amin.

 

Exit mobile version