Rashin Tallafi Ya Hana Sana’ar Kiwon Kaji A Kebbi – AYZ Annur 

Kaji

Daga Umar Faruk,

Kiwon kaji wata hanya ce ta dogaro da kai har da samar da ayyukan yi ga matasa musamman masara aikin yi a duk fadin kasar nan.

Haka kuma masana sun bayyana cewa kiwon kaji kashi biyu ne akwai kajin gida da na kasashen turawa wadanda ake kiwon da ilimin zamani. Wanda duk mai bukatar kiwon kaji turawa yana bukatar horo kafin Fara kiwon kajin turawa.

Haka zalika wannan horasawar ta ilimin kiwon kaji yana bukatar kudi domin sayen abinci, magani da sauran abubuwan da ake bukata don gudanar da kiwon kaji na zamani wanda ake tunanin samun riba.

Bisa ga hakan ne wakilin LEADERSHIP A YAU ya ziyarci gonar kiwon kaji na AYZ Annur da ke garin Gwandu inda shugaban gonar, Yahuza Zaki Gwandu ya bayyana yadda kiwon kajin turawa na zamani yake a halin da muke ciki.

Ya fara da bayyana tarihin yadda ya fara kiwon kaji a garin na Gwandu, na fara kiwon kaji Shekaru biyu da suka gabata da kajin turawa guda 50 yan sati biyar da haihuwa masu yin kwai da ake kira a turance (layers) a kan kudi ga kowane Naira dari 750 .

Haka kuma kowace safiya suna cin abinci na Naira dari 600, bayan wata biyu sun kara girma da kuma cin abincinsu zai karu zuwa Naira dari 800.

Hakazalika bayan kajin sun cika makonni 17 ana kiwon su a cikin daki, daga nan za a sanya su cikin daki na zamani da ake kira a turance Battery cage daga lokacin da suka cika sati daya cikin battery cage sun cika sati goma sha takwas ya zama wata hudu da sati biyu zasu fara nasa kwai.

Har ila yau ya ce, “muna sayen buhun abinci kaji a kowane makon kan kudi Naira dubu 3,850, bayan sun fara nasa kwai a cikin kowane mako zamu samu kret na kwai guda 6 da rabi ga wanda ke da kaji guda hamsi, amma wanda ke da fiye da hamsi zai samu fiye da kret shidda a cikin mako, muna sayar da kret din kwai Naira dubu 1,200 saboda tsadar abinci. Wanda a kasuwa suna sayar da kret na kwai kan kudi Naira dubu 1, 300.

A duk mako muna samun rabar Naira dubu 2, 650 a wata ko yazama Naira dubu 10, 600.

“A cewar Yahuza Zaki Gwandu, idan mutun na son fara kiwon kajin turawa akalla yana bukatar tsabar kudi Naira dubu 100 bayan ya tanadi wurin da zai fara kiwon da kuma ‘ya’yan kaji tun daga kwara hamsin har zuwa ko nawa mutun ka iya saye. A shekara idan har mai kiwon kaji na da kaji hamsin zai iya samun riba ta Naira dubu dari 600 ga kudin kwai Kawai, inji Yahuza Zaki Gwandu mai kiwon kajin turawa a cikin garin Gwandu.”

Ribar da na samu a shekarar 2020 ta kai kimanin Naira dubu 127,200, amma yanzu abinda ke bamu wahala da kuma rage muna kwarin gwiwa shi ne tsadar abincin kaji da kuma wahalar samu, a shekarar da ta gabata muna sayen buhun abincin kaji a kan Naira dubu 3,850, amma yanzu buhun abincin kaji ya kai Naira dubu 5, 300 ga duk buhu daya wanda a nan take an samu karin Naira dubu 1, 450 a kowane buhu guda na dusar kaji,wannan karin yasa duk wanda ke da karamin jari cikin matsala da kuma tunani na yaya za ya yi, kai bari ma na sheda maka cewa a halin yanzu a duk garin Gwandu ni kadai ne ke da kajin da ke nasa kwai a cikin masu karamin jari, Saboda tsadar abinci yasanya da yawan masu kiwon kaji komawa ga kajin da ake kira brolars don sun danfi saukin kiwo wasu kuma sun bar sana’ar kiwon kaji.

Saboda muna kira ga gwamnatin da kuma masu ruwa da tsaki kan sana’ar kiwon kaji da su kawo dauke ta hanyar bada tallafi na jari ko kayan da zasu karawa ma su sana’ar kiwon kaji kwarin gwiwa kan tabbatar an inganta sana’ar kiwon kaji a yankunan kananan hukumomin jihar Kebbi.

Domin rashin tallafi ya hana samun cikaken bunkasa na sana’ar kiwon kaji a jihar ta kebbi musamman ga masu karamin jari.

Bugu da kari muna neman gwamnatin ta taimaka wurin ganin cewa an ba masu sana’ar kiwon kaji masu karamin karfi horo da horassuwa kan ilimin kiwon na kaji ta hanyar zamani wanda zai taimaka ainun wurin bunkasa kasuwancin na kiwon kaji a duk fadin jihar. Ya kuma kara da cewa” akwai bukatar samar da kayan kiwon kaji na zamani kamar battery cage domin wanda nake amfani dashi ba na zamani ba ne. Battery cage na zamani ana sayar dashi a kan kudi Naira dubu 48,437.50 ba da kudi daukowa ba, haka sai kuma na gida ana sayar dashi kan kudi Naira dubu 65,000 wanda a Ibadan jihar OYO a keyin sa, duk battery cage daya yana dauakar kaji 96, inji Yahuza Zaki Gwandu mai sana’ar kiwon kaji a garin Gwandu a jihar Kebbi”.

Daga karshe ya kara da cewa duk ka’idodin da aka shata kan bada tallafin bashin NIRSAL da SMEDAN na cika tun shekarar da ta gabata, amma har yanzu shuru kake ji kamar an shuka dusa. Saboda haka muna kara kira ga gwamnatin da hukumomin da abin ya shafa suyi waiwaye kan wannan domin ita ma wata matsala ce wadda ke hana gudanar da sana’ar kiwon kajin.

 

Exit mobile version