Rundunar Sojin saman Nijeriya (NAF) ta yi fatali da rahotanni a wasu sassan kafafen yada labarai cewa yarjejeniyar kwangilar da aka kulla tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Amurka (USA) don samar da jirgin sama 12 A-29 Super Tucano na cikin hadari saboda “Mummunan titin jirgin sama” dake 407 Air Combat Training Group (407 ACTG), Kainji.
Daraktan hulda da jama’a da bayanai na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, a cikin wata sanarwa da aka gabatar ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, ya ce Mataimakin Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojan Sama, Sanata Mike Nnachi, yayin da yake yi wa kwamitin da ke kula da kasafin kudi na Majalisar Dattawa bayani game da kudaden da rundunar ke bukata acikin kasafin kudin na 2021, bayanan kudin jirgin ya fito filii.
Idan za a iya tunawa, Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojan Sama ya fada a makon jiya cewa Nijeriya na fuskantar barazanar rasa dala miliyan 493 da aka biya Amurka don sayen jiragen yakin Super Tucano, saboda hanyar jirgin saman kasar bashi da ingancin da zai dauki jiragen yakin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanya kudi a $ 493m a shekarar 2018 ga wani kamfanin kasar Amurka domin siyan jiragen domin shawo kan tayar da kayar baya da sauran matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.