Rashin Tsaro A Abuja: Al’ummar Kuje Sun Yi Zanga-zanga

Pic.13. Acting IGP, Mohammed Adamu, during the handing over ceremony of the 19th to the 20th IGP at the Police Headquarters in Abuja on Wednesday (16/1/19). 00555/16/1/2019/Anthony Alabi/NAN

Wadansu mazaunna garin Pegi dake karamar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja a raar Laraba sun gudanar zanga-zangar dangane da rashin tsaro na sace-sacen jama’a da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin. Musamma ma yadda aka sace wadansu a kwanan nan.

Masu zanga-zanga wanda suke gudanar da ita ta lumana sun rufe kofar shiga Sakatariyar Kuje din, suna dauke da takardu da aka yi rubutu daban-daban da ya hada da; “Kidnappers on rampage in Kuje”, da “Give us security in Pegi community” wato ‘Garkuwa da na ci gaba a Kuje’ da kuma ‘A Bamu tsaro a Pegi.’

Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa mahukumta a Abuja da karamar hukumar Kuje sun kasa ba su tsaron da ya kamata. Inda ake sace su daya bayan daya. Sannan sun yi zargin cewa sun kasa gama titin da ya hada su da garin Kuje, sannan an yi watsi da asalin yadda za a yi aikin.

Aderibigbe Taiwo, shugaban masu zanga-zangar ya shaidawa manema labarai cewa; manufar yin zanga-zangar shi ne domin jawo hankalin hukumomin domin su san me ke faruwa na rashin tsaro a yankin tare da irin wahalhalun da mutanen yankin ke fuskanta.

Exit mobile version