Rashin Tsaro: Matsalar Abinci Ya Kunno Kai Yayin Da Manoma Suka Bar Gonakinsu

abinci

Daga Mahdi M. Muhammad,

Rahotanni sun nuna cewa, al’umomin da ke noma a jihohin Benuwai da Nasarawa suna fuskantar hare-hare ba kakkautawa a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ke haifar da damuwar yiwuwar matsalar karancin abinci idan ba a yi wani abu cikin gaggawa don magance lamarin ba.

Manoma a yankunan da ke fama da rikici na jihohin Benuwai da Nasarawa suna cikin mawuyacin hali a halin yanzu saboda yawan hare-hare daga ’yan bindiga ya tilasta yawancinsu barin gonakinsu.

Wadannan manoma sun ci gaba da yin kuka kan rashin zuwa gonakinsu, musamman a lokacin damina.

A Benuwai, mafi yawan manoman da abin ya shafa a kananan hukumomi daban-daban na jihar suna cikin damuwa game da halin da ake ciki, wanda suka ce mai yiyuwa ne ya yi tasiri kan samar da abinci a cikin watanni masu zuwa.

Yayin da wadanda ke wurare kamar Gwer, Guma, Makurdi, Logo, da sauran wasu yankuna ke fama da matsaloli daban-daban, wasu kuma daga Sankera suna fuskantar matsaloli masu tsari biyo bayan wasu matakan da Gwamna Samuel Ortom ya jagoranta don ragewa rashin tsaro da ke damun yankin.

Wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kori wasu daga cikin wadannan manoma daga gida tun daga shekarar 2018, yayin da wadanda ke Sankera galibin ayyukan ‘yan ta’addan yankin ne ya kore su, da kuma mamayar makiyaya da makamai.

Sankera ta kunshi kananan hukumomi uku, Kastina-Ala, Ukum da Logo.

Manoma da sauran masu kasuwanci suna samun matsala mai wahala su kwashe kayan su daga wani wuri zuwa wani, ko kuma su ci gaba da harkokin su na noma a Sankera.

Ga manoman Sankera, dokar da gwamnatin jihar ta kafa kan hana amfani da tsohuwar samfurin Toyota Corolla, ta ce ana amfani da ita sosai a yankin don aikata laifuka, baya ga haramcin da aka yi a baya na amfani da babura kowane iri a yankin har sai an sake nazarin lamarin matsalar tsaro, ta shafe su ta wani bangare yayin da mamayewar makiyaya dauke da makamai a yankin Logo ya sake afka musu.

Wani manomi a karamar Hukumar Ukum, ya nuna damuwa kan haramcin, yana mai cewa ya haifar da wahala a kan mutane, wanda akasari ake ganin shi ne mafi yawan masu noman dawa a jihar.

Ya ci gaba da cewa, “mutanen yankin na matukar shan wahala. Rashin tsaro yana bamu wahala. Tun a farko, gwamnati ta hana amfani da kekuna, kuma a kwanan nan, amfani da Duck Nyas, wata tsohuwar samfurin Toyota Corolla. A Binuwai, muna da fili mai yawa don noma. Yawancin filayen noma ba su da nisa da gida kuma ba za ku iya zuwa can da kafa ba, don haka manoma suna amfani da baburansu.”

Ya ci gaba da cewa, “ba za mu iya zuwa gona ba kuma. Yana shafan kaina ne saboda ina da wani babur da mahaifiyata take amfani da shi da kuma Toyota Corolla da mahaifina ma ya yi amfani da shi. A yanzu haka, mahaifina ya ajiye motarsa ​​a kauye kuma mahaifiyata ba za ta iya amfani da babur dinta ba. Yana da wahala mu je wadancan gonakin da ba su kusa da gidan mu.”

Har ila yau, wani manomi a garin Tor Donga na Kastina-Ala, Iorliam Jastrow Aondonwo, ya ce, kalubalen na da yawa, kamar yadda yawancin manoma a yankin, ciki har da shi, suka koma ga yin azumi tare da yin addu’ar Allah Ya dafa wa gwamnati don juya wasu matakan tsaurara.

Aondonwo ya ce, matsalar ta fi shafar manoma, inda ya kara da cew, haramcin babura, wanda shi ne babbar hanyar motsa su, ya tilasta musu daina zuwa gona.

