Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASUWANCI

Rashin Taki Ne Matsalar Manoma ­–Sarkin Noman Potiskum

by Tayo Adelaja
October 3, 2017
in KASUWANCI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Alhaji Adamu hamshaƙin manomi ne, domin kuwa har ya kai matsayin Sarkin noma a garin Potiskum ta Jihar Yobe. A makon da ya gabata ne ya zayyana wa wakilin LEADERSHIP A Yau wasu al’amura waɗanda suka shafi noma da manoma a Jihar Yobe.

Yayin da aka tambaye shi dangane da matsalolin da suka fi addabar manoma. Sarkin yayi godiya da wannan tambayar, domin tana ɗaya daga cikin abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Ya ce: “Na gode da ka yi min wannan tambaya domin kuwa yanka ne aka yi akan gaɓa, domin ina da abin faɗa maka a kai, alal haƙiƙa, a halin da ake ciki mu manoman Jihar Yobe babu babbar matsalar da tafi ci mana tuwo a ƙwarya, da ta wuce matsalar rashin ishasshen takin zamani. A gaskiya wannan na matuƙar damun mu matuƙa. Don haka a kullum roƙon mu ga gwamnatin tarayya da ta Jihar Yobe shi ne, su ɗauki harkokin samar da takin zamani da muhimmanci, kasancewar shi ne abu na farko da ya kamata su yi wa manoma gata da shi.”

Sarkin noman ya ƙara da cewa, babu wani babban tallafin da gwamnatin tarayya za ta fara bayar wa ga manoma, don haɓɓaka harkokin su na noma fiye da samar musu da isasshen takin zamani kuma akan lokaci ba sai lokaci ya ƙure ba.

To amma a bara, a cewarsa saboda rashin takin zamani duka-duka, kayayyakin amfanin gona, ba su wuce buhuna dubu ya samu ba. Don haka rashin takin zamanin shi ya haddasa musu irin wannan giɓi da suka fuskanta.

Da aka nemi jin ta bakin Sarkin Noma, kan ko yana ganin akwai wata mafita ga wannan matsala. sai ya ce; “A gaskiya ni a ganina babbar mafita dangane da wannan matsala ita ce akwai buƙatar lallai gwamnatoci, da su koma ga tsarin da na rarraba takin zamani ta hanyar tanadar da shi, kafin ma faɗuwar damina da kuma bin tsarin bayar da takin kai tsaye, ga manoma tare da

la’akari da irin ƙarfin shi manomin.

“Ina roƙon gwamnatin tarayya cewar in har da gaske a ke kan bayar da fifiko ga harkokin noma to akwai buƙatar, ta zage damtse da kuma ɗaura ɗamara matuka don ganin duk wani tallafin da za ta bayar ga manoma ya kai ga waɗanda ake nufi da shi, labudda ta yin hakan ƙasar nan za ta iya dogara da aikin noma kawai ba sai man fetur ba.

Da yake tofa albarkacinsa dangane da sauran matsalolin manoma, Alhaji Adamu ya ce; “Ba shakka akwai wasu matsalolin da ke addabar mu masu matuƙar muhimmanci, da suka haɗa da samar wa manoma da rancen kuɗaɗen yin noma, da kayayyakin yin noma, da suka haɗa da motocin noma, da kuma sussuka da magungunan feshi da makamantansu. Matuƙar an yi hakan, to na tabbata gwamnatin ƙasar nan ta shugaba Muhammadu Buhari, na iyakar ƙoƙarinta akan ƙudirinta dangane da aikin noma.” Inji shi

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ba Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Bashin Naira Biliyan 39 –Fashola

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 336 A Kasafin Kuɗin Bana Don Manyan Ayyuka

RelatedPosts

Sugar

Alakar Dake Tsakanin Sukari Ca Ciwon Suga

by Muhammad
2 months ago
0

Da yawa a yankin kasashen nahiyar Afirka ana ganin sukari...

A Na Cigaba Da Zaman Doya Da Man Ja Tsakanin Majalisa Da Shugaba Trump

Ba Da Mugun Nufi Shugaba Buhari Ya Garkame Iyakoki Ba – Ministar Kudi

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Ministar kudi da tsaretsare, Uwargida Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar...

Gwamnatin Tarraya Ta Kebe Biliyan N2.6 Don Aikin Tashar Mambilla A 2020

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Sama da shekaru arba’in da suka shude kenan da bada...

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 336 A Kasafin Kuɗin Bana Don Manyan Ayyuka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version