Kusan ana iya cewa al’ummar Nijeriya sun shiga zulumi da zaman fargaba da kuma rashin tabbas tun bayan sace dalibai maza sama da 500 a makarantar sakandiren Kankara da ke Jihar Katsina. Boko Haram ce ta dauki alhakin yin garkuwa da daliban, ko da yake har yanzu ba a ji komai daga bangaren hukumomin Nijeriya kan sakon muryar da kungiyar masu tayar da kayar bayan ta fitar ba. Wannan yanayi na matsalar tsaro ga alama ta sa wasu jihohin Arewacin kasar kaukar matakin rufe makarantunsu.
Jihar Katsina ce ta fara rufe nata makarantun, sai Zamfara ta sanar da irin wannan mataki kan makarantu bakwai a yankunan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna da kuma Sokoto. Jihohi kamar Jigawa da Kaduna, su ma sun sanar da rufe makarantu, amma sun ce sun yi hakan ne saboda Annobar Korona.
Jihar Kano ta biyo baya inda a daren Talata ta sanar da rufe makarantun kwana sannan ta umarci iyaye su kwashe ‘ya’yansu ba tare da bata lokaci ba. Lamarin dai ya zo ne kwana biyar, bayan sace daruruwan dalibai a garin Kankara.
A wannan shekarar daruruwan mutane sun mutu a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriyar wanda galibin lokuta ake alakanta wa da ‘yan bindiga ko fashi, sai dai a yanzu akwai shakku da diga ayar tambaya kan ko ta’asar da ake tafkawa a wadannan yankuna na da alaka da Boko Haram.
Masana suna mai gargadin cewa rashin yi wa warwara tufka tun a kan lokaci na iya durkusar da yankin Arewa, ganin a kulum abubuwa sake rincabewa suke. Wasu na ganin shugaban babu wata damuwa tattare da shi ganin yadda ake ta yawo da hotunan bidiyo da ke nuna shi ya kai ziyara gonarsa.
“Akwai rashin nuna kwarewa da nuna halin ko-in-kula, da rashin sanin mene ne shugaanci da Buhari ke nunawa,” a cewar Tsohuwar Ministar ilimin Nijeriya Oby Ezekwesili a tattaunawarta da BBC. Tsohuwar Ministar ta zargi gwamnati da nuna sake da kuma ambatar ‘yan ta’adda a matsayin ƴan fashin daji.
Iyayen yara da daliban da dama sun bayyana takaici da wannan hali da munanar matsalar tsaro abin da ya kai ga wasu jihohi na rufe makarantu. Ko da yake akwai jihohin da ke danganta rufe makarantu da sake dawowar annobar Korona, sai dai akwai masu ganin yanayin tsaron kasar ne sila.
Wasu iyayye da kafifin yada labarai suka zanta da su da kuma dalibai sun nuna takaici da rokon gwamnati ta kawo karshen wannan yanayi da ake ciki ganin a baya an shafe watanni ana zaman gida saboda annobar. Iyaye na fargabar makomar ilimi a Arewa inda aka gagara shawo kan barazanar da tsaro ke haifarwa a kasar.
Satar mutane domin neman kudin fansa abu ne da ya jima yana ciwa al’umma tuwo a kwarya, wannan dalili ya sanya matafiya suka rage sannan aka takaita balaguro a kasar. Karuwar lamarin ya sanya ana ta kokwanto da tambayar yadda masu garkuwar ke cin karensu babu babbaka, har su gaggari jami’an tsaro.
Amma satar daliban Kankara a yanzu ya sake baje sabon babi, inda wasu ke tambayar ko dama ‘yan Boko Haram ne suka sauya salo. Hankulan ‘yan Nijeriya a yanzu a tashe ya ke, kuma a na zama cikin yanayi na rashin tabbas la’akari da cewa a kullum labarin sauyawa ya ke.
A shekara ta 2009 mayakan Boko Haram suka soma kai munanan hare-hare, mafi aksari a yankunan Arewa maso Gabashin Nijeriya. Dubbai sun mutu, kazalika milyoyi sun rasa muhallai da tilasta musu hijira.