Ya ce, “yanzu haka mutanen yankin sun koma yin tattaki. Halin da ake ciki mai tsanani ne, kuma idan ba a sake duba shawarar da gwamnati ta yanke ba, za a samu karancin abinci kuma dole ne mu dogara da samar da abinci a wajen jihar.”

“A halin yanzu, mu manoma mun koma yin addu’a a cocinanmu domin gwamnati ta sauya ra’ayi. Na yi imanin akwai wasu hanyoyin da gwamnati za ta iya bincika ayyukan miyagun samari a maimakon hana motoci, abin da ke haifar mana da wahala kenan sosai,” in ji shi.

Haka zalika, David Abase, wani manomi da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijirar tare da danginsa tun a shekarar 2018 sakamakon harin da aka kai musu a gidansu na Abagena, ya ce, matsalar abinci za ta kusantowa sai dai idan an yi wani abu a kan lokaci don kauce wa halin da ake ciki yanzu.

Haka kuma, Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN) na jihar, Aondongu Saaku, ya ce, rashin tsaro ya shafi noma, ya kara da cewa, mummunan halin da ake ciki zai kara tsananta matsalar abinci a kasar nan saboda manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda tsoron ana kashe su.

Ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai ban tsor, sannan ya ce, yunwa za ta addabi kasar sai dai in an dakile halin da ake ciki a yanzu, yana mai cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni daban-daban na nuni da matsalar abinci.

Haka zalika, manoma a Jihar Nasarawa, wadanda al’ummominsu suka fuskanci hare-hare kwanan nan, an tilasta musu yin watsi da gonakinsu.

Da dama daga cikin irin wadannan manoma sun ce ba za su koma ba har sai gwamnatin jihar ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa.

daya daga cikin irin wadannan al’ummomin sune Ajimaka, mazaunin Tib a cikin karamar hukumar Doma. Al’umma sun afka cikin hari a ranar 24 ga Afrilu, 2021.

A yayin harin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai, an kashe akalla mazauna kauyuka 18, akasarinsu manoma yayin da aka lalata dukiyoyi da dama.

Wasu daga cikin manoman a Lafia sun bayyana hare-haren da cewa ba su dace ba.

Sauran kauyukan da ‘yan bindigar suka kai wa hari sun hada da Dooshima, Antsa, Dooka, Angwan Yara, Ikyayior, Targema, Tse Tor da Chia, Umurayi, Dooga, Gindan Rail, Ajikamaka da Ankoma, duk a yankin Ekye Debelopment, Doma ta Kudu a aaramar hukumar Doma.

Da yake bayar da labarin yadda lamarin ya faru, daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, wanda ya kware a harkar noman rani a garin Dooka, Cif Augustine Kuza, ya ce, wasu da ake zargin makiyaya ne sun kwace gonar tasa ta shinkafa.

Kuza ya ce, ya kashe sama da Naira Miliyan 1 don noma gonar, wanda a cewarsa, ya zama wurin kiwo ga makiyaya.

“Ina kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su kawo min dauki,” in ji shi.

Shima da yake zantawa da manema labarai, wani manomi mai mata biyu da ’ya’ya bakwai, Timothy Atta ya ce, “Ina cikin gidana lokacin da na fara jin karar harbe-harbe. Kamar yadda nake tunanin daga ina ne harbin bindigogin yake fitowa, wadancan Fulani makiyaya da muke zaune tare da su a yankin Ajimaka na aaramar hukumar Doma sun zo sun gaya mana cewa hare-haren da suke ta faruwa a Jihar Benuwai ba za su wuce zuwa Nasarawa ba.”

Ya nuna mamakinsa na cewa, an kai hari a wurin duk da tabbacin da makiyaya ke bayarwa a yankinsu.

Da yake maida martani game da ci lamarin, shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar, Mista Samuel Michi, ya yi Allah wadai da yawaitar hare-hare da kisan manoma a jihar.

Michi, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Akwanga na jihar, duk da haka, ya jaddada bukatar tattaunawa tsakanin manoman Tib da ke fada da Fulani makiyaya domin inganta bangaren noma a jihar.

“Muna kira ga gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki da su yi kokarin kawo bangarorin biyu a kan teburi ta yadda za a cimma tattaunawa kuma a kare maslaha ta kowa don ci gaban jihar da ma kasa baki daya,” in ji shi.

 

Exit mobile version