Rashin Tsaro Ba Kwakkwaran Dalili Ba Ne Da Zai Hana Zaban 2023 – Moghalu

Rashin Tsaro

Daga Yusuf Shuaibu,

A kwanakin da suka gabata ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa hare-haren da ake kai wa ofishoshinta a wasu bangarorin kasar nan za su iya shafar harkokin zaben shekarar 2023.

Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Kingsley Moghalu ya bayyana cewa, rashin tsaron da ake samu a Nijeriya ba kwakkwaran dalili ba ne da zai hana gudanar da zaban shekarar 2023.  Moghalu wanda shi ne dan takarar jam’iyyar YPP a zaben shekarar 2019, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja. Ya ce ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage wajen gudanar da zaban shekarar 2023 duk da farmakin da ake kai wa ofishoshin hukumar INEC da ake yi a wasu yankuna da ke cikin kasar nan.

“Ina tunanin ya kamata mu fahimci cewa muna cikin dimokaradiyya ce, ko Amurka ta gudanar da zabe lokacin da ake cikin yaki. Ba na karfafa tunanin wadannan abubuwa ne za su hana mu gudanar da dimokaradiyya dukka saboda rashin tsaro a Nijeriya.

“Ko shugaban kasa Buhari a cikin jawabinsa na ‘yan kwanakin nan, ya bayyana cewa za a gudanar da zabe a shekarar 2023, ina mai tabbacin cewa wannan kyakkyawan  matsaya ne kuma ina tunanin shi ne matakin da ya dace a dauka,” in ji Mista Moghalu.

Kafin ganawarsa da shugaban kasa Buhari, shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ya yi magana a kan rashin yuwuwar gudanar da zaban shekarar 2023, sakamakon hare-hare ‘yan bindiga da suke farmakan ofishoshin hukumar zabe a wasu jihohin kasar nan.

Farmakin da aka samu a wasu jihohin kasar nan sun yi sanadiyyar lalata ofisoshin hukumar zabe guda guda 42, wanda suka shafi gine-gine da kayayyakin zabe da sauran kayayyaki wadanda ba na zabe ba.

Mista Moghalu ya gabatar da shawarwari guda biyar ga gwamnatin tarayya wadanda za su taimaka wajen hada kai ‘yan Nijeriya. Daga cikin shawarwarin dai sun hada da, ya bayar da shawarar kafa wata hukumar tattaunawa na gaskiya. A cewarsa, hukumar ta kasance ta kunshi mambobi guda bakwai masu zaman kansu kuma a sami mutum daya a kowani yankin da ke fadin kasar nan, a sami dayan mamba daga kasar waje da saka hannun majalisar dinkin duniya ko daga yankin Afirka ta Kudu, ta kasance sun dauki tsawan wata shida suna gudanar da bincike kamar yadda aka yi a watan Junairun shekarar 1966 zuwa watan Junairun shekarar 1970 tare da gayyatar shaidu da masu shaka ido wajen gudanar da bincike da bayar da shawarwari da zai kawo yafewa juna da kuma gina kasa.”

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ya bukaci shugaban kasa Buhari ya gayyaci wadanda suke neman ballewa wajen tattaunawa da samo hanyoyin magance matsaloli da samar da sabon tsarin mulki a kasar nan.

“Ya kamata shugaban kasa Buhari ya kafa kwamitin masana tarihi da za su gabatar da rikicin da aka taba samu a tsakanin yankin Arewa da kuma Kuduncin Nijeriya, da sake bibiyan hanyoyin da aka bi wajen kawo karshen lamarin. Yana da kyau a sake duba yadda aka warware yakin basasan Nijeriya domin gudanar da tattaunawa da dinke farakan da ke gudana a halin yanzu.

“Ya kamata a saka ranar 30 ga watan Mayun na kowacce shekarar a matsayin ranar tunawa da miliyoyin mutanen da suka mutu lokacin yakin basasan Nijeriya,” in ji shi.

Bugu da kari, Mista Moghalu ya yi magana a kan bukatar samar da karamin tsarin kasa wajen horar da jami’ai domin kwarewa a kan aikinsu. Ya daura alhakkin farmakin da ake kai wa a yankin Kudancin Nijeriya a kan ‘yan siyasa, wanda ya bukaci mutanen yankin da su yaki ‘yan siyasan a zaban shekarar 2023.

“Yana ganin ‘yan siyasa da dama wajen matsalolin tsaro da ake samu a cikin kasar nan, a wasu lokutan kuma aiki ne kawai na ta’addanci. Mun sani cewa akwai hannun masu kokarin ballewa a cikin tabarbarewar tsaron kasar nan. Akwai hade-haden abubuwa masu yawa a cikin lamarin.

“Akwai masu ganin ana kawo rikicin bangarance ne domin a hana babban zabe mai zuwa,” in ji shi.

Exit mobile